< Ezra 2 >
1 Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu.
2 Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana). Ga jerin mazan mutanen Isra’ila.
3 Zuriyar Farosh mutum 2,172
4 ta Shefatiya 372
5 ta Ara 775
6 ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,812
7 ta Elam 1,254
8 ta Zattu 945
9 ta Zakkai 760
10 ta Bani 642
11 ta Bebai 623
12 ta Azgad 1,222
13 ta Adonikam 666
14 ta Bigwai 2,056
15 ta Adin 454
16 ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98
17 ta Bezai 323
18 ta Yora 112
19 ta Hashum 223
20 ta Gibbar 95.
21 Mutanen Betlehem 123
22 na Netofa 56
23 na Anatot 128
24 na Azmawet 42
25 na Kiriyat Yeyarim, da Kefira Beyerot 743
26 na Rama da Geba 621
27 na Mikmash 122
28 na Betel da Ai 223
29 na Nebo 52
30 na Magbish 156
31 na ɗayan Elam ɗin 1,254
32 na Harim 320
33 na Lod, da Hadid da Ono 725
34 na Yeriko 345
35 na Sena’a 3,630.
36 Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973
37 ta Immer 1,052
38 ta Fashhur 1,247
39 ta Harim 1,017.
40 Lawiyawa. Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodawiya) mutum 74.
41 Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 128.
42 Masu tsaron haikali. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai mutum 139.
43 Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot,
44 Keros, Siyaha, Fadon,
45 Lebana, Hagaba, Akkub,
46 Hagab, Shamlai, Hanan,
47 Giddel, Gahar, Reyahiya,
48 Rezin, Nekoda, Gazzam,
49 Uzza, Faseya, Besai,
50 Asna, Meyunawa, Nefussiyawa,
51 Bakbuk, Hakufa, Harhur,
52 Bazlut, Mehida, Harsha,
53 Barkos, Sisera, Tema,
54 Neziya da Hatifa.
55 Zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda,
56 Ya’ala, Darkon, Giddel,
57 Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Ami.
58 Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392.
59 Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba.
60 ’Yan zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 652.
61 Daga cikin firistoci kuma, zuriyar Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna).
62 Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne.
63 Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna.
64 Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,
65 ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200.
66 Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245,
67 raƙuma 435, da jakuna 6,720.
68 Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake.
69 Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100.
70 Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu.