< Markus 14 >
1 To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe.
逾越节和除酵节前两天,祭司长和宗教老师想方设法用诡计逮捕耶稣,然后将其杀害。
2 Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”
但他们暗想:“不可在节日期间下手,免得引发民众暴动。”
3 Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.
耶稣这段时间在伯大尼。一天他在麻风病人西门家里吃饭时,一个女人前来,拿着一瓶非常昂贵的甘松纯香膏。她打破瓶身,把香膏倒在耶稣的头上。
4 Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka?
那里的人中,有人很生气地说:“为什么这样浪费香膏呢?
5 Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.”
这香膏的钱值一年的薪水,应该用来接济穷人。”他们对她感到很愤怒。
6 Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni.
但耶稣说:“让她这么做!她对我做了一件美好的事情,为何要批判她?”
7 Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.
你们常与穷苦人在一起,可以随时帮助他们。但你们不常和我在一起。
8 Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata.
她已尽其所能在我被安葬之前,提前用香膏涂上我的身体。
9 Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”
告诉你们实话,无论福音传到世界何处,人们世界都会记得她的所作所为。
10 Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su.
这时,十二门徒中的的加略人犹大跑去见祭司长,要把耶稣出卖给他们。
11 Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.
他们听此甚是欢喜,就答应给他好处,于是犹大就开始寻找出卖耶稣的机会。
12 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
除酵节的第一天,也是宰杀逾越节羊羔的那一天,门徒问耶稣:“你想要我们到哪里为你预备逾越节晚餐呢?”
13 Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.
耶稣派出两名门徒,对他们说:“你们去城里,看到一个拿着水瓶之人向你们迎面走来,就跟着他。
14 Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’
无论他进入谁家,就询问那家的主人,我和门徒应该在哪里庆祝逾越节。
15 Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.”
他必带你们去楼上一个大房间处,那里已经布置整齐,预备妥当,你们在那里为我们做准备就好了。”
16 Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.
门徒离开了,他们进了城,果真遇到了耶稣所说之事,于是预备好了逾越节的晚餐。
17 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun.
到了晚上,耶稣和十二门徒过来了。
18 Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.”
在用餐的过程中,耶稣说:“告诉你们实话,你们中间有一个人要出卖我。”
19 Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?”
门徒们都很震惊,纷纷询问:“是我吗,是吗?”
20 Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano.
耶稣对他们说:“他是十二门徒里的一人,就是与我分享食物之人中的一个。”
21 Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”
正如经文所预言:“人子将逝,但出卖人子之人必有灾祸!而且那人如果没有降生才好。”
22 Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”
他们用餐时,耶稣拿起饼,祝福后把饼分给众人,说:“拿去吃吧,这是我的身体。”
23 Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.
他又拿起杯子,祝福后把它递给门徒,他们都喝了。
24 Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa.
耶稣说:“这是我的血,为众人而流,用于立约。
25 Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’”
告诉你们实话,从今后我不再喝葡萄酒,直到我在上帝之国品尝新酒。”
26 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
他们吟唱完圣歌后开始向橄榄山而去。
27 Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa, “‘Zan bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.’
耶稣告诉他们:“你们所有人都会放弃我,因为经文上记着:‘我要攻击牧人,羊群就彻底散了。’
28 Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
但在我复活后,要比你们先到加利利。”
29 Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”
彼得对他说:“就算所有的人都弃你而去,我也不会。”
30 Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyukai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”
耶稣对他说:“我告诉你实话,就在今天晚上,鸡叫两遍以前,你会有三次不肯认我的情况。”
31 Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.
彼得坚决地说:“就算必须与你同死,我也决不会不认你!”众人也这样说。
32 Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi addu’a.”
他们来到一个名叫客西马尼的地方;耶稣对门徒说:“你们坐在这里,我去祷告了。”
33 Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.
他带上彼得、雅各和约翰,这时开始感到心烦意乱,非常难过。
34 Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.”
耶稣对他们说:“这痛苦如此煎熬,我感到快死了一样。请留在这里,保持警醒。”
35 Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a.
耶稣稍往前了几步,伏在地上祷告,请求如果可能,那必然发生的事情就不要发生。
36 Ya ce, “Ya Abba, Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”
他说:“上帝啊,吾父,你无所不能,那么求你让这次的痛苦远离我。但这不应是我所求的,而是你所要的。”
37 Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na sa’a ɗaya?
耶稣回来后发现门徒睡着了,就对彼得说:“西门,你睡着了吗?难道你连一个小时也不能清醒吗?
