< Zabura 137 >
1 A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona.
2 A can a kan rassan itatuwa muka rataye garayunmu,
3 gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”
4 Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji a baƙuwar ƙasa?
5 In na manta da ke, ya Urushalima, bari hannuna na dama manta da iyawarsa.
6 Bari harshena yă manne wa rufin bakina in ban tuna da ke ba, in ban so Urushalima farin cikin mafi girma ba.
7 Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi a ranar da Urushalima ta fāɗi. Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta, A ragargaza ta har tushenta!”
8 Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka, mai farin ciki ne wanda ya sāka miki saboda abin da kika yi mana,
9 shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu.