< Zabura 126 >
1 Waƙar haurawa. Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.
都もうでの歌 主がシオンの繁栄を回復されたとき、われらは夢みる者のようであった。
2 Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”
その時われらの口は笑いで満たされ、われらの舌は喜びの声で満たされた。その時「主は彼らのために大いなる事をなされた」と言った者が、もろもろの国民の中にあった。
3 Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki.
主はわれらのために大いなる事をなされたので、われらは喜んだ。
4 Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb.
主よ、どうか、われらの繁栄を、ネゲブの川のように回復してください。
5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.
涙をもって種まく者は、喜びの声をもって刈り取る。
6 Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.
種を携え、涙を流して出て行く者は、束を携え、喜びの声をあげて帰ってくるであろう。