< Mattheum 20 >
1 simile est enim regnum caelorum homini patri familias qui exiit primo mane conducere operarios in vineam suam
Gama mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da asuba ya nemi 'yan kwadago da za su yi aiki a gonarsa.
2 conventione autem facta cum operariis ex denario diurno misit eos in vineam suam
Bayan sun shirya kudin da zai biya ma'aikata kimanin dinari daya a kowanne yini, sai ya aike su gonarsa suyi aiki.
3 et egressus circa horam tertiam vidit alios stantes in foro otiosos
Misalin sa'a ta uku sai ya sake fita, sai ya ga wasu ma'aikata suna tsaye a bakin kasuwa, babu aiki.
4 et illis dixit ite et vos in vineam et quod iustum fuerit dabo vobis
Sai ya ce masu, 'Kuzo kuyi aiki a gonar, duk abinda ya wajaba, zan ba ku,' Sai suka tafi su yi aikin.
5 illi autem abierunt iterum autem exiit circa sextam et nonam horam et fecit similiter
Sai ya sake fita a sa'a ta shida ya kuma sake fita a sa'a ta tara, ya sake yin hakan din.
6 circa undecimam vero exiit et invenit alios stantes et dicit illis quid hic statis tota die otiosi
Ya kuma sake yin haka a sa'a ta sha daya, da ya fita sai ya ga wasu a tsaye da ba sa yin kome. Sai ya ce masu, 'Me yasa kuke tsaye ba ku yin kome dukan yini?'
7 dicunt ei quia nemo nos conduxit dicit illis ite et vos in vineam
Sai suka ce masa, 'Ai babu wanda ya dauke mu aiki, shi yasa.' Sai ya ce masu, 'ku ma, kuje cikin gonar.
8 cum sero autem factum esset dicit dominus vineae procuratori suo voca operarios et redde illis mercedem incipiens a novissimis usque ad primos
Da yamma ta yi, sai mai gonar ya ce wa manajansa, 'Ka kira ma'aikatan nan ka biya su hakkin su, amma ka fara da wadanda suka zo a karshe, zuwa na farkon.'
9 cum venissent ergo qui circa undecimam horam venerant acceperunt singulos denarios
Sa'adda wadanda suka fara aiki da yamma suka zo, an biya su daidai yadda ake biya a yini.
10 venientes autem et primi arbitrati sunt quod plus essent accepturi acceperunt autem et ipsi singulos denarios
Da wadanda suka fara aiki tun safe suka zo, suna tsammani za a ba su fiye da wadanda sun zo daga baya, amma aka ba kowannensu dinari daya.
11 et accipientes murmurabant adversus patrem familias
Da suka karbi hakkinsu, suka yi gunaguni game da mai gonar.
12 dicentes hii novissimi una hora fecerunt et pares illos nobis fecisti qui portavimus pondus diei et aestus
Suka ce, 'Wadannan da suka zo a karshe, sa'a guda ce kadai suka yi aiki, amma ka ba su daidai da mu, mu da muka yi fama da aiki cikin zafin rana.'
13 at ille respondens uni eorum dixit amice non facio tibi iniuriam nonne ex denario convenisti mecum
Amma mai gonar ya amsa wa daya daga cikin su, ya ce, 'Aboki na, ban yi maku laifi ba. Ai mun shirya zan biya ku yadda ake biya a yini, ko ba haka ba?
14 tolle quod tuum est et vade volo autem et huic novissimo dare sicut et tibi
Ku karbi abin da ke na ku, ku tafi. Ganin dama ta ne, in ba wadannan da suka zo a karshe daidai da ku.
15 aut non licet mihi quod volo facere an oculus tuus nequam est quia ego bonus sum
Ashe, ba daidai bane a gare ni, in yi abin da na ga dama da mallaka ta? Ko kishi ne kuke yi saboda kirki na?'
16 sic erunt novissimi primi et primi novissimi multi sunt enim vocati pauci autem electi
Haka yake, na karshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na karshe.'' [An kira dayawa, amma kadan ne zababbu].
