< Zabura 67 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, (Sela)
To the chief music-maker. With corded instruments. A Psalm. A Song. May God give us mercy and blessing, and let the light of his face be shining on us; (Selah)
2 don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.
So that men may see your way on the earth, and your salvation among all nations.
3 Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.
Let the peoples give you praise, O God; let all the peoples give you praise.
4 Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. (Sela)
O let the nations be glad, and make song of joy; for you will be the judge of the peoples in righteousness, guiding the nations of the earth. (Selah)
5 Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.
Let the peoples give you praise, O God; let all the peoples give you praise.
6 Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.
The earth has given her increase; and God, even our God, will give us his blessing.
7 Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.
God will give us his blessing; so let all the ends of the earth be in fear of him.

< Zabura 67 >