Preface
Read
+
Publisher
Nainoia, Inc.
PO Box 462, Bellefonte, PA 16823
(814) 470-8028
Nainoia Inc, Publisher
LinkedIn/NAINOIA-INC
Third Party Publisher Resources
Request Custom Formatted Verses
Please contact us below
Submit your proposed corrections
I understand that the Aionian Bible republishes public domain and Creative Commons Bible texts and that volunteers may be needed to present the original text accurately. I also understand that apocryphal text is removed and most variant verse numbering is mapped to the English standard. I have entered my corrections under the verse(s) below. Proposed corrections to the Hausa Contemporary Bible, Song-of-Solomon Chapter 7 https://www.AionianBible.org/Bibles/Hausa---Contemporary/Song-of-Solomon/7 1) Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, Ya diyar sarki! Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, aikin hannun gwanin sassaƙa. 2) Cibinki kamar kwaf ne da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama wanda furen bi-rana ya kewaye. 3) Nonanki sun yi kamar bareyi biyu, tagwayen barewa. 4) Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus. 5) Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. Gashinki ya yi kamar shunayya; yakan ɗauke hankalin sarki. 6) Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo! 7) Tsayinki ya yi kamar itacen dabino, kuma nonanki sun yi kamar’ya’yan itace. 8) Na ce, “Zan hau itacen dabino; zan kama’ya’yansa.” Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa, ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa, 9) kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. Ƙaunatacciya Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora. 10) Ni ta ƙaunataccena ce, kuma sha’awarsa domina ne. 11) Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari, bari mu kwana a ƙauye. 12) Bari mu tafi gonar inabi da sassafe don mu ga ko kuringar ta yi’ya’ya, ko furanninsu sun buɗe, ko rumman sun yi fure, a can zan nuna maka ƙaunata. 13) Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, sabo da tsoho, da na ajiye dominka, ƙaunataccena. Additional comments?
Refresh Captcha
The world's first Holy Bible un-translation!