< Firistoci 4 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
And the LORD spoke unto Moses, saying:
2 “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da wani ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji,
Speak unto the children of Israel, saying: If any one shall sin through error, in any of the things which the LORD hath commanded not to be done, and shall do any one of them:
3 “‘In shafaffen firist ya yi zunubi, ya jawo wa jama’a laifi, dole yă kawo wa Ubangiji ɗan bijimi marar lahani a matsayin hadaya don zunubi saboda zunubin da ya yi.
if the anointed priest shall sin so as to bring guilt on the people, then let him offer for his sin, which he hath sinned, a young bullock without blemish unto the LORD for a sin-offering.
4 Zai kawo bijimin a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kan bijimin, yă kuma yanka shi a gaban Ubangiji.
And he shall bring the bullock unto the door of the tent of meeting before the LORD; and he shall lay his hand upon the head of the bullock, and kill the bullock before the LORD.
5 Sa’an nan shafaffen firist zai ɗiba jinin bijimin yă kai cikin Tentin Sujada.
And the anointed priest shall take of the blood of the bullock, and bring it to the tent of meeting.
6 Yă tsoma yatsarsa a cikin jinin, yă kuma yafa sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen wuri mai tsarki.
And the priest shall dip his finger in the blood, and sprinkle of the blood seven times before the LORD, in front of the veil of the sanctuary.
7 Sa’an nan firist ɗin zai zuba jinin a ƙahonin bagaden turare masu ƙanshi da suke a gaban Ubangiji a Tentin Sujada. Sauran jinin bijimin zai zuba a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.
And the priest shall put of the blood upon the horns of the altar of sweet incense before the LORD, which is in the tent of meeting; and all the remaining blood of the bullock shall he pour out at the base of the altar of burnt-offering, which is at the door of the tent of meeting.
8 Zai cire dukan kitsen daga bijimin hadaya don zunubi, kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su,
And all the fat of the bullock of the sin-offering he shall take off from it; the fat that covereth the inwards, and all the fat that is upon the inwards,
9 da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta, waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
and the two kidneys, and the fat that is upon them, which is by the loins, and the lobe above the liver, which he shall take away by the kidneys,
10 Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin yă ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya.
as it is taken off from the ox of the sacrifice of peace-offerings; and the priest shall make them smoke upon the altar of burnt-offering.
11 Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da hanjinsa,
But the skin of the bullock, and all its flesh, with its head, and with its legs, and its inwards, and its dung,
12 wato, dukan sauran bijimi, dole yă ɗauke su zuwa waje da sansani zuwa wani wuri mai tsabta inda ake zub da toka, yă ƙone shi a itacen da yake cin wuta a tarin toka.
even the whole bullock shall he carry forth without the camp unto a clean place, where the ashes are poured out, and burn it on wood with fire; where the ashes are poured out shall it be burnt.
13 “‘In dukan jama’ar Isra’ilawa suka yi zunubi ba da gangan ba, har suka aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake jama’ar ba su san batun ba, duk da haka sun yi laifi.
And if the whole congregation of Israel shall err, the thing being hid from the eyes of the assembly, and do any of the things which the LORD hath commanded not to be done, and are guilty:
14 Sa’ad da suka gane da zunubin da suka aikata, dole taron su kawo ɗan bijimi a matsayin hadaya don zunubi, su kawo shi a gaban Tentin Sujada.
when the sin wherein they have sinned is known, then the assembly shall offer a young bullock for a sin-offering, and bring it before the tent of meeting.
15 Dattawan jama’a za su ɗibiya hannuwansu a kan bijimin a gaban Ubangiji, sai a yanka bijimin a gaban Ubangiji.
And the elders of the congregation shall lay their hands upon the head of the bullock before the LORD; and the bullock shall be killed before the LORD.
16 Sa’an nan shafaffen firist zai ɗibi jinin bijimi zuwa cikin Tentin Sujada.
And the anointed priest shall bring of the blood of the bullock to the tent of meeting.
17 Zai tsoma yatsarsa cikin jini yă kuma yayyafa shi a gaban Ubangiji sau bakwai a gaban labule.
And the priest shall dip his finger in the blood, and sprinkle it seven times before the LORD, in front of the veil.
