< Karin Magana 7 >

1 Ɗana, ka kiyaye kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka.
My son, keep my words, And treasure up my commandments with thee!
2 Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu; ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka.
Keep my commandments and live! Yea, my teaching, as the apple of thine eye!
3 Ka daure su a yatsotsinka; ka rubuta su a allon zuciyarka.
Bind them upon thy fingers, Write them upon the tablet of thy heart!
4 Ka faɗa wa hikima, “Ke’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka;
Say unto wisdom, “Thou art my sister!” And call understanding thy near acquaintance;
5 za su kiyaye ka daga mazinaciya, daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali.
That they may keep thee from the wife of another, From the stranger, that useth smooth words.
6 A tagar gidana na leƙa ta labule mai rammuka.
For through the window of my house, Through the lattice I was looking forth,
7 Sai na gani a cikin marasa azanci, na lura a cikin samari, wani matashi wanda ba shi da hankali.
And I saw among the simple ones, I discerned among the youths, A young man void of understanding.
8 Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta, yana tafiya a gefen wajen gidanta
He was passing through the street near her corner, And was going the way to her house,
9 da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa, yayinda duhun dare yana farawa.
At twilight, in the evening, At midnight, yea, in the thick darkness.
10 Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi, saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi.
And, behold, a woman met him, In the attire of a harlot, and subtle of heart, —
11 (Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya, ƙafafunta ba sa zama a gida;
One noisy and unruly, Whose feet abide not in her house;
12 wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali, tana yawo a kowace kusurwa.)
Who is now in the streets, now in the broad places, And lurketh near every corner.
13 Sai ta kama shi ta rungume shi da duban soyayya a fuskarta ta ce,
She caught hold of him and kissed him, And with a shameless face said to him,
14 “Ina da hadaya ta salama a gida; yau zan cika alkawarina.
“Thank-offerings have been upon me, And this day have I performed my vows;
15 Saboda haka na fito don in sadu da kai; na neme ka na kuma same ka!
Therefore came I forth to meet thee, —Diligently to seek thy face, and I have found thee!
16 Na lulluɓe gadona da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.
I have spread my bed with coverlets, With tapestry of the thread of Egypt.
17 Na yayyafa turare a gadona da mur, aloyes da kuma kirfa.
I have sprinkled my bed With myrrh, aloes, and cinnamon.
18 Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe; bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!
Come, let us take our fill of love until the morning; Let us solace ourselves with caresses.
19 Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa.
For the good-man is not at home; He is gone a long journey;
20 Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”
He hath taken a purse of money with him; At the day of the full moon he will return.”
21 Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.
By her much fair speech she seduced him; By the smoothness of her lips she drew him away.
22 Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo
He goeth after her straightway, As an ox goeth to the slaughter, Or as one in fetters to the chastisement of the fool,
23 sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.
Till an arrow strike through his liver; —As a bird hasteneth into the snare, And knoweth not that it is laid for its life.
24 Yanzu fa,’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.
Now, therefore, ye children, hearken to me, And attend to the words of my mouth!
25 Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta.
Let not thy heart turn aside to her ways; Go not astray in her paths!
26 Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.
For many are the wounded which she hath cast down; Yea, countless is the number of those slain by her.
27 Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira. (Sheol h7585)
Her house is the way to the under-world, Leading down to the chambers of death. (Sheol h7585)

< Karin Magana 7 >