< Mattheum 21 >
1 et cum adpropinquassent Hierosolymis et venissent Bethfage ad montem Oliveti tunc Iesus misit duos discipulos
Yayinda Yesu da almajiransa suka kusato Urushalima sai suka zo Betafaji wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa guda biyu,
2 dicens eis ite in castellum quod contra vos est et statim invenietis asinam alligatam et pullum cum ea solvite et adducite mihi
yace masu, “Ku shiga kauyen da yake gaban ku zaku iske wata jaka da aholaki tara da ita. Ku kwance su ku kawo mani su.
3 et si quis vobis aliquid dixerit dicite quia Dominus his opus habet et confestim dimittet eos
Idan wani ya gaya maku wani abu game da haka, sai ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsu,' mutumin kuwa zai aiko ku da su nan da nan.”
4 hoc autem factum est ut impleretur quod dictum est per prophetam dicentem
Anyi wannan kuwa domin a cika annabcin anabin. Yace,
5 dicite filiae Sion ecce rex tuus venit tibi mansuetus et sedens super asinam et pullum filium subiugalis
“Ku cewa diyar Sihiyona, duba, ga sarkinki na zuwa wurin ki, mai tawali'u ne, kuma akan jaki wanda aholaki ne.”
6 euntes autem discipuli fecerunt sicut praecepit illis Iesus
Sai almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su.
7 et adduxerunt asinam et pullum et inposuerunt super eis vestimenta sua et eum desuper sedere fecerunt
Suka kawo jakar da dan aholakin, suka sa tufafinsu akai, Yesu kuwa ya zauna akan tufafin.
8 plurima autem turba straverunt vestimenta sua in via alii autem caedebant ramos de arboribus et sternebant in via
Yawancin jama'a kuwa suka baza tufafinsu akan hanya, wasu kuma suka yanko ganye daga bishiyoyi suka shimfida su a hanya.
9 turbae autem quae praecedebant et quae sequebantur clamabant dicentes osanna Filio David benedictus qui venturus est in nomine Domini osanna in altissimis
Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, “Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!”
10 et cum intrasset Hierosolymam commota est universa civitas dicens quis est hic
Sa'adda Yesu ya shiga Urushalima sai doki ya cika birnin ana cewa, “Wanene wannan?”
11 populi autem dicebant hic est Iesus propheta a Nazareth Galilaeae
Sai jama'a suka amsa, “Wannan shine Yesu annabi, daga Nazaret ta Galili.”
12 et intravit Iesus in templum Dei et eiciebat omnes vendentes et ementes in templo et mensas nummulariorum et cathedras vendentium columbas evertit
Sai Yesu ya shiga haikalin. Ya kori duk wadanda ke saye da sayarwa a cikin ikiilisiya. Ya birkice teburan masu canjin kudi da kujerun masu sayar da tantabaru.
13 et dicit eis scriptum est domus mea domus orationis vocabitur vos autem fecistis eam speluncam latronum
Ya ce masu, “A rubuce yake, 'Za a kira gidana gidan addu'a,' amma kun mayar dashi kogon 'yan fashi.”
14 et accesserunt ad eum caeci et claudi in templo et sanavit eos
Sai makafi da guragu suka zo wurin sa a haikalin, ya warkar da su.
15 videntes autem principes sacerdotum et scribae mirabilia quae fecit et pueros clamantes in templo et dicentes osanna Filio David indignati sunt
Amma da manyan firistoci da malaman attaura suka ga abubuwan banmamaki da yayi, kuma sa'adda suka ji yara suna tada murya a cikin haikalin suna cewa, “Hossana ga dan Dauda,” sai suka ji haushi.
16 et dixerunt ei audis quid isti dicant Iesus autem dicit eis utique numquam legistis quia ex ore infantium et lactantium perfecisti laudem
Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?'' Yesu ya ce masu, “I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?”
17 et relictis illis abiit foras extra civitatem in Bethaniam ibique mansit
Sai Yesu ya bar su, ya fice daga birnin zuwa Betaniya ya kwana a wurin.
18 mane autem revertens in civitatem esuriit
Washegari da safe yayin da yake komawa birnin, sai yaji yunwa.
19 et videns fici arborem unam secus viam venit ad eam et nihil invenit in ea nisi folia tantum et ait illi numquam ex te fructus nascatur in sempiternum et arefacta est continuo ficulnea (aiōn )
Da ya ga bishiyar baure a bakin hanya, sai yaje wurin amma bai sami kome ba sai dai ganye. Sai ya ce mata, “Kada ki kara yin 'ya'ya har abada.” Sai nan take bishiyar bauren ta bushe. (aiōn )
20 et videntes discipuli mirati sunt dicentes quomodo continuo aruit
Da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suka ce, “Kaka bishiyar bauren ta bushe nan da nan?”
21 respondens autem Iesus ait eis amen dico vobis si habueritis fidem et non haesitaveritis non solum de ficulnea facietis sed et si monti huic dixeritis tolle et iacta te in mare fiet
Yesu ya amsa yace masu, “Hakika ina ce maku, in dai kuna da bangaskiya ba ku yi shakka ba, ba abinda aka yi wa bauren nan kadai za kuyi ba har ma za ku cewa tsaunin nan, “Ka ciru ka fada teku,' sai kuwa haka ta kasance.
22 et omnia quaecumque petieritis in oratione credentes accipietis
Kome kuka roka cikin addu'a, in dai kun gaskanta, za ku samu.”
23 et cum venisset in templum accesserunt ad eum docentem principes sacerdotum et seniores populi dicentes in qua potestate haec facis et quis tibi dedit hanc potestatem
Sa'adda Yesu ya shiga haikalin, sai manyan fristocin da shugabannin jama'a suka zo suka same shi yayin da yake koyarwa, suka ce, “Da wane iko kake yin wadannan abubuwa?”
24 respondens Iesus dixit illis interrogabo vos et ego unum sermonem quem si dixeritis mihi et ego vobis dicam in qua potestate haec facio
Yesu ya amsa yace masu, “Ni ma zan yi maku tambaya daya. In kun fada mani, ni ma zan fada maku ko da wane iko nake yin wadannan abubuwa.
25 baptismum Iohannis unde erat e caelo an ex hominibus at illi cogitabant inter se dicentes si dixerimus e caelo dicet nobis quare ergo non credidistis illi
Daga ina baftismar Yahaya ta fito, daga sama ko kuma daga mutune?” Sai suka yi shawara a tsakanin su, suka ce, “In munce, 'daga sama,' zai ce mana, 'don me bamu gaskanta dashi ba?'
26 si autem dixerimus ex hominibus timemus turbam omnes enim habent Iohannem sicut prophetam
Amma in munce, ' daga mutune,' muna tsoron jama'a, saboda sun san Yahaya annabi ne.”
27 et respondentes Iesu dixerunt nescimus ait illis et ipse nec ego dico vobis in qua potestate haec facio
Sai suka amsa ma Yesu suka ce, ''Bamu sani ba.” Shi ma yace masu, “Nima bazan gaya maku ko da wane iko nake yin abubuwan nan ba.
28 quid autem vobis videtur homo habebat duos filios et accedens ad primum dixit fili vade hodie operare in vinea mea
Amma me kuke tunani? Wani mutum yana da 'ya'ya biyu. Ya je wurin na farkon yace, 'Da, je ka kayi aiki yau a cikin gona.'
29 ille autem respondens ait nolo postea autem paenitentia motus abiit
Yaron ya amsa yace, 'bazan yi ba,' amma daga baya ya canza tunaninsa ya tafi.
30 accedens autem ad alterum dixit similiter at ille respondens ait eo domine et non ivit
Sai mutumin ya je wurin da na biyun ya fada masa abu guda. Wannan dan ya amsa ya ce, 'zanje, baba,' amma bai je ba.
31 quis ex duobus fecit voluntatem patris dicunt novissimus dicit illis Iesus amen dico vobis quia publicani et meretrices praecedunt vos in regno Dei
Wanene a cikin 'ya'ya biyun nan yayi nufin ubansa?” Suka ce, “na farkon.” Yesu ya ce masu, “Hakika ina gaya maku, masu karbar haraji da karuwai za su shiga mulkin Allah kafin ku.