17 et ascendens Iesus Hierosolymam adsumpsit duodecim discipulos secreto et ait illis
Da Yesu zai tafi Urushalima, ya dauki sha-biyun nan a gefe, yayin da suke tafiya, sai ya ce masu,
18 ecce ascendimus Hierosolymam et Filius hominis tradetur principibus sacerdotum et scribis et condemnabunt eum morte
“Ku duba fa, zamu tafi Urushalima, kuma za a bada Dan Mutum ga manyan firistoci da marubuta. Za su kuma yanke masa hukuncin kisa,
19 et tradent eum gentibus ad deludendum et flagellandum et crucifigendum et tertia die resurget
za su kuma bada shi ga al'ummai don suyi masa ba'a, su bulale shi, su kuma gicciye shi. Amma a rana ta uku, za a tada shi.''
20 tunc accessit ad eum mater filiorum Zebedaei cum filiis suis adorans et petens aliquid ab eo
Sai uwar 'ya'yan Zabadi ta zo wurin Yesu tare da 'ya'yanta. Ta rusuna a gabansa tana neman alfarma a wurinsa.
21 qui dixit ei quid vis ait illi dic ut sedeant hii duo filii mei unus ad dexteram tuam et unus ad sinistram in regno tuo
Yesu ya ce mata, Me kike so in yi maki?'' Sai ta ce masa, ''Ina so ka ba 'ya'yana izinin zama a mulkinka, daya a hannun damanka, daya kuma a hannun hagunka.
22 respondens autem Iesus dixit nescitis quid petatis potestis bibere calicem quem ego bibiturus sum dicunt ei possumus
Amma Yesu ya amsa, ya ce, ''Baku san abin da kuke roko ba. Ko zaku iya sha daga cikin kokon da zan sha bada dadewa ba?'' Sai suka ce masa, ''Zamu iya.''
23 ait illis calicem quidem meum bibetis sedere autem ad dexteram meam et sinistram non est meum dare vobis sed quibus paratum est a Patre meo
Sai ya ce masu, ''In dai kokon nan da zan sha ne, lallai zaku sha. Amma, zama a hannun dama na da kuma hannun hagu na, ba ni ne mai bayarwa ba, amma na wadanda Uba na ya shirya domin su ne.''
24 et audientes decem indignati sunt de duobus fratribus
Sa'anda sauran almajirai goma suka ji haka, sun yi bacin rai da 'yan'uwan nan biyu.
25 Iesus autem vocavit eos ad se et ait scitis quia principes gentium dominantur eorum et qui maiores sunt potestatem exercent in eos
Amma Yesu ya kira su wurin sa, ya ce, ''Kuna sane da cewa, sarakunan al'ummai suna gwada masu mulki, manyan-gari kuma na nuna masu iko.
26 non ita erit inter vos sed quicumque voluerit inter vos maior fieri sit vester minister
Ba zai kasance haka a tsakanin ku ba. A maimakon haka, duk wanda ke da marmari ya zama da girma a tsakanin ku, ya zama baran ku.
27 et qui voluerit inter vos primus esse erit vester servus
Wanda kuma ke da marmari ya zama na farko a cikin ku, ya zama baran ku.
28 sicut Filius hominis non venit ministrari sed ministrare et dare animam suam redemptionem pro multis
Kamar dai yadda Dan mutum bai zo don a bauta masa ba, amma yayi bauta, ya kuma bada ransa fansa domin mutane dayawa.''
29 et egredientibus eis ab Hiericho secuta est eum turba multa
Da suka fita daga Yariko, babban taro suka bi shi.
30 et ecce duo caeci sedentes secus viam audierunt quia Iesus transiret et clamaverunt dicentes Domine miserere nostri Fili David
Suka kuma ga makafi biyu zaune a bakin hanya. Da makafin suka ji cewa Yesu ne ke wucewa, sai suka tada murya suna cewa, ''Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai.''
31 turba autem increpabat eos ut tacerent at illi magis clamabant dicentes Domine miserere nostri Fili David
Amma jama'ar suka tsauta masu, suka ce suyi shiru. Duk da haka, makafin suka kara tada murya fiye da na da, suka ce, ''Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai.''
32 et stetit Iesus et vocavit eos et ait quid vultis ut faciam vobis
Sai Yesu ya tsaya cik, ya sa aka kira su, sai ya ce masu, ''Me kuke so in yi maku?''
33 dicunt illi Domine ut aperiantur oculi nostri
Sai suka ce masa, Ya Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.''
34 misertus autem eorum Iesus tetigit oculos eorum et confestim viderunt et secuti sunt eum
Sai Yesu yayi juyayi a cikin sa, ya taba idanunsu. Nan da nan, suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.