< Waƙar Waƙoƙi 7 >
1 Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, Ya diyar sarki! Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, aikin hannun gwanin sassaƙa.
Hvor skønne er dine Trin i Skoene, du ædelbårne! Dine Hofters Runding er som Halsbånd, Kunstnerhånds Værk,
2 Cibinki kamar kwaf ne da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama wanda furen bi-rana ya kewaye.
dit Skød som det runde Bæger, ej savne det Vin, dit Liv som en Hvededynge, hegnet af Liljer;
3 Nonanki sun yi kamar bareyi biyu, tagwayen barewa.
dit Bryst som to Hjortekalve, Gazelletvillinger,
4 Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus.
din Hals som Elfenbenstårnet, dine Øjne som Hesjbons damme ved Bat-Rabbims Port, din Næse som Libanons Tårn, der ser mod Damaskus,
5 Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. Gashinki ya yi kamar shunayya; yakan ɗauke hankalin sarki.
Hovedet på dig som Karmel, dit Hoveds Lokker som Purpur; en Konge er fanget i Garnet.
6 Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!
Hvor er du fager og yndig, du elskede, yndefulde!
7 Tsayinki ya yi kamar itacen dabino, kuma nonanki sun yi kamar’ya’yan itace.
Som Palmen, så er din Vækst, dit Bryst som Klaser.
8 Na ce, “Zan hau itacen dabino; zan kama’ya’yansa.” Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa, ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,
Jeg tænker: Jeg vil op i Palmen, gribe fat i dens Stilke; dit Bryst skal være som Vinstokkens Klaser, din Næses Ånde som Æbleduft,
9 kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. Ƙaunatacciya Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.
din Gane som ædel Vin, der liflig flyder ind i min Mund, glider over mine Læber og Tænder.
10 Ni ta ƙaunataccena ce, kuma sha’awarsa domina ne.
Jeg er min Vens, og til mig står hans Attrå.
11 Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari, bari mu kwana a ƙauye.
Kom min Ven, vi vil ud på Landet, blive i Landsbyer Natten over;
12 Bari mu tafi gonar inabi da sassafe don mu ga ko kuringar ta yi’ya’ya, ko furanninsu sun buɗe, ko rumman sun yi fure, a can zan nuna maka ƙaunata.
Vingårde søger vi årle, vi ser, om Vinstokken skyder, om Knopperne åbnes, Granattræet blomstrer. Der giver jeg dig min Kærlighed.
13 Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, sabo da tsoho, da na ajiye dominka, ƙaunataccena.
Kærlighedsæblerne dufter, for vor Dør er al Slags Frugt, ny og gammel tillige; til dig, min Ven, har jeg gemt dem.