18 Zai zuba jinin a ƙahonin bagaden da suke gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Zai zuba sauran jinin a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.
And he shall put of the blood upon the horns of the altar which is before the LORD, that is in the tent of meeting, and all the remaining blood shall he pour out at the base of the altar of burnt-offering, which is at the door of the tent of meeting.
19 Zai cire dukan kitsen daga gare shi yă ƙone a kan bagade,
And all the fat thereof shall he take off from it, and make it smoke upon the altar.
20 yă kuma yi da wannan bijimi kamar yadda ya yi da bijimi na hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsu, za a kuwa gafarta musu.
Thus shall he do with the bullock; as he did with the bullock of the sin-offering, so shall he do with this; and the priest shall make atonement for them, and they shall be forgiven.
21 Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a.
And he shall carry forth the bullock without the camp, and burn it as he burned the first bullock; it is the sin-offering for the assembly.
22 “‘Sa’ad da shugaba ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta, to, ya yi laifi.
When a ruler sinneth, and doeth through error any one of all the things which the LORD his God hath commanded not to be done, and is guilty:
23 Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo bunsuru marar lahani a matsayin hadayarsa.
if his sin, wherein he hath sinned, be known to him, he shall bring for his offering a goat, a male without blemish.
24 Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun yă kuma yanka shi a inda ake yankan hadayar ƙonawa a gaban Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi.
And he shall lay his hand upon the head of the goat, and kill it in the place where they kill the burnt-offering before the LORD; it is a sin-offering.
25 Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsarsa yă sa a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.
And the priest shall take of the blood of the sin-offering with his finger, and put it upon the horns of the altar of burnt-offering, and the remaining blood thereof shall he pour out at the base of the altar of burnt-offering.
26 Zai ƙone dukan kitse a kan bagade kamar yadda ya ƙone kitsen hadaya ta salama. Ta haka firist zai yi kafara saboda zunubin mutumin, za a kuwa gafarta masa.
And all the fat thereof shall he make smoke upon the altar, as the fat of the sacrifice of peace-offerings; and the priest shall make atonement for him as concerning his sin, and he shall be forgiven.
27 “‘In wani memba a cikin jama’a ya yi zunubi ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.
And if any one of the common people sin through error, in doing any of the things which the LORD hath commanded not to be done, and be guilty:
28 Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo akuya marar lahani a matsayin hadayarsa domin zunubin da ya yi.
if his sin, which he hath sinned, be known to him, then he shall bring for his offering a goat, a female without blemish, for his sin which he hath sinned.
29 Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa.
And he shall lay his hand upon the head of the sin-offering, and kill the sin-offering in the place of burnt-offering.
30 Sa’an nan firist zai ɗibi jinin da yatsarsa yă zuba a ƙahoni a bagaden hadaya ta ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a ƙasan bagade.
And the priest shall take of the blood thereof with his finger, and put it upon the horns of the altar of burnt-offering, and all the remaining blood thereof shall he pour out at the base of the altar.
31 Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.
And all the fat thereof shall he take away, as the fat is taken away from off the sacrifice of peace-offerings; and the priest shall make it smoke upon the altar for a sweet savour unto the LORD; and the priest shall make atonement for him, and he shall be forgiven.
32 “‘Idan kuwa daga cikin’yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo’yar tunkiya marar lahani.
And if he bring a lamb as his offering for a sin-offering, he shall bring it a female without blemish.
33 Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta hadaya don zunubi a inda ake yankan hadayar ƙonawa.
And he shall lay his hand upon the head of the sin-offering, and kill it for a sin-offering in the place where they kill the burnt-offering.
34 Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubin da yatsarsa yă zuba a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.
And the priest shall take of the blood of the sin-offering with his finger, and put it upon the horns of the altar of burnt-offering, and all the remaining blood thereof shall he pour out at the base of the altar.
35 Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist ɗin zai yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa.
And all the fat thereof shall he take away, as the fat of the lamb is taken away from the sacrifice of peace-offerings; and the priest shall make them smoke on the altar, upon the offerings of the LORD made by fire; and the priest shall make atonement for him as touching his sin that he hath sinned, and he shall be forgiven.

< Firistoci 4 >