< Zabura 122 >

1 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.” 2 Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima. 3 An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda. 4 A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila. 5 A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda. 6 Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya. 7 Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.” 8 Saboda’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.” 9 Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki.

< Zabura 122 >