< Yohanna 1 >
1 Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.
A cikin farko akwai Kalma, Kalmar kuma tana tare da Allah, wannan Kalma kuwa Allah ne.
2 Yana nan tare da Allah tun farar farawa.
Shi kuwa tare da Allah yake tun farko.
3 Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
Dukan abu ta wurinsa aka yi su, babu abin da aka halitta sai ta wurin sa.
4 A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.
A cikinsa rai ya ke, kuma wannan rai ya zama haske ga dukan mutane.
5 Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.
Hasken ya haskaka a cikin duhu, kuma duhun bai rinjaye shi ba.
6 Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna.
Akwai wani mutum wanda Allah ya aiko, mai suna Yahaya.
7 Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya.
Ya zo a matsayin mai ba da shaida game da hasken, domin kowa ya ba da gaskiya ta wurinsa.
8 Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken.
Ba Yahaya ne hasken ba, amma ya zo ne domin ya shaida hasken.
9 Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya.
Wannan shine haske na gaskiya mai ba da haske ga dukan mutane, da ke zuwa cikin duniya.
10 Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba.
Yana cikin duniya, kuma an halicci duniya ta wurinsa, amma duniya bata san shi ba.
11 Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba.
Ya zo wurin nasa, amma nasa basu karbe shi ba.
12 Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama’ya’yan Allah
Amma duk iyakar wadanda suka karbe shi, suka kuma ba da gaskiya ga sunansa, ya ba su 'yanci su zama 'ya'yan Allah.
13 ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.
Wadanda aka haife su ba ta wurin jini ba, ko ta wurin nufin jiki, ko nufin mutum, amma ta wurin Allah.
14 Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.
Kalmar kuma ya zama jiki ya zauna cikin mu. Mun ga daukakarsa, daukaka irin ta makadaici shi kadai wanda ya zo daga Uban, cike da alheri da gaskiya.
15 (Yohanna ya ba da shaida game da shi. Ya ɗaga murya yana cewa, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya fi ni girma domin yana nan kafin ni.’”)
Yahaya ya yi shaida akansa yana kira da karfi, cewa, “Wannan shine wanda na yi magana a kansa cewa, 'Shi wanda ke zuwa bayana, ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.'”
16 Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka.
Domin daga cikarsa ne muka karbi alheri akan alheri.
17 Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.
Gama shari'a ta zo daga wurin Musa. Alheri da gaskiya sun zo ta wurin Yesu Almasihu.
18 Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi.
Babu lokacin da wani ya taba ganin Allah, shi wanda shi kadai ne Allah, wanda ke jingine da kirjin Uba, shi ya bayyana shi.
19 To, ga shaidar Yohanna sa’ad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne.
Wannan ita ce shaidar Yahaya sa'adda Yahudawa suka aika da Firistoci da Lawiyawa zuwa gareshi don su tambaye shi, “Wanene kai?”
20 Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.”
Ya fada dalla dalla, kuma bai musunta ba, yana amsa masu cewa, “ba nine Almasihu ba.”
21 Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?” Ya ce, “A’a, ni ba shi ba ne.” “Kai ne Annabin nan?” Ya amsa ya ce, “A’a.”
Sai suka tambaye shi, “To kai wanene? Kai Iliya ne?” Yace, “Ba ni ba ne.” Suka ce, “Kai ne anabin?” Ya amsa, “A'a”.
22 A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?”
Sai suka ce masa, “Kai wanene, domin mu bada amsa ga wadanda suka aiko mu? Me kake fadi game da kanka?”
23 Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’”
Yace, “Ni murya ne, da ke kira cikin jeji, 'Ku daidaita hanyar Ubangiji,' kamar yadda annabi Ishaya ya fada.”
24 To, waɗansu Farisiyawan da aka aika
Su wadanda aka aika daga wurin Farisawa suke. Sai suka tambaye shi cewa,
25 suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”
“To don me kake baftisma idan kai ba Almasihu bane, ko Iliya, ko annabin?”.
26 Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba.
Yahaya ya amsa masu, cewa, “Ina baftisma ne da ruwa. Amma a cikinku akwai wani tsaye wanda ba ku sani ba,
27 Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”
shi wanda ke zuwa bayana, wanda ko igiyar takalminsa ban isa in kwance ba.”
28 Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma.
Wadannan abubuwa sun faru ne a Baitanya, a dayan ketaren Urdun, a wurin da Yahaya ke Baftisma.
29 Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!
