< Zabura 36 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa.
2 Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.
3 Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri.
4 Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.
5 Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai.
6 Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.
7 Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.
8 Suna biki a yalwar gidanka; kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.
9 Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai cikin haskenka mukan ga haske.
10 Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka, adalcinka ga masu gaskiyar zuciya.
11 Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini, ko hannun mugu ya kore ni.
12 Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi, a zube, ba za su kuwa iya tashi ba!