< Ishaya 59 >

1 Tabbatacce hannun Ubangiji bai kāsa yin ceto ba, kunnensa kuma bai kurmance da zai kāsa ji ba.
הן לא קצרה יד יהוה מהושיע ולא כבדה אזנו משמוע
2 Amma laifofinku sun raba ku da Allahnku; zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku, saboda kada yă ji.
כי אם עונתיכם היו מבדלים בינכם לבין אלהיכם וחטאותיכם הסתירו פנים מכם--משמוע
3 Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma da alhaki. Leɓunanku suna faɗin ƙarairayi, harshenku kuma yana raɗar mugayen abubuwa.
כי כפיכם נגאלו בדם ואצבעותיכם בעון שפתותיכם דברו שקר--לשונכם עולה תהגה
4 Babu wani mai ce a yi adalci; babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci. Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi; suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta.
אין קרא בצדק ואין נשפט באמונה בטוח על תהו ודבר שוא הרו עמל והוליד און
5 Suna ƙyanƙyashe ƙwan kāsā su kuma saƙa yanar gizo-gizo. Duk wanda ya ci ƙwansu zai mutu, kuma sa’ad da ƙwan ya fashe, zai ƙyanƙyashe kububuwa.
ביצי צפעוני בקעו וקורי עכביש יארגו האכל מביציהם ימות והזורה תבקע אפעה
6 Yanar gizo-gizonsu ba amfani don tufa; ba za su iya rufuwa da abin da suka yi ba. Ayyukansu mugaye ne, ayyukan tā da hargitsi kuma suna a hannuwansu.
קוריהם לא יהיו לבגד ולא יתכסו במעשיהם מעשיהם מעשי און ופעל חמס בכפיהם
7 Ƙafafunsu sukan gaggauta zuwa aikata zunubi; suna da saurin zub da jini. Tunaninsu mugaye ne; lalaci da hallaka sun shata hanyoyinsu.
רגליהם לרע ירצו וימהרו לשפך דם נקי מחשבותיהם מחשבות און--שד ושבר במסלותם
8 Ba su san hanyar salama ba; babu adalci a hanyoyinsu. Sun mai da su karkatattun hanyoyi; babu wanda zai yi tafiya a kansu ya sami salama.
דרך שלום לא ידעו ואין משפט במעגלותם נתיבותיהם עקשו להם--כל דרך בה לא ידע שלום
9 Saboda haka gaskiya ta yi nisa da mu, adalci kuma ba ya kaiwa gare mu. Muna neman haske, sai ga duhu; muna neman haske, sai muka yi ta tafiya cikin baƙin inuwa.
על כן רחק משפט ממנו ולא תשיגנו צדקה נקוה לאור והנה חשך לנגהות באפלות נהלך
10 Kamar makafi, sai lallubar bango muke yi, muna lallubawar hanyarmu kamar marasa idanu. Da tsakar rana muna tuntuɓe sai ka ce wuri ya fara duhu; cikin ƙarfafa, mun zama kamar matattu.
נגששה כעורים קיר וכאין עינים נגששה כשלנו בצהרים כנשף באשמנים כמתים
11 Muna gurnani kamar beyar; muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci amma ina; mun nemi fansa, amma yana can da nisa.
נהמה כדבים כלנו וכיונים הגה נהגה נקוה למשפט ואין לישועה רחקה ממנו
12 Gama laifofinmu suna da yawa a gabanka, zunubanmu kuma suna ba da shaida gāba da mu. Laifofinmu kullum suna a gabanmu, muna kuma sane da laifofinmu,
כי רבו פשעינו נגדך וחטאותינו ענתה בנו כי פשעינו אתנו ועונתינו ידענום
13 tawaye da mūsun Ubangiji, mun juye bayanmu ga Allahnmu, zugawa a yi zalunci da tayarwa, faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya.
פשע וכחש ביהוה ונסוג מאחר אלהינו דבר עשק וסרה הרו והגו מלב דברי שקר
14 Saboda haka aka kau da yin gaskiya adalci kuma ya tsaya can da nesa; gaskiya ta yi tuntuɓe a tituna, sahihanci ba zai shiga ba.
והסג אחור משפט וצדקה מרחוק תעמד כי כשלה ברחוב אמת ונכחה לא תוכל לבוא
15 Gaskiya ta ɓace gaba ɗaya, kuma duk wanda ya guji mugunta zai zama ganima. Ubangiji ya duba bai kuwa ji daɗi cewa babu adalci ba.
ותהי האמת נעדרת וסר מרע משתולל וירא יהוה וירע בעיניו כי אין משפט
16 Ya ga cewa babu wani, ya yi mamaki cewa babu wanda zai shiga tsakani; saboda haka hannunsa ya aikata masa ceto, adalcinsa kuma ya raya shi.
וירא כי אין איש וישתומם כי אין מפגיע ותושע לו זרעו וצדקתו היא סמכתהו
17 Ya yafa sulke a matsayin rigar ƙirji, da hulan kwanon ceto a kansa; ya sa rigunan ɗaukar fansa ya kuma nannaɗe kansa da kishi kamar a cikin alkyabba.
וילבש צדקה כשרין וכובע ישועה בראשו וילבש בגדי נקם תלבשת ויעט כמעיל קנאה
18 Bisa ga abin da suka yi, haka za a sāka fushi a kan abokan gābansa ramuwa kuma a kan maƙiyansa; zai sāka wa tsibirai abin da ya dace da su.
כעל גמלות כעל ישלם--חמה לצריו גמול לאיביו לאיים גמול ישלם
19 Daga yamma, mutane za su ji tsoron Ubangiji, daga mafitar rana kuma, za su girmama ɗaukakarsa. Gama zai zo kamar rigyawa mai tsananin gudu cewa numfashin Ubangiji zai tafi tare da shi.
ויראו ממערב את שם יהוה וממזרח שמש את כבודו כי יבוא כנהר צר רוח יהוה נססה בו
20 “Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji.
ובא לציון גואל ולשבי פשע ביעקב--נאם יהוה
21 “Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji.
ואני זאת בריתי אותם אמר יהוה--רוחי אשר עליך ודברי אשר שמתי בפיך לא ימושו מפיך ומפי זרעך ומפי זרע זרעך אמר יהוה מעתה ועד עולם

< Ishaya 59 >