38 Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”
保持清醒进行祷告,以免被诱惑征服。你们精神虽然有意愿,但肉体却很软弱。”
39 Ya sāke komawa, ya maimaita addu’ar da ya yi.
耶稣再次离开去祷告,祷告的内容相同。
40 Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa.
他再回来的时候,看见门徒都睡着了,因为他们实在太疲倦了,也不知道该说些什么。
41 Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi.
耶稣第三次回来,对他们说:“你们还在睡觉吗?还在休息吗?那么现在就休息够了,因为时间到了!看,人子即将遭受背叛,将其交给一群罪人。
42 Ku tashi! Mu tafi! Ga mai bashe ni ɗin yana zuwa!”
起来吧,我们走!出卖我的人来了。”
43 Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.
耶稣正说话之际,十二门徒中的犹大和一群手拿刀棒之人前来,这些人都是祭司长、宗教老师和长老所派。
44 Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.”
这个叛徒和他们约好一个暗号:“我亲吻谁,谁就是耶稣。抓住他,让士兵把他押走。”
45 Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba.
犹大来了,对耶稣说:“拉比!”然后亲吻耶稣。
46 Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi.
其他人动手抓住耶稣,把他逮捕。
47 Sai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist.
但站在耶稣身边的一个人拔出自己的刀,砍了大祭司的仆人一刀,削掉他的一只耳朵。
48 Yesu ya ce, “Ina jagoran wani tawaye ne da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni?
耶稣对他们说:“你们带着刀棒而来,是把我当作危险的罪犯捉拿吗?
49 Kowace rana ina tare da ku, ina koyarwa a filin haikali, ba ku kama ni ba. Amma dole a cika Nassi.”
我每天在圣殿中教导众人,跟你们在一起,你们却没有捉拿我。这一切就是为了应验经文所述。”
50 Sai kowa ya yashe shi ya gudu.
这时候,所有门徒都逃跑了,弃他而去。
51 Wani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi,
(有一个年轻的追随者,披着一块麻布。
52 sai ya gudu ya bar rigarsa, ya gudu tsirara.
众人捉住他时,他丢掉麻布,赤身逃跑了。)
53 Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru.
他们把耶稣押到大祭司那里,所有的祭司长、长老和宗教老师都聚集在一起。
54 Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.
彼得远远跟着耶稣,走进大祭司的官邸,和差役们一起火炉旁取暖。
55 Manyan firistoci da dukan’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.
屋子内,祭司长和公议会的所有人都在试图找证据控告耶稣,要把他处死,但什么都没有找到。
56 Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.
虽然有许多人作假证控告他,但他们的证供相互矛盾。
57 Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce,
有几个人站起来,作假证控告他说:
58 “Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’”
“我们听他说过:‘我要拆毁这由人手所建之所,三日之内另建一座并非人手所造的神庙。’”
59 Duk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.
但就是这样的证词,也并不能自圆其说。
60 Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?”
大祭司站起来,走到议会面前,问耶稣:“这些人作证控告你的是什么?你没有什么想说的吗?”
61 Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”
耶稣沉默。大祭司又问他:“你是被祝福的圣子基督吗?”
62 Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”
耶稣说:“我是。你们会看到人子站在万能上帝的右边,驾天上云彩降临。”
63 Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma?
大祭司于是撕开自己的衣服,说:“我们还要什么证人呢?
64 Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Duka suka yanke masa hukuncin kisa.
你们都听见这亵渎之语了。你们认为如何?” 他们都认为他有罪,要求将其处决。
65 Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.
于是有人开始向他吐唾沫,蒙住他的脸,用拳头打他,对他说:“现在你怎么不预言了,你这个‘预言家’!”士兵把他带到一旁,开始殴打他。
66 Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can.
这时候,彼得坐在外面的院子里,大祭司的一个婢女走过来,
67 Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”
看见彼得在烤火,那婢女径直看着他说:“你也是那拿撒勒人耶稣一伙的!”
68 Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.
彼得却否认说:“我不知道你在说什么,不知道你什么意思!”他于是走到前院,这时鸡叫了。
69 Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.”
那婢女看见他在那里,就又对旁边的人说:“这个人也是他们一伙的!”
70 Sai ya sāke yin musu. Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”
彼得再次否认。过了一会,其他人对彼得说:“你真是他们一伙的,因为你也是加利利人。”
71 Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”
彼得就诅咒发誓说:“我不认得你们说的这个人!”
72 Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.
此刻听到公鸡第二次打鸣。彼得想起耶稣对他说过的话:“鸡叫两遍以前,你会有三次不肯认我的情况。”想到这里,他痛哭起来。