< Ru’uya ta Yohanna 19 >

1 Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa, “Halleluya! Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu,
After these things, I heard as it were, a loud voice of a great multitude in heaven, saying—Hallelujah! The salvation and the glory and the power of our God!
2 gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma. Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta. Ya rama jinin bayinsa a kanta.”
Because, true and righteous, are his judgments; because he hath judged the great harlot, who, indeed, corrupted the earth with her lewdness, —and hath avenged the blood of his servants, at her hand.
3 Suka sāke tā da murya suka ce, “Halleluya! Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.” (aiōn g165)
And, a second time, have they said—Hallelujah! And, her smoke, ascendeth unto ages of ages. (aiōn g165)
4 Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce, “Amin, Halleluya!”
And the twenty-four elders and the four living creatures, fell down, and did homage unto God, who sitteth upon the throne, saying—Amen! Hallelujah!
5 Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku da kuke bayinsa, ku da kuke tsoronsa, babba da yaro!”
And, a voice, from the throne, came forth, saying—Be giving praise unto our God, all ye his servants, ye that revere him, the small and the great.
6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.
And I heard as a voice of a great multitude, and as a voice of many waters, and as a voice of mighty thunderings, saying—Hallelujah! Because the Lord, [our] God, the Almighty, hath become king.
7 Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta.
Let us rejoice and exult, and give glory unto him, because the marriage of the Lamb, is come, and, his wife, hath made herself ready;
8 Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta ta sanya.” (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.)
and it hath been given unto her, that she should be arrayed in fine linen, bright, pure, for, the fine linen, is, the righteous acts of the saints.
9 Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”
And he saith unto me—Write! Happy, they who, unto the marriage supper of the Lamb, have been bidden! And he saith unto me—These words, are, true [words] of God.
10 Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”
And I fell down at his feet, to do him homage; and he saith unto me—See! [thou do it] not! A fellow-servant, am I, of thee and of thy brethren who have the witness of Jesus: unto God, do homage! For, the witness of Jesus, is the spirit of the prophecy.
11 Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi.
And I saw heaven, set open, and lo! a white horse, and, he that was sitting thereon, [called] Faithful, and True; and, in righteousness, doth he judge and make war;
12 Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi.
and, his eyes, are a flame of fire, and, upon his head, are many diadems, having, a name, written, which, no one, knoweth, but himself,
13 Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne.
and arrayed with a mantle sprinkled with blood, and his name hath been called—The Word of God.
14 Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin.
And, the armies which were in heaven, were following him, upon white horses, clothed with fine linen, white, pure;
15 Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki.
and, out of his mouth, is going forth a sharp sword, that, therewith, he may smite the nations, —and, he, shall shepherd them with a sceptre of iron, and, he, treadeth the wine-press of the wrath of the anger of God the Almighty.
16 A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.
And he hath, upon his mantle and upon his thigh, a name, written—King of kings, and Lord of lords.
17 Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah,
And I saw one messenger, standing in the sun, and he cried out with a loud voice, saying, unto all the birds that fly in mid-heaven, —Hither! be gathered together unto the great supper of God, —
18 don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane,’yantacce da bawa, babba da yaro.”
that ye may eat the flesh of kings, and the flesh of captains, and the flesh of mighty men, and the flesh of horses, and of them who sit upon them, and the flesh of all, both free and bond, and small and great.
19 Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa.
And I saw the wild-beast, and the kings of the earth, and their armies, gathered together—to make war with him who was sitting upon the horse, and with his army.
20 Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. (Limnē Pyr g3041 g4442)
And the wild-beast, was taken, and, with him, the false prophet who wrought the signs before him, whereby he deceived them who received the mark of the wild-beast and them who were doing homage unto his image, —alive, were they two cast into the lake of fire that burneth with brimstone. (Limnē Pyr g3041 g4442)
21 Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.
And, the rest, were slain with the sword of him that was sitting upon the horse, which went forth out of his mouth, and, all the birds, were filled with their flesh.

< Ru’uya ta Yohanna 19 >