< Zabura 26 >
1 Ta Dawuda. Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba.
2 Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina;
3 gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.
4 Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya;
5 na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye.
6 Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,
7 ina shelar yabonka da ƙarfi ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.
8 Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune.
9 Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi raina tare da masu son yin kisankai
10 waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu, waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.
11 Amma na yi rayuwa marar zargi; ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.
12 Ƙafafuna suna tsaye daram; cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.