Preface
Read
+
Publisher
Nainoia, Inc.
PO Box 462, Bellefonte, PA 16823
(814) 470-8028
Nainoia Inc, Publisher
LinkedIn/NAINOIA-INC
Third Party Publisher Resources
Request Custom Formatted Verses
Please contact us below
Submit your proposed corrections
I understand that the Aionian Bible republishes public domain and Creative Commons Bible texts and that volunteers may be needed to present the original text accurately. I also understand that apocryphal text is removed and most variant verse numbering is mapped to the English standard. I have entered my corrections under the verse(s) below. Proposed corrections to the Hausa Contemporary Bible, Psalms Chapter 20 https://www.AionianBible.org/Bibles/Hausa---Contemporary/Psalms/20 1) Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka. 2) Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona. 3) Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. (Sela) 4) Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara. 5) Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka. 6) Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa. 7) Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu. 8) Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram. 9) Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira! Additional comments?
Refresh Captcha
The world's first Holy Bible un-translation!