< Titus 1 >
1 Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, ta wurin bangaskiyar zababbun mutanen Allah da sanin gaskiya da ta yadda da allahntaka.
这封信来自上帝的仆人、耶稣基督的使徒保罗。我发送这封信,是为了建立上帝所选子民的信心,并分享可以让我们为上帝而活的真理知识。
2 Wadannan na cikin begen rai marar matuka wanda Allah, wanda babu karya a cikinsa, ya alkawarta kafin dukkan lokatan zamanai. (aiōnios )
这给了他们永生的希望,这永生是从不说谎的上帝很久以前承诺的。 (aiōnios )
3 A daidai lokaci, ya bayyana maganarsa ta wurin sakonsa da ya damka mani in shelar. Zan yi wannan ta wurin umarnin Allah mai ceton mu.
在适当的时候,上帝就按照福音的宣讲,显化他的道。这宣讲也是我遵循主上帝的命令,在他的委托下讲述给你们。
4 Zuwa ga Titus, da' na gaske a cikin bangaskiyarmu. Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah Uba da Almasihu Yesu mai ceton mu.
这封信是寄给提多的,他是我真正的儿子,通过我们共同对上帝的信任。愿你们拥有来自父上帝和救世主基督耶稣的恩惠和平安。
5 Sabili da wannan ne na bar ka a Karita domin ka daidaita abubuwan da basu cika ba, ka kuma nada dattibai a dukan birane kamar yadda na umarceka.
我过去之所以把你留在克里特岛,是要你办好需要完成的事,照我所说的在各城任命长老。
6 Dole ne dattijo ya zama marar abin zargi, mijin mace daya, da amintattun 'ya'ya wadanda babu wani zargi na mugunta ko rashin kamun kai a kansu.
长老的人选必须拥有良好声誉,有一名妻子,儿女都信主,没有人控告其放荡或不服从。
7 Wajibi ne shugaban Ikklisiya, a matsayin sa na mai kulla da haikalin Allah, ya zama marar aibi. Kada ya zama mai surutu ko rashin hakuri. Kada ya zama mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai hayaniya, ko mai handama.
作为上帝的领导者,大长老必须拥有良好的声誉,不能傲慢自大、不能随便动怒、不好酒、不打人、不贪不义之财。
8 Maimakon haka, ya zama mai karbar baki, abokin abinda ke mai kyau. Dole ne ya zama mai hankali, adali, cike da allahntaka, da kuma kamun kai.
他要热情好客, 喜爱好的事情,做良善正直的事情。他应为上帝而活,应该自我控制,
9 Ya zama mai rike amintaccen sakon da aka koyar da karfi, yadda zai iya karfafa wasu da koyarwa mai kyau ya kuma yi wa wadanda suke hamayya da shi gyara.
必须将自己奉献给那所传授的、值得信赖的道。这样他能以正确的教导鼓励他人,说服那些不同意的人。
10 Domin akwai kangararrun mutane dayawa, musamman masu kaciya. Maganganunsu na banza ne. Suna yaudara kuma suna badda mutane.
因为周围有很多背叛者,他们说了很多没有意义的欺骗之语,尤其是来自奉行割礼的那群人。
11 Wajibi ne mu hana su. Suna koyar da abinda bai kamata su koyar ba saboda makunyaciyar riba suna kuma rusar da iyalai dungum.
他们的言论必须停止。这些人让整个家庭陷入混乱,为了赚钱而进行错误的传授。
12 Daya daga cikinsu, kuma mai hikima ne daga cikinsu, yace, “Kirawa manyan makaryata ne, lalatattu kuma miyagun dabbobi, masu kyiuya da zarin cin abinci.”
他们自己人中就有一个先知说过:“克里特人总爱说谎,他们就是懒惰而贪婪的恶兽。”
13 Wannan magana gaskiya ne, ka yi masu gyara da tsanani yadda zasu kafu a cikin bangaskiya.
这说的是真的。因此,你要严厉地责备他们,让他们用健全的方式相信上帝,
14 Kada ka mai da hankalin ka ga tatsunniyoyi na Yahudawa ko dokokin mutane wadanda sun sauya gaskiya.
不再理会犹太人的无稽之谈和偏离正道之人的说法。
15 Ga wadanda suke da tsarki, komai mai tsarki ne. Amma wadanda suke marasa tsarki da rashin bangaskiya, komai marar tsarki ne. Domin zuciyarsu da lamirinsu sun gurbata.
对于心灵洁净之人,一切都是洁净;但对于污秽和不信上帝的人,一切都不洁净,连他们的思想和良心都是污秽的。
16 Suna cewa sun san Allah, amma sun musanta shi ta wurin ayyukansu. Sun zama abin kyama da marasa biyayya. Ba za a iya tabbaatar dasu ba akan wani aiki maikyau.
他们声称知道上帝,行为却显示并非如此。他们是可憎的、悖逆的,做任何善事都毫无用处。