< Zabura 125 >
1 Waƙar haurawa. Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona, wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.
A Song of Ascents. They that trust in the LORD are as mount Zion, which cannot be moved, but abideth for ever.
2 Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, haka Ubangiji ya kewaye mutanensa yanzu da har abada kuma.
As the mountains are round about Jerusalem, so the LORD is round about His people, from this time forth and for ever.
3 Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance a kan ƙasar da take rabon adalai ba, domin kada masu adalci su yi amfani da hannuwansu su aikata mugunta.
For the rod of wickedness shall not rest upon the lot of the righteous; that the righteous put not forth their hands unto iniquity.
4 Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu, ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.
Do good, O LORD, unto the good, and to them that are upright in their hearts.
5 Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta. Salama tă kasance tare da Isra’ila.
But as for such as turn aside unto their crooked ways, the LORD will lead them away with the workers of iniquity. Peace be upon Israel.