< Karin Magana 31 >

1 Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriya mahaifiyarsa ta koya masa,
דברי למואל מלך משא אשר יסרתו אמו׃
2 “Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina! Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!
מה ברי ומה בר בטני ומה בר נדרי׃
3 Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata, ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna.
אל תתן לנשים חילך ודרכיך למחות מלכין׃
4 “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel, ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi, ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,
אל למלכים למואל אל למלכים שתו יין ולרוזנים או שכר׃
5 don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta, su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.
פן ישתה וישכח מחקק וישנה דין כל בני עני׃
6 A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;
תנו שכר לאובד ויין למרי נפש׃
7 bari su sha su manta da talaucinsu kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.
ישתה וישכח רישו ועמלו לא יזכר עוד׃
8 “Yi magana domin bebaye, domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.
פתח פיך לאלם אל דין כל בני חלוף׃
9 Yi magana a kuma yi shari’ar adalci; a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”
פתח פיך שפט צדק ודין עני ואביון׃
10 Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.
אשת חיל מי ימצא ורחק מפנינים מכרה׃
11 Mijinta yana da cikakken amincewa da ita kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.
בטח בה לב בעלה ושלל לא יחסר׃
12 Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakin ranta.
גמלתהו טוב ולא רע כל ימי חייה׃
13 Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.
דרשה צמר ופשתים ותעש בחפץ כפיה׃
14 Ita kamar jirgin’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa.
היתה כאניות סוחר ממרחק תביא לחמה׃
15 Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
ותקם בעוד לילה ותתן טרף לביתה וחק לנערתיה׃
16 Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.
זממה שדה ותקחהו מפרי כפיה נטע כרם׃
17 Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.
חגרה בעוז מתניה ותאמץ זרעותיה׃
18 Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.
טעמה כי טוב סחרה לא יכבה בליל נרה׃
19 Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.
ידיה שלחה בכישור וכפיה תמכו פלך׃
20 Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata.
כפה פרשה לעני וידיה שלחה לאביון׃
21 Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri.
לא תירא לביתה משלג כי כל ביתה לבש שנים׃
22 Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.
מרבדים עשתה לה שש וארגמן לבושה׃
23 Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari.
נודע בשערים בעלה בשבתו עם זקני ארץ׃
24 Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa’yan kasuwa da ɗamara.
סדין עשתה ותמכר וחגור נתנה לכנעני׃
25 Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.
עז והדר לבושה ותשחק ליום אחרון׃
26 Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.
פיה פתחה בחכמה ותורת חסד על לשונה׃
27 Tana lura da sha’anin gidanta kuma ba ta cin abincin ƙyuya.
צופיה הליכות ביתה ולחם עצלות לא תאכל׃
28 ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka; haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,
קמו בניה ויאשרוה בעלה ויהללה׃
29 “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo, amma ke kin fi su duka.”
רבות בנות עשו חיל ואת עלית על כלנה׃
30 Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe; amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
שקר החן והבל היפי אשה יראת יהוה היא תתהלל׃
31 Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta, bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.
תנו לה מפרי ידיה ויהללוה בשערים מעשיה׃

< Karin Magana 31 >