< Mai Hadishi 1 >

1 Kalmomin Malami, ɗan Dawuda, Sarki a Urushalima.
דברי קהלת בן דוד מלך בירושלם׃
2 “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami. “Gaba ɗaya ba amfani! Kome ba shi da amfani!”
הבל הבלים אמר קהלת הבל הבלים הכל הבל׃
3 Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar da yake fama a duniya?
מה יתרון לאדם בכל עמלו שיעמל תחת השמש׃
4 Zamanai sukan zo zamanai su wuce, amma duniya tana nan har abada.
דור הלך ודור בא והארץ לעולם עמדת׃
5 Rana takan fito rana ta kuma fāɗi, ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.
וזרח השמש ובא השמש ואל מקומו שואף זורח הוא שם׃
6 Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa; tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.
הולך אל דרום וסובב אל צפון סובב סבב הולך הרוח ועל סביבתיו שב הרוח׃
7 Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku, duk da haka teku ba ya cika. Daga inda rafuffukan suke fitowa, a can suke komawa kuma.
כל הנחלים הלכים אל הים והים איננו מלא אל מקום שהנחלים הלכים שם הם שבים ללכת׃
8 Dukan abubuwa suna kawo gajiya, gaban magana. Ido ba ya gaji da gani, haka ma kunne yă ƙoshi da ji.
כל הדברים יגעים לא יוכל איש לדבר לא תשבע עין לראות ולא תמלא אזן משמע׃
9 Abin da ya taɓa kasancewa, zai sāke kasance, abin da aka yi za a sāke yi kuma; babu wani abu sabo a duniya.
מה שהיה הוא שיהיה ומה שנעשה הוא שיעשה ואין כל חדש תחת השמש׃
10 Akwai wani abin da za a ce, “Duba! Ga wani abu sabo”? Abin yana nan, tun dā can, ya kasance kafin lokacinmu.
יש דבר שיאמר ראה זה חדש הוא כבר היה לעלמים אשר היה מלפננו׃
11 Ba a tunawa da mutanen dā, haka su ma da ba a haifa ba tukuna waɗanda za su biyo bayansu ba za a tuna da su ba.
אין זכרון לראשנים וגם לאחרנים שיהיו לא יהיה להם זכרון עם שיהיו לאחרנה׃
12 Ni, Malami, sarki ne bisa Isra’ila a Urushalima.
אני קהלת הייתי מלך על ישראל בירושלם׃
13 Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane!
ונתתי את לבי לדרוש ולתור בחכמה על כל אשר נעשה תחת השמים הוא ענין רע נתן אלהים לבני האדם לענות בו׃
14 Na ga dukan abubuwan da ake yi a duniya, dukansu ba su da amfani, naushin iska ne kawai.
ראיתי את כל המעשים שנעשו תחת השמש והנה הכל הבל ורעות רוח׃
15 Abin da yake tanƙwararre ba zai miƙu ba; ba za a kuma iya ƙidaya abin da ba shi ba.
מעות לא יוכל לתקן וחסרון לא יוכל להמנות׃
16 Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.”
דברתי אני עם לבי לאמר אני הנה הגדלתי והוספתי חכמה על כל אשר היה לפני על ירושלם ולבי ראה הרבה חכמה ודעת׃
17 Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.
ואתנה לבי לדעת חכמה ודעת הוללות ושכלות ידעתי שגם זה הוא רעיון רוח׃
18 Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki; yawan sani, yawan ɓacin rai.
כי ברב חכמה רב כעס ויוסיף דעת יוסיף מכאוב׃

< Mai Hadishi 1 >