32 venit enim ad vos Iohannes in via iustitiae et non credidistis ei publicani autem et meretrices crediderunt ei vos autem videntes nec paenitentiam habuistis postea ut crederetis ei
Gama Yahaya ya zo maku a hanyar adalci, amma ba ku gaskata da shi ba, a yayinda masu karbar haraji da karuwai suka gaskata da shi. Ku kuwa, bayan kun ga abin da ya faru, baku ma tuba daga baya ba don ku gaskata da shi.
33 aliam parabolam audite homo erat pater familias qui plantavit vineam et sepem circumdedit ei et fodit in ea torcular et aedificavit turrem et locavit eam agricolis et peregre profectus est
Ku saurari wani misalin. Anyi wani mutum, mai gona. Yayi shuka a gonar, ya shinge ta, ya gina ramin matse inabi a cikin gonar, ya kuma gina wata hasumiyar tsaro, sai ya bada hayar gonar ga wadansu manoma. Sai ya tafi wata kasa.
34 cum autem tempus fructuum adpropinquasset misit servos suos ad agricolas ut acciperent fructus eius
Da kakar inabi ta yi, sai ya aiki wadansu bayi su karbo masa amfanin gonar.
35 et agricolae adprehensis servis eius alium ceciderunt alium occiderunt alium vero lapidaverunt
Amma manoman suka kama bayin, suka doddoki dayan, suka kashe dayan, suka jejjefe dayan da duwatsu.
36 iterum misit alios servos plures prioribus et fecerunt illis similiter
Sai mai gonar ya sake aika wadansu bayinsa da suka fi na farko, amma manoman suka yi masu kamar yadda suka yi wa sauran.
37 novissime autem misit ad eos filium suum dicens verebuntur filium meum
Bayan wannnan, sai mai gonar ya aika da dansa wurin su yana cewa, 'za su yi wa dana biyayya.'
38 agricolae autem videntes filium dixerunt intra se hic est heres venite occidamus eum et habebimus hereditatem eius
Amma da manoman suka ga dan, sai suka ce a tsakanin su, 'wannan shine magajin. Kuzo, mu kashe shi mu gaji gonar.'
39 et adprehensum eum eiecerunt extra vineam et occiderunt
Sai suka dauke shi, suka jefar da shi daga cikin gonar, suka kashe shi.
40 cum ergo venerit dominus vineae quid faciet agricolis illis
To idan me gonar ya zo, me zai yiwa manoman?
41 aiunt illi malos male perdet et vineam locabit aliis agricolis qui reddant ei fructum temporibus suis
Suka ce masa, “Zai hallaka mugayen manoman nan ta hanya mai tsanani, zai kuma bada gonar haya ga wadansu manoman, mutanen da za su biya, lokacin da inabin ya nuna.”
42 dicit illis Iesus numquam legistis in scripturis lapidem quem reprobaverunt aedificantes hic factus est in caput anguli a Domino factum est istud et est mirabile in oculis nostris
Yesu yace masu, “Baku taba karantawa a nassi ba,'' 'Dutsen da magina suka ki ya zama dutse mafi amfani. Wannan daga Ubangijine, kuma abin mamaki ne a idanunmu?'
43 ideo dico vobis quia auferetur a vobis regnum Dei et dabitur genti facienti fructus eius
Saboda haka ina gaya maku, za a karbe mulkin Allah daga wurin ku a ba wata al'umma da zata bada amfaninsa.
44 et qui ceciderit super lapidem istum confringetur super quem vero ceciderit conteret eum
Duk wanda ya fadi akan dutsen nan zai ragargaje. Amma duk wanda dutsen ya fadawa, zai nike.”
45 et cum audissent principes sacerdotum et Pharisaei parabolas eius cognoverunt quod de ipsis diceret
Da manyan firistocin da farisawan suka ji wannan misalin, sai suka gane da su yake.
46 et quaerentes eum tenere timuerunt turbas quoniam sicut prophetam eum habebant
Da suka nemi kama shi, sai suka ji tsoron taron, saboda mutanen sun dauke shi annabi.