< Ibraniyawa 2 >
1 Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce.
Therefore we must pay greater attention to what we have heard, so that we do not drift away.
2 Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace,
For if the message spoken through angels was valid and every transgression and disobedience received a just retribution,
3 yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi.
how will we escape if we neglect so great a salvation? This salvation was first announced by the Lord, and it was confirmed to us by those who heard him.
4 Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.
God also bore further witness with signs, wonders, various miracles, and gifts of the Holy Spirit distributed according to his will.
5 Ba ga mala’iku ba ne ya sa su yi mulkin duniya mai zuwa, wanda muke magana a kai ba.
For it was not to angels that God subjected the world to come, about which we are speaking.
6 Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa, “Mene ne mutum, da kake tuna da shi, ɗan mutum da kake kula da shi?
But in one place someone has testified: “What is man that yoʋ are mindful of him, or the son of man that yoʋ care for him?
7 Ka sa shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku; ka naɗa shi da ɗaukaka da girma,
Yoʋ made him a little lower than the angels and crowned him with glory and honor;
8 ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba.
yoʋ put everything in subjection under his feet.” In subjecting everything to him, God left nothing that is not subjected to him. But now we do not yet see everything subjected to him.
9 Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa.
But we do see Jesus, who for a little while was made lower than the angels, now crowned with glory and honor because he suffered death, so that by the grace of God he might taste death for everyone.
10 Ta wurin kawo’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.
For in bringing many sons to glory, it was fitting that God, for whom and through whom all things exist, should make the author of their salvation perfect through suffering.
11 Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu’yan’uwansa.
For he who sanctifies and those who are being sanctified all have one Father. That is why Jesus is not ashamed to call them brothers,
12 Ya ce, “Zan sanar da sunanka ga’yan’uwana; a gaban jama’a zan rera yabonka.”
saying, “I will declare yoʋr name to my brothers; in the midst of the congregation I will sing yoʋr praise.”
13 Har wa yau ya ce, “Zan dogara gare shi.” Ya kuma ce, “Ga ni, da’ya’yan da Allah ya ba ni.”
And again, “I will put my trust in him.” And again, “Here I am, with the children God has given me.”
14 Da yake’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis
Therefore, since the children all have flesh and blood, Jesus himself took on flesh and blood as well, so that through death he might destroy the one who has the power of death, that is, the devil,
15 ya kuma’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.
and free those who all their lives were held in slavery by the fear of death.
16 Gama tabbatacce ba mala’iku ne ya taimaka ba, sai dai zuriyar Ibrahim.
For surely it is not angels that he helps, but the descendants of Abraham.
17 Saboda wannan dole a mai da shi kamar’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane.
Therefore he had to become like his brothers in every way, so that he could be a merciful and faithful high priest in service to God, in order to make atonement for the sins of the people.
18 Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.
Because he himself suffered when he was tempted, he is able to help those who are being tempted.