< Zabura 20 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.
For the chief musician. A psalm of David. May Yahweh help you in the day of trouble; may the name of the God of Jacob protect you
2 Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.
and send help from the holy place to support you from Zion.
3 Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. (Sela)
May he call to mind all your offerings and accept your burnt sacrifice. (Selah)
4 Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
May he grant you your heart's desire and fulfill all your plans.
5 Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.
Then we will rejoice in your victory, and, in the name of our God, we will raise banners. May Yahweh grant all your petitions.
6 Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa.
Now I know that Yahweh will rescue his anointed one; he will answer him from his holy heaven with the strength of his right hand that can rescue him.
7 Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.
Some trust in chariots and others in horses, but we call on Yahweh our God.
8 Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram.
They will be brought down and fall, but we will rise and stand upright!
9 Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!
Yahweh, rescue the king; help us when we call.