< Yohanna 3 >
1 akwai wani Bafarise da ake kira Nikodimu, shugaba a cikin Yahudawa.
2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dare ya ce masa, “Rabbi, mun sani cewa kai malami ne da kazo daga wurin Allah, gama ba wanda zai iya yin wadannan alamu da kake yi sai idan Allah na tare da shi.”
3 Yesu ya amsa masa, “Hakika, hakika, idan ba a sake haifuwar mutum ba, ba zai iya ganin mulkin Allah ba.”
4 Nikodimu ya ce masa, “Yaya za a sake haifuwar mutum bayan ya tsufa? Ba zai iya sake shiga cikin cikin uwarsa kuma a haife shi ba, zai iya?”
5 Yesu ya amsa, “Hakika, hakika, idan ba a haifi mutum da ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga cikin mulkin Allah ba.
6 Abin da aka haifa ta wurin jiki, jiki ne, kuma abin da aka haifa ta wurin Ruhu, Ruhu ne.
7 Kada ka yi mamaki don na ce maka, 'dole a maya haifuwar ka.'
8 Iska takan hura duk inda ta ga dama. Ka kan ji motsin ta, amma ba ka san inda ta fito ko inda za ta tafi ba. Haka duk wanda aka haifa daga Ruhu.”
9 Nikodimu ya amsa yace masa, “Yaya wannan zai yiwu?”
10 Yesu ya amsa yace masa, “Kai malami ne a Israila amma ba ka san wadannan al'amura ba?
11 Hakika, hakika, ina gaya maka, muna fadin abubuwan da muka sani, kuma muna shaida abubuwan da muka gani. Duk da haka ba ku karbi shaidar mu ba.
12 Idan na gaya maka abubuwan da ke na duniya amma baka gaskata ba, to yaya zaka gaskata idan na gaya maka abubuwa na sama?
13 Babu wanda ya taba hawa zuwa sama sai dai shi wanda ya sauko daga sama: wato Dan Mutum.
14 Kamar yadda Musa ya ta da maciji a jeji, haka ma dole a ta da Dan Mutum
15 domin dukan wadanda suka bada gaskiya gareshi su sami rai na har abada. (aiōnios )
16 Gama Allah ya kaunaci duniya sosai, har ya ba da makadaicin Dansa, domin duk wanda ya bada gaskiya gareshi, kada ya mutu, amma ya samu rai madawwami. (aiōnios )
17 Gama Allah bai aiko da Dansa cikin duniya domin ya kayar da duniya ba, amma domin a ceci duniya ta wurin sa.
18 Duk wanda ya bada gaskiya gare shi ba a kayar da shi ba, amma duk wanda bai bada gaskiya gare shi ba an riga an kayar da shi, domin bai bada gaskiya ga sunan wannan da shi kadai ne Dan Allah ba.
19 Wannan shi ne dalilin shari'ar, domin haske ya zo duniya, amma mutane suka kaunaci duhu fiye da hasken, sabili da ayyukan su na mugunta ne.
20 Domin duk wanda ke mugayen ayyuka ya ki haske, kuma baya zuwa wurin hasken domin kada ayyukansa su bayyanu.
21 Sai dai duk wanda yake aikata gaskiya kan zo wurin hasken domin ayyukansa, da ake aiwatarwa ga Allah, su bayyanu.
22 Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi kasar Yahudiya. A can ya dan zauna tare da su ya kuma yi Baftisma.
23 Yahaya ma yana Baftisma a Ainon kusa da Salim domin akwai ruwa da yawa a can. Mutane na zuwa wurin sa yana masu Baftisma,
24 domin a lokacin ba a jefa Yahaya a kurkuku ba tukuna.
25 Sai gardama ta taso tsakanin almajiran Yahaya da wani Bayahude akan al'adun tsarkakewa.
26 Suka je wurin Yahaya suka ce, “Rabbi, wanda yake tare da kai a dayan ketaren kogin Urdun, kuma ka shaida shi, duba, yana baftisma, kuma mutane duka suna zuwa wurin sa.”
27 Yahaya ya amsa, “Mutum ba zai iya samun wani abu ba sai an ba shi daga sama.
28 Ku da kanku zaku shaida na ce, 'Ba ni ne Almasihu ba' amma amaimakon haka, 'an aiko ni kafin shi.'
29 Amaryar ta angon ce. Yanzu abokin angon, wanda ke tsaye yana saurarensa, yana murna sosai saboda muryan angon. Murnata ta cika domin wannan.
30 Dole shi ya karu, ni kuma in ragu.
31 Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa. Shi Wanda ya zo daga duniya, na duniya ne, kuma game da duniya yake magana. Shi wanda ya fito daga sama yana saman kowa.
32 Ya shaida abubuwan da ya ji ya kuma gani, amma babu wanda ya karbi shaidarsa.
33 Duk wanda ya karbi shaidarsa ya tabbatar Allah gaskiya ne.
34 Domin duk wanda Allah ya aika kan yi magana da kalmomin Allah. Domin bai bada Ruhun da ma'auni ba.
35 Uban ya kaunaci Dan, ya kuma ba da dukan komai a hanunsa.
36 Shi wanda ya bada gaskiya ga Dan ya na da rai madawwami, amma wanda ya ki yiwa Dan biyayya ba zai ga rai ba, amma fushin Allah na kansa. (aiōnios )