< Zabura 13 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Har yaushe, ya Ubangiji? Za ka manta da ni har abada ne? Har yaushe za ka ɓoye fuskarka daga gare ni?
למנצח מזמור לדוד
2 Har yaushe zan yi kokawa da tunanina kuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata? Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina?
עד-אנה יהוה תשכחני נצח עד-אנה תסתיר את-פניך ממני
3 Ka dube ni ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna. Ka ba da haske ga fuskata, ko in yi barci cikin mutuwa;
עד-אנה אשית עצות בנפשי-- יגון בלבבי יומם עד-אנה ירום איבי עלי
4 abokin gābana zai ce, “Na sha ƙarfinsa,” kuma abokan gābana za su yi murna sa’ad da na fāɗi.
הביטה ענני יהוה אלהי האירה עיני פן-אישן המות
5 Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa; zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.
פן-יאמר איבי יכלתיו צרי יגילו כי אמוט
6 Zan rera ga Ubangiji gama ya yi mini alheri.
ואני בחסדך בטחתי-- יגל לבי בישועתך אשירה ליהוה כי גמל עלי

< Zabura 13 >