< Zabura 132 >

1 Waƙar haurawa. Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda da kuma dukan irin wuyan da ya jimre.
ヱホバよねがはくはダビデの爲にそのもろもろの憂をこころに記たまへ
2 Ya yi rantsuwa ga Ubangiji ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,
ダビデ、ヱホバにちかひヤコブの全能者にうけひていふ
3 “Ba zan shiga gidana ko in kwanta a gado ba,
われヱホバのために處をたづねいだし ヤコブの全能者のために居所をもとめうるまでは 我家の幕屋にいらず わが臥床にのぼらず わが目をねぶらしめず わが眼瞼をとぢしめざるべしと
4 ba zan ba wa idanuna barci ba, ba gyangyaɗi wa idanuna,
われヱホバのために處をたづねいだし ヤコブの全能者のために居所をもとめうるまでは 我家の幕屋にいらず わが臥床にのぼらず わが目をねぶらしめず わが眼瞼をとぢしめざるべしと
5 sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”
われヱホバのために處をたづねいだし ヤコブの全能者のために居所をもとめうるまでは 我家の幕屋にいらず わが臥床にのぼらず わが目をねぶらしめず わが眼瞼をとぢしめざるべしと
6 Mun ji haka a Efrata, muka yi ƙaro da shi a filayen Ya’ar,
われらエフラタにて之をききヤアルの野にて見とめたり
7 “Bari mu tafi wurin zamansa; bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa,
われらはその居所にゆきて その承足のまへに俯伏さん
8 ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.
ヱホバよねがはくは起きて なんぢの稜威の櫃とともになんぢの安居所にいりたまへ
9 Bari a suturta firistocinka da adalci; bari tsarkakanka su rera don farin ciki.”
なんぢの祭司たちは義を衣 なんぢの聖徒はみな歓びよばふべし
10 Saboda Dawuda bawanka, kada ka ƙi shafaffenka.
なんぢの僕ダビデのためになんぢの受膏者の面をしりぞけたまふなかれ
11 Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,
ヱホバ眞實をもてダビデに誓ひたまひたれば之にたがふことあらじ 曰くわれなんぢの身よりいでし者をなんぢの座位にざせしめん
12 in’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari da farillan da na koya musu, to’ya’yansu maza za su zauna a kan kursiyinka har abada abadin.”
なんぢの子輩もしわがをしふる契約と證詞とをまもらばかれらの子輩もまた永遠になんぢの座位にざすべしと
13 Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa,
ヱホバはシオンを擇びておのが居所にせんとのぞみたまへり
14 “Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin; a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta,
曰くこれは永遠にわが安居處なり われここに住ん そはわれ之をのぞみたればなり
15 zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa; matalautanta za su ƙoshi da abinci.
われシオンの糧をゆたかに祝し くひものをもてその貧者をあかしめん
16 Zan suturta firistocinta da ceto, tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki.
われ救をもてその祭司たちに衣せん その聖徒はみな聲たからかによろこびよばふべし
17 “A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda in kuma kafa fitila saboda shafaffena.
われダビデのためにかしこに一つの角をはえしめん わが受膏者のために燈火をそなへたり
18 Zan suturta abokan gābansa da kunya, amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.”
われかれの仇にはぢを衣せん されどかれはその冠弁さかゆべし

< Zabura 132 >