Washegari, Yahaya ya ga Yesu yana zuwa wurinsa ya ce, “Duba, ga Dan Ragon Allah wanda ke dauke zunubin duniya!
30 Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’
Wannan shine wanda na fada maku cewa, “Shi wanda ke zuwa bayana ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.'
31 Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.”
Ban san shi ba, amma saboda a bayyana shi ga Isra'ila ne nazo ina baftisma da ruwa. “
32 Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa.
Yahaya ya shaida, cewa, “Na ga Ruhu yana saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa.
33 Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’
Ban gane shi ba, amma shi wanda ya aiko ni in yi baftisma cikin ruwa ya fada mani cewa, 'duk wanda ka ga Ruhun ya sauka kuma ya zauna a kansa, shine wanda ke yin baftisma cikin Ruhu mai tsarki.'
34 Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”
Na gani, na kuma shaida cewa wannan shine Dan Allah.”
35 Kashegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa.
Kuma, washegari, da Yahaya na tsaye da biyu daga cikin almajiransa,
36 Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”
suka ga Yesu na wucewa, sai Yahaya ya ce, “Duba, ga Dan rago na Allah!”
37 Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.
Sai almajiransa biyu suka ji ya fadi haka, suka kuwa bi Yesu.
38 Da juyewa, sai Yesu ya ga suna bin sa, sai ya tambaye, su ya ce, “Me kuke nema?” Suka ce, “Rabbi” (wato, “Malam”), “ina kake da zama?”
Da Yesu ya waiwaya ya gan su suna bin sa, sai ya ce masu, “Me kuke so?” Suka amsa, “Rabbi (wato 'Mallam'), ina kake da zama?”
39 Ya amsa musu ya ce, “Ku zo, za ku kuma gani.” Saboda haka suka je suka ga inda yake da zama, suka kuma zauna a can tare da shi. Wajen sa’a ta goma ce kuwa.
Yace masu, “Zo ku gani.” Sai suka zo suka ga inda yake zama; suka zauna da shi ranan nan, gama wajen sa'a ta goma ne.
40 Andarawus ɗan’uwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun nan da suka bi Yesu bayan da suka ji maganar Yohanna a kan Yesu.
Daya daga cikin wadanda suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu shine Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus.
41 Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗan’uwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi).
Ya fara neman dan'uwansa Siman yace masa, “Mun sami Almasihu” (wanda ake kira 'Kristi').
42 Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan).
Ya kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi yace, “Kai ne Siman dan Yahaya. Za a kira ka Kefas,” (ma'ana, 'Bitrus').
43 Kashegari Yesu ya yanke shawara yă tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, “Bi ni.”
Washegari, da Yesu yana shirin tafiya zuwa Galili, sai ya sami Filibus, ya ce masa, “ka biyo ni.”
44 Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne.
Filibus dan asalin Baitsaida ne, garin Andarawus da Bitrus.
45 Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa, Yesu Banazare, ɗan Yusuf.”
Filibus ya sami Natana'ilu yace masa, “Mun same shi, shi wanda Musa ya rubuta shi a cikin attaura, da annabawa: Yesu Dan Yusufu, Ba-Nazarat.”
46 Natanayel ya ce, “A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?” Filibus ya ce, “Zo ka gani.”
Natana'ilu ya ce masa, “za a iya samun wani abu nagari a Nazarat?” Filibus yace masa, “Zo ka gani.”
47 Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, “Ga mutumin Isra’ila na gaske wanda ba shi da ha’inci.”
Yesu ya ga Natana'ilu yana zuwa wurinsa sai yayi magana game da shi, “Duba, Ba-Isra'ile na hakika wanda babu yaudara a cikinsa.”
48 Natanayel ya yi tambaya ya ce, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yă kira ka.”
Natana'ilu yace masa, “Ta yaya ka san ni?” Sai Yesu ya amsa masa yace, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'adda kake a gindin baure, na gan ka.”
49 Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Isra’ila.”
Natana'ilu ya amsa, “Rabbi, Kai Dan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!”
50 Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.”
Yesu ya amsa masa yace, “Don na ce maka, 'Na gan ka a gindin Baure', ka gaskanta? Za ka ga abubuwa da suka fi wannan girma.”
51 Sai ya ƙara da cewa, “Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, mala’ikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.”
Sai yace, 'Hakika, hakika ina gaya maka, zaka ga sammai a bude, mala'ikun Allah kuma suna hawa suna sauka akan Dan Mutum.”