< Zabura 113 >
1 Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji.
2 Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma.
3 Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji.
4 Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai
5 Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa,
6 wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya?
7 Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;
8 ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu.
9 Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji.