< Ayyukan Manzanni 17 >

1 Bayan sun wuce biranen Amfibolis da Aboloniya, sun iso birnin Tasalunika, in da akwai wata majami'ar Yahudawa a wurin.
And when they had passed through Amphipolis and Apollonia, they came to Thessalonica, where there was a synagogue of the Jews.
2 Bulus, kamar yadda ya saba, ya nufi wurinsu, yana tattaunawa da su har Asabaci uku, daga cikin littattafai.
And Paul, according to his custom, went in to them, and, for three sabbath-days, he reasoned with them from the Scriptures,
3 Bulus ya bude littattafai yana bayyana masu cewa, dole ne Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu. Ya ce, ''Wannan Yesu kuwa da nake sanar maku, shine Almasihu''.
explaining and affirming that it was necessary for the Christ to suffer and to rise from the dead; and that this Jesus whom I preach to you is the Christ.
4 Wasu Yahudawa sun yarda, sun bi Bulus da Sila, da wadansu Helenawa, da Shugabannin Mata da jama'a da yawa.
And some of them believed, and associated themselves with Paul and Silas; of the devout Greeks, a great multitude, and of the chief women, not a few.
5 Yahudawan da basu ba da gaskiya ba suka cika da kishi, suka dauki wadansu 'yan ta'adda daga cikin kasuwa, suka tada tarzoma cikin birnin, mutane da yawa na bin su. Sun kai hari a gidan Yason, da niyyar fitar da Bulus da Sila a gaban jama'a.
But the unbelieving Jews, taking with them some evil men, who were loungers about the markets, and collecting a mob, set the city in an uproar; and having assaulted the house of Jason, they sought to bring them out to the people.
6 Amma da ba su ga Bulus da Sila ba, suka ja Yason da wasu 'yan'uwa masu bi zuwa gaban mahukuntar birnin, suna cewa, ''Wadannan ne fa masu ta da zaune tsaye, gashi sun zo mana.
But not finding them, they dragged Jason and certain brethren before the rulers of the city, crying out: These men, who have thrown the world into confusion, have come hither also;
7 Wadannan mutane da Yason ya marabta, sun saba wa dokokin Kaisar; Suna cewa akwai wani sarki mai suna - Yesu.''
whom Jason has received into his house: and they all act in opposition to the decrees of Cæsar, saying, That there is another king, Jesus.
8 Da taron jama'a, da mahukuntan birnin suka ji haka, sun damu.
And the multitude, and the rulers of the city, were troubled when they heard these things.
9 Bayan da sun amshi kudi daga wurin Yason da sauran 'yan'uwan, sai suka sake su.
And they took security of Jason, and of the others, and let them go.
10 A wannan daren, 'yan'uwa masu bi suka fitar da Bulus da Sila, suka aike su garin Biriya. Da isar su can, su ka nufa majami'ar Yahudawa.
And the brethren immediately sent away Paul and Silas by night to Berea; and when they had come, they went into the synagogue of the Jews.
11 Mutanen Biriya daban suke da na Tasalunika, sun yarda da sakon Bulus da zuciya daya, suna kuma binciken littattafai kowace rana domin su tabbatar da sakon Bulus, ko gaskiya ne.
These were of a better disposition than those in Thessalonica, for they received the word with all readiness of mind, examining the Scriptures daily, whether these things were so.
12 Saboda haka mutane da yawa cikin su sun ba da gaskiya, tare da wadansu sannanun mata Helenawa da maza da yawa.
Therefore, many of them believed; both of influential women, who were Greeks, and of men, not a few.
13 Amma da Yahudawan Tasalunika suka ji cewa Bulus yana wa'azin kalmar Allah a Biriya, sun haura can, sun tada hankulan jama'a.
But when the Jews of Thessalonica learned that the word of God was preached by Paul in Berea also, they came thither, and excited the multitude.
14 Nan da nan, masu bi na Biriya sun dauki Bulus sun aika shi zuwa teku, an bar Sila da Timoti a Biriya tukuna.
Then the brethren immediately sent Paul away, to go as if to the sea; but Silas and Timothy remained there.
15 Wadanda sun fitar da Bulus, sun kai shi har zuwa birnin Atina. Bulus ya ba su sako, su fada wa Sila da Timoti suyi hanzari su same shi.
And those who conducted Paul brought him to Athens: and having received a commandment for Silas and Timothy, that they should come to him as soon as possible, they departed.
16 Sa'anda Bulus yana jiran zuwan Sila da Timoti a Atina, ya yi fushi a ransa, da ya ga birnin cike da gumakai.
Now while Paul was waiting for them at Athens, his spirit was stirred within him, when he saw the city full of idols.
17 Ya tattauna da Yahudawa a cikin majami'a tare da masu yin sujada ga Allah, da kuma wadanda yake samu a kowace rana, a kasuwa.
