< Yohanna 1 >
1 A cikin farko akwai Kalma, Kalmar kuma tana tare da Allah, wannan Kalma kuwa Allah ne.
2 Shi kuwa tare da Allah yake tun farko.
3 Dukan abu ta wurinsa aka yi su, babu abin da aka halitta sai ta wurin sa.
4 A cikinsa rai ya ke, kuma wannan rai ya zama haske ga dukan mutane.
5 Hasken ya haskaka a cikin duhu, kuma duhun bai rinjaye shi ba.
6 Akwai wani mutum wanda Allah ya aiko, mai suna Yahaya.
7 Ya zo a matsayin mai ba da shaida game da hasken, domin kowa ya ba da gaskiya ta wurinsa.
8 Ba Yahaya ne hasken ba, amma ya zo ne domin ya shaida hasken.
9 Wannan shine haske na gaskiya mai ba da haske ga dukan mutane, da ke zuwa cikin duniya.
10 Yana cikin duniya, kuma an halicci duniya ta wurinsa, amma duniya bata san shi ba.
11 Ya zo wurin nasa, amma nasa basu karbe shi ba.
12 Amma duk iyakar wadanda suka karbe shi, suka kuma ba da gaskiya ga sunansa, ya ba su 'yanci su zama 'ya'yan Allah.
13 Wadanda aka haife su ba ta wurin jini ba, ko ta wurin nufin jiki, ko nufin mutum, amma ta wurin Allah.
14 Kalmar kuma ya zama jiki ya zauna cikin mu. Mun ga daukakarsa, daukaka irin ta makadaici shi kadai wanda ya zo daga Uban, cike da alheri da gaskiya.
15 Yahaya ya yi shaida akansa yana kira da karfi, cewa, “Wannan shine wanda na yi magana a kansa cewa, 'Shi wanda ke zuwa bayana, ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.'”
16 Domin daga cikarsa ne muka karbi alheri akan alheri.
17 Gama shari'a ta zo daga wurin Musa. Alheri da gaskiya sun zo ta wurin Yesu Almasihu.
18 Babu lokacin da wani ya taba ganin Allah, shi wanda shi kadai ne Allah, wanda ke jingine da kirjin Uba, shi ya bayyana shi.
19 Wannan ita ce shaidar Yahaya sa'adda Yahudawa suka aika da Firistoci da Lawiyawa zuwa gareshi don su tambaye shi, “Wanene kai?”
20 Ya fada dalla dalla, kuma bai musunta ba, yana amsa masu cewa, “ba nine Almasihu ba.”
21 Sai suka tambaye shi, “To kai wanene? Kai Iliya ne?” Yace, “Ba ni ba ne.” Suka ce, “Kai ne anabin?” Ya amsa, “A'a”.
22 Sai suka ce masa, “Kai wanene, domin mu bada amsa ga wadanda suka aiko mu? Me kake fadi game da kanka?”
23 Yace, “Ni murya ne, da ke kira cikin jeji, 'Ku daidaita hanyar Ubangiji,' kamar yadda annabi Ishaya ya fada.”
24 Su wadanda aka aika daga wurin Farisawa suke. Sai suka tambaye shi cewa,
25 “To don me kake baftisma idan kai ba Almasihu bane, ko Iliya, ko annabin?”.
26 Yahaya ya amsa masu, cewa, “Ina baftisma ne da ruwa. Amma a cikinku akwai wani tsaye wanda ba ku sani ba,
27 shi wanda ke zuwa bayana, wanda ko igiyar takalminsa ban isa in kwance ba.”
28 Wadannan abubuwa sun faru ne a Baitanya, a dayan ketaren Urdun, a wurin da Yahaya ke Baftisma.
29 Washegari, Yahaya ya ga Yesu yana zuwa wurinsa ya ce, “Duba, ga Dan Ragon Allah wanda ke dauke zunubin duniya!
30 Wannan shine wanda na fada maku cewa, “Shi wanda ke zuwa bayana ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.'
31 Ban san shi ba, amma saboda a bayyana shi ga Isra'ila ne nazo ina baftisma da ruwa. “
32 Yahaya ya shaida, cewa, “Na ga Ruhu yana saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa.
33 Ban gane shi ba, amma shi wanda ya aiko ni in yi baftisma cikin ruwa ya fada mani cewa, 'duk wanda ka ga Ruhun ya sauka kuma ya zauna a kansa, shine wanda ke yin baftisma cikin Ruhu mai tsarki.'
34 Na gani, na kuma shaida cewa wannan shine Dan Allah.”
35 Kuma, washegari, da Yahaya na tsaye da biyu daga cikin almajiransa,
36 suka ga Yesu na wucewa, sai Yahaya ya ce, “Duba, ga Dan rago na Allah!”
37 Sai almajiransa biyu suka ji ya fadi haka, suka kuwa bi Yesu.
38 Da Yesu ya waiwaya ya gan su suna bin sa, sai ya ce masu, “Me kuke so?” Suka amsa, “Rabbi (wato 'Mallam'), ina kake da zama?”
39 Yace masu, “Zo ku gani.” Sai suka zo suka ga inda yake zama; suka zauna da shi ranan nan, gama wajen sa'a ta goma ne.
40 Daya daga cikin wadanda suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu shine Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus.
41 Ya fara neman dan'uwansa Siman yace masa, “Mun sami Almasihu” (wanda ake kira 'Kristi').
42 Ya kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi yace, “Kai ne Siman dan Yahaya. Za a kira ka Kefas,” (ma'ana, 'Bitrus').
43 Washegari, da Yesu yana shirin tafiya zuwa Galili, sai ya sami Filibus, ya ce masa, “ka biyo ni.”
44 Filibus dan asalin Baitsaida ne, garin Andarawus da Bitrus.
45 Filibus ya sami Natana'ilu yace masa, “Mun same shi, shi wanda Musa ya rubuta shi a cikin attaura, da annabawa: Yesu Dan Yusufu, Ba-Nazarat.”
46 Natana'ilu ya ce masa, “za a iya samun wani abu nagari a Nazarat?” Filibus yace masa, “Zo ka gani.”
47 Yesu ya ga Natana'ilu yana zuwa wurinsa sai yayi magana game da shi, “Duba, Ba-Isra'ile na hakika wanda babu yaudara a cikinsa.”
48 Natana'ilu yace masa, “Ta yaya ka san ni?” Sai Yesu ya amsa masa yace, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'adda kake a gindin baure, na gan ka.”
49 Natana'ilu ya amsa, “Rabbi, Kai Dan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!”
50 Yesu ya amsa masa yace, “Don na ce maka, 'Na gan ka a gindin Baure', ka gaskanta? Za ka ga abubuwa da suka fi wannan girma.”
51 Sai yace, 'Hakika, hakika ina gaya maka, zaka ga sammai a bude, mala'ikun Allah kuma suna hawa suna sauka akan Dan Mutum.”