< Yohanna 2 >

1 A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can,
Bayan kwana uku, akwai aure a Kana ta Galili, mahaifiyar Yesu kuma tana wurin.
2 aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren.
An gayyaci Yesu da almajiransa zuwa auren.
3 Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”
Da ruwan inabin ya kare, maihafiyar Yasu tace masa, “basu da ruwan inabi.”
4 Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.”
Yesu yace mata, “Mace, me yasa kika zo wurina? Lokaci na bai yi ba tukuna”.
5 Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.”
Maihafiyarsa tace wa ma'aikatan, “Ku yi duk abin da yace maku.”
6 Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.
To akwai randunan ruwa na dutse guda shidda a wurin wadanda Yahudawa ke amfani da su domin al'adansu na tsarkakewa, kowace zata iya daukar durom guda.
7 Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.
Yesu yace masu, “Cika randunan da ruwa”. Sai suka cika randunan makil.
8 Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.” Suka yi haka.
Sai yace wa ma'aikatan, “Ku diba daga ciki ku kai wa shugaban biki.” Sai suka yi hakannan.
9 Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya
Shugaban bikin ya dandana ruwan da ya zama ruwan inabin, amma bai san inda ya fito ba (amma ma'aikatan wadanda suka jawo ruwan sun sani). Sai ya kira ango
10 ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”
yace masa, “Kowane mutum yakan raba ruwan inabi mai kyau da farko, kafin mai arhar bayan an shanye mai kyaun. Amma kai ka ajiye mai kyaun sai yanzu.”
11 Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.
Wannan alama ta farko ce da Yesu yayi a Kana ta Galili, ya kuma bayyana daukakarsa, almajiransa kuma suka gaskata da shi.
12 Bayan wannan sai ya tafi Kafarnahum tare da mahaifiyarsa da’yan’uwansa da kuma almajiransa. A can suka zauna’yan kwanaki.
Bayan wannan, Yesu, da mahaifiyarsa, da 'yan'uwansa da almajiransa suka tafi Kafarnahum, kuma suka zauna can wasu 'yan kwanaki.
13 Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima.
To idin ketarewa na Yahudawa ya kusato, Yesu kuwa ya wuce zuwa Urushalima.
14 A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi.
Ya iske wadanda suke sayar da shanu da tumaki da tantabaru, masu canjin kudi kuma na zaune a wurin.
15 Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu.
Sai yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Sai ya watsar da sulallan masu canjin kudin ya birkitar da teburansu.
16 Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!”
Yace wa masu sayar da tantabaru, “Ku fitar da wadannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci.”
17 Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.”
Almajiransa suka tuna a rubuce yake, “Himma domin gidanka za ta cinye ni.”
18 Sai Yahudawa suka tambaye shi, “Wace abar banmamaki za ka nuna mana ka tabbatar mana ikonka na yin duk waɗannan?”
Sai shugabannin Yahudawa suka amsa suka ce masa, “Wace alama za ka nuna mana, da shike kana yin wadannan abubuwan?”
19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.”
Yesu ya amsa, “Ku rushe wannan haikali, kuma a cikin kwana uku zan gina shi.”
20 Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?”
Sai shugabanin Yahudawa suka ce, “An dauki shekaru arba'in da shidda kamin a gama gina wannan haikalin, za ka dau kwanaki uku kadai wajen gina shi?”
21 Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne.
Amma yana nufin haikali na jikinsa ne.
22 Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi.
Bayan da aka tashe shi daga matattu, sai almajiransa suka tuna ya fadi haka, suka kuma ba da gaskiya ga nassi da wannan kalami da Yesu ya fada.
23 To, yayinda yake a Urushalima a Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa suka ga abubuwan banmamakin da yake aikata suka kuma gaskata da sunansa.
Kuma, da yana Urushalima a idin ketarewa, a lokacin idin, mutane da yawa suka gaskata ga sunansa, sa'adda suka ga alamun da ya yi.
24 Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane.
Amma Yesu bai yadda da su ba domin ya san su duka,
25 Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum.
saboda baya bukatar wani ya shaida masa game da mutum, domin ya san abinda ke cikin sa.

< Yohanna 2 >