Accordingly, he reasoned in the synagogue with the Jews and devout persons, and in the market daily, with those who chanced to meet him.
18 Amma wadan su Abikuriyawa da masana sun yi karo da shi. Wadansun su na cewa, ''Menene wannan sakaren ke cewa?'' Wadansu kuma sun ce, ''Da alama mai wa'azi ne na wasu alloli dabam,'' domin yana wa'azin Yesu da tashin sa daga matattu.
And some of the Epicurean and Stoic philosophers disputed with him; and some said: What can this babbler possibly wish to say? Others said: He seems to be a proclaimer of strange demons: for he preached to them Jesus and the Resurrection.
19 Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, ''Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka?
And they took him, and brought him to Mars hill, saying: Are we able to understand what this new teaching is, which is announced by you?
20 Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su.''
For you bring some strange things to our ears: we wish to understand then what these things mean.
21 (Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su).
For all the Athenians and resident strangers have leisure for nothing else than to tell or to hear some new thing.
22 Bulus ya tsaya a tsakiyar Tudun Arasa ya ce, ''Ku mutanen Atiniya na lura masu kwazon addini ne ku.
Then Paul stood in the midst of Mars hill, and said: Men of Athens, I perceive that in all respects your reverence for demons excels that of other men.
23 Na lura da abubuwan sujadar ku yayin da nake zagawa, amma na ga wani bagadi da rubutu a kansa mai cewa, ''Ga Allah wanda ba a sani ba.” Abin da kuke bauta wa cikin rashin sani, shi nake sanar maku.
For as I was passing through, and looking attentively at the objects of your worship, I dis covered also an altar with this inscription: TO THE UNKNOWN GOD. Whom therefore you ignorantly worship, him I make known to you.
24 Allahn da ya yi duniya da kome da ke cikinta, tun da ya ke shine Ubangijin sama da kasa, ba ya zama a haikalin da mutane suka gina da hannu.
God, who made the world, and all things that are in it, being Lord of heaven and earth, dwells not in temples made with hands;
25 Ba ya neman taimakon kowa, babu kuma wanda ya isa ya ba shi. Shine ke ba da rai, da numfashi da kowanne abu.
nor is he ministered to by the hands of men, as if he needed any thing: for he himself gives to all life, and breath, and all things:
26 Daga mutum daya ya hallici dukan al'umman duniya, ya rarraba, ya kuma sanya kowa a inda ya shirya masa.
and he has made from one blood every nation of men, that they might dwell on all the face of the earth, having marked out their appointed times, and the bounds of their dwelling:
27 Domin su nemi Allah ko za su iya kaiwa zuwa gareshi su same shi, ga shi kuwa ba ya nesa da kowannenmu.
that they might seek for God, if perhaps they would feel after him, and find him, although, indeed, he is not far from every one of us.
28 A cikinsa muke rayuwa, muna walwala, kamar yadda wani daga cikin masananku yace, 'Mu 'ya'yansa ne'.
For in him we live, and move, and have our being: as also some of your own poets have said: For we his offspring are.
29 Idan mu 'ya'yan Allah ne, bai kamata mu danganta Allah da zinariya ko azurfa, ko kuma duwatsu da itatuwa da an sassaka ba.
Therefore, being the offspring of God, we ought not to think that the Godhood is like gold, or silver, or stone, sculptured by art and the device of man.
30 Saboda haka ne, Allah ya kawar da kwanakin jahilci, amma ya ba da umarni kowa a ko'ina ya tuba.
Yet the times of this ignorance God overlooked; but now, he commands all men everywhere to repent:
31 Akwai ranar da ya shirya zai yi wa duniya shari'a cikin adalci, ta wurin mutumin da ya zaba. Allah ya nuna wannan mutumin, ta wurin ta da shi daga matattu''.
because he has appointed a day in which he will judge the world, in righteousness, by the man whom he has chosen, giving to all assurance of this, by having raised him from the dead.
32 Da mutanen Atina sun ji batun tashi daga matattu, wadansu suka yi wa Bulus ba'a; amma wadansu kuma sun ce, ''Za mu saurare ka kuma, a kan wannan maganar.''
And when they heard of the resurrection of the dead, some mocked; others said: We will hear you again concerning this matter.
33 Bayan haka, Bulus ya bar su.
And so Paul departed from among them.
34 Amma wasu maza a cikinsu sun yarda da bisharar, sun ba da gaskiya, hade da Diyonisiyus dan Majalisar Tudun Arasa da wata mace mai suna Damaris, da wadansu tare da su.
But certain men associated with him, and believed; among whom was Dionysius the Areopagite, and a woman named Damaris, and others with them.

< Ayyukan Manzanni 17 >