< Ibraniyawa 13 >

1 Bari kaunar 'yan'uwa ta cigaba.
Broderkærligheden blive ved!
2 Kada ku manta da karrama baki, domin ta wurin yin haka, wasu suka marabci mala'iku ba tare da saninsu ba.
Glemmer ikke Gæstfriheden; thi ved den have nogle, uden at vide det, haft Engle til Gæster.
3 Ku tuna da wadanda ke cikin kurkuku, kamar dai kuna tare da su cikin wannan hali. Kuma ku tuna da masu shan azaba kamar tare kuke cikin wannan hali
Kommer de fangne i Hu, som vare I selv medfangne; dem, der lide ilde, som de, der også selv ere i et Legeme.
4 Bari kowa ya girmama aure, bari kuma a tsarkake gadon aure, gama Allah zai shar'anta fasikai da mazinata.
Ægteskabet være æret hos alle, og Ægtesengen ubesmittet; thi utugtige og Horkarle skal Gud dømme.
5 Bari halinku ya kubuta daga kaunar kudi. Ku dangana da abubuwan da kuke dasu, domin Allah da kansa yace, “Bazan barku ba, ba kuma zan yashe ku ba.”
Eders Vandel være uden Pengegridskhed, nøjes med det, I have; thi han har selv sagt: "Jeg vil ingenlunde slippe dig og ingenlunde forlade dig,"
6 Bari mu zama da dangana domin mu sami gabagadin cewa, “Ubangiji ne mai taimakona, ba zan ji tsoro ba. To me mutum zai iya yi mani?”
så at vi kunne sige med frit Mod: "Herren er min Hjælper, jeg vil ikke frygte; hvad kan et Menneske gøre mig?"
7 Ku fa lura da wadanda ke shugabanninku, wadanda suka horar da ku cikin maganar Allah, kuma ku lura da sakamakon rayuwarsu, ku yi koyi da bangaskiyarsu.
Kommer eders Vejledere i Hu, som have forkyndt eder Guds Ord, og idet I betragte deres Vandrings Udgang, så efterligner deres Tro!
8 Yesu Almasihu daya ne a jiya, da yau, da har abada. (aiōn g165)
Jesus Kristus er i Går og i Dag den samme, ja, til evig Tid. (aiōn g165)
9 Kada ku kauce zuwa ga bakin koyarwa daban daban, domin yana da kyau zuciya ta ginu ta wurin alheri, amma ba da dokoki game da abinci ba, wadanda basu taimaki wadanda suka kiyayesu ba.
Lader eder ikke lede vild af mange Hånde og fremmede Lærdomme; thi det er godt, at Hjertet styrkes ved Nåden, ikke ved Spiser; thi deraf have de, som holdt sig dertil, ingen Nytte haft.
10 Muna da bagadin da wadanda ke hidima a cikin alfarwa basu da ikon su ci daga bisansa.
Vi have et Alter, hvorfra de, som tjene ved Tabernaklet, ikke have Ret til at spise.
11 Babban firist na shiga wuri mai tsarki da jinin dabbobin da aka yanka, hadayar zunubai, amma namansu a kan kai bayan sansani a kone shi.
Thi de Dyr, hvis Blod for Syndens Skyld bæres ind i Helligdommen af Ypperstepræsten, deres Kroppe opbrændes uden for Lejren.
12 Domin haka Yesu shima ya sha wahala a bayan kofar birnin, domin ya tsarkake mutane ta wurin jininsa.
Derfor led også Jesus uden for Porten, for at han kunde hellige Folket ved sit eget Blod.
13 Domin haka bari mu tafi gare shi a bayan sansani dauke da kunyarsa.
Så lader os da gå ud til ham uden for Lejren, idet vi bære hans Forsmædelse;
14 Domin bamu da wani birni dawwamamme a nan. Maimako haka muna bidar birni dake zuwa.
thi her have vi ikke en blivende Stad, men vi søge den kommende.
15 Ta wurin sa kuma, bari kullum mu mika hadayu na yabo ga Allah, yabon kuwa shine kalmomin bakinmu da ke daukaka sunansa.
Lader os da ved ham altid frembære Gud Lovprisnings Offer, det er: en Frugt af Læber, som bekende hans Navn.
16 Kada kuma mu manta da yin nagarta da kuma taimakon juna, domin Allah na farin ciki sosai da irin wadannan hadayun.
Men glemmer ikke at gøre vel og at meddele; thi i sådanne Ofre har Gud Velbehag.
17 Ku yi biyayya da sadaukarwa ga shugabanninku, domin suna aikin tsaro a kanku saboda rayukanku, kamar wadanda zasu bada lissafi. Kuyi biyayya gare su saboda su yi aikin lura daku cikin farin ciki, ba da bakin ciki ba, don in su yi da bakin ciki ba zai amfane ku ba.
Lyder eders Vejledere og retter eder efter dem; thi de våge over, eders Sjæle som de, der skulle gøre Regnskab - for at de må gøre dette med Glæde og ikke sukkende: thi dette er eder ikke gavnligt.
18 Kuyi mana addu'a, domin mun tabbata muna da lamiri mai tsabta, kuma muna burin muyi rayuwar dake daidai cikin dukkan al'amura.
Beder for os; thi vi ere forvissede om, at vi have en god Samvittighed, idet vi ønske at vandre rettelig i alle Ting.
19 Kuma ina karfafa ku dukka kuyi haka, domin in sami dawowa gareku da sauri.
Og jeg formaner eder des mere til at gøre dette, for at jeg desto snarere kan gives eder igen.
20 To bari Allahn salama, wanda ya tada babban makiyayin tumakin nan daga matattu, Ubangijinmu Yesu, ta wurin jinin madawwamin alkawari, (aiōnios g166)
Men Fredens Gud, som førte den store Fårenes Hyrde, vor Herre Jesus, op fra de døde med en evig Pagts Blod, (aiōnios g166)
21 ya kammala ku da dukan abu mai kyau domin ku aikata nufinsa. Bari yayi aiki a cikinmu wanda zai gamshe shi sosai. Ta wurin Yesu Almasihu, bari daukaka ta tabbata gare shi har abada. Amin. (aiōn g165)
han bringe eder til Fuldkommenhed i alt godt, til at gøre hans Villie, og han virke i eder det, som er velbehageligt for hans Åsyn, ved Jesus Kristus: ham være Æren i Evighedernes Evigheder: Amen. (aiōn g165)
22 'Yan'uwa, yanzu dai ina karfafa ku, da ku jurewa takaitacciyar maganar karfafawar da na rubuto maku.
Jeg beder eder, Brødre! at I finde eder i dette Formaningsord; thi jeg har jo skrevet til eder i Korthed.
23 Ina so ku sani an saki dan'uwan mu Timoti, tare da shi zan zo in gan ku idan ya iso da sauri.
Vid, at vor Broder Timotheus er løsladt; sammen med ham vil jeg se eder, dersom han snart kommer.
24 Ku gaida shugabanninku dukka da kuma dukkan masu bada gaskiya. 'Yan'uwa daga can Italiya suna gaishe ku.
Hilser alle eders Vejledere og alle de hellige! De fra Italien hilse eder.
25 Bari alheri ya kasance tare daku dukka.
Nåden være med eder alle!

< Ibraniyawa 13 >