< Ishaya 58 >

1 “Ku yi ihu da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa. Ku tā da muryarku kamar busar ƙaho. Ku furta wa mutanena tawayensu da kuma ga gidan Yaƙub zunubansu.
קרא בגרון אל תחשך כשופר הרם קולך והגד לעמי פשעם ולבית יעקב חטאתם
2 Gama kowace rana suna nemana; suna marmarin sanin hanyoyina, sai ka ce al’ummar da take yin abin da yake daidai ba ta kuma yashe umarnan Allahnta ba. Sun nemi shawarwaran da suke daidai daga gare ni suna kuma marmari Allah ya zo kusa da su.
ואותי יום יום ידרשון ודעת דרכי יחפצון כגוי אשר צדקה עשה ומשפט אלהיו לא עזב ישאלוני משפטי צדק קרבת אלהים יחפצון
3 Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi, ba ka kuma gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, ba ka kuma lura da wannan ba?’ “Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata.
למה צמנו ולא ראית ענינו נפשנו ולא תדע הן ביום צמכם תמצאו חפץ וכל עצביכם תנגשו
4 Azuminku yakan ƙare a faɗa da kuma hargitsi, kuna ta naushin juna da mugayen naushe-naushe. Ba za ku iya azumi kamar yadda kuke yi a yau ku zaci za a ji muryarku can sama.
הן לריב ומצה תצומו ולהכות באגרף רשע לא תצומו כיום להשמיע במרום קולכם
5 Irin azumin da na zaɓa ke nan, rana guda kawai don mutum ya ƙasƙantar da kansa? Sunkuyar da kanku kamar iwa kawai kuna kuma kwance a tsummoki da toka? Abin da kuke kira azumi ke nan rana yardajje ga Ubangiji?
הכזה יהיה צום אבחרהו--יום ענות אדם נפשו הלכף כאגמן ראשו ושק ואפר יציע--הלזה תקרא צום ויום רצון ליהוה
6 “Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya?
הלוא זה צום אבחרהו--פתח חרצבות רשע התר אגדות מוטה ושלח רצוצים חפשים וכל מוטה תנתקו
7 Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?
הלוא פרס לרעב לחמך ועניים מרודים תביא בית כי תראה ערם וכסיתו ומבשרך לא תתעלם
8 Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan; sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku, ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya.
אז יבקע כשחר אורך וארכתך מהרה תצמח והלך לפניך צדקך כבוד יהוה יאספך
9 Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,
אז תקרא ויהוה יענה תשוע ויאמר הנני אם תסיר מתוכך מוטה שלח אצבע ודבר און
10 in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana.
ותפק לרעב נפשך ונפש נענה תשביע וזרח בחשך אורך ואפלתך כצהרים
11 Ubangiji zai bishe ku kullum; zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa, kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa.
ונחך יהוה תמיד והשביע בצחצחות נפשך ועצמתיך יחליץ והיית כגן רוה וכמוצא מים אשר לא יכזבו מימיו
12 Mutanenku za su sāke gina kufai na da su kuma daga tsofaffin harsashai; za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe, Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama.
ובנו ממך חרבות עולם מוסדי דור ודור תקומם וקרא לך גדר פרץ משבב נתיבות לשבת
13 “In kun kiyaye ƙafafunku daga take Asabbaci da kuma daga aikata abin da kuka gan dama a ranata mai tsarki, in kuka kira Asabbaci ranar murna rana mai tsarki ta Ubangiji kuma mai bangirma, in kuka girmama ta ta wurin ƙin yin abin da kuka gan dama da kuma yin al’amuranku ko yin mugayen maganganu,
אם תשיב משבת רגלך עשות חפצך ביום קדשי וקראת לשבת ענג לקדוש יהוה מכבד וכבדתו מעשות דרכיך ממצוא חפצך ודבר דבר
14 sa’an nan za ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, zan kuma sa ku a kan maɗaukaka ƙasashe ku kuma yi biki a gādon mahaifinku Yaƙub.” Ni Ubangiji ne na faɗa.
אז תתענג על יהוה והרכבתיך על במותי (במתי) ארץ והאכלתיך נחלת יעקב אביך--כי פי יהוה דבר

< Ishaya 58 >