< Zabura 85 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub.
For the end, a Psalm for the sons of Core. O Lord, you has taken pleasure in your land: you have turned back the captivity of Jacob.
2 Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. (Sela)
You have forgiven your people their transgressions; you has covered all their sins. (Pause)
3 Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka.
You has caused all your wrath to cease: you have turned from your fierce anger.
4 Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
Turn us, O God of our salvation, and turn your anger away from us.
5 Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?
Wouldest you be angry with us for ever? or will you continue your wrath from generation to generation?
6 Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?
O God, you will turn and quicken us; and your people shall rejoice in you.
7 Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka.
Show us your mercy, O Lord, and grant us your salvation.
8 Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta.
I will hear what the Lord God will say concerning me: for he shall speak peace to his people, and to his saints, and to those that turn their heart towards him.
9 Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
Moreover his salvation is near them that fear him; that glory may dwell in our land.
10 Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba.
Mercy and truth are met together: righteousness and peace have kissed [each other].
11 Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa, adalci kuma yă duba daga sama.
Truth has sprung out of the earth; and righteousness has looked down from heaven.
12 Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.
For the Lord will give goodness; and our land shall yield her fruit.
13 Adalci na tafiya a gabansa yana shirya hanya domin ƙafafunsa.
Righteousness shall go before him; and shall set his steps in the way.