< Ayuba 35 >
1 Sai Elihu ya ce,
2 “Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’
3 Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita, kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’
4 “Zan so in ba ka amsa kai tare da abokanka.
5 Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani; ku dubi gizagizai a samanku.
6 In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah? In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa?
7 In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku?
8 Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai, adalcinku kuma yakan shafi’yan adam ne kaɗai.
9 “Mutane suna kuka don yawan zalunci; suna roƙo don taimako daga hannu mai ƙarfi.
10 Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni, mai ba da waƙoƙi cikin dare,
11 wanda ya fi koya mana fiye da dabbobin duniya ya kuma sa muka fi tsuntsayen cikin iska hikima.’
12 Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako domin girman kan mugaye.
13 Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.
14 Ta yaya zai saurara sosai ko zai saurara lokacin da kake cewa ba ka ganinsa, cewa ka kawo ƙara a wurinsa kuma dole ka jira shi.
15 Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsa ko kaɗan ba ya kula da mugunta.
16 Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai; yana ta yawan magana ba tare da sani ba.”