< Zabura 122 >
1 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.”
2 Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima.
3 An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda.
4 A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.
5 A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda.
6 Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.
7 Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.”
8 Saboda’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”
9 Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki.