Preface
Read
+
Publisher
Nainoia, Inc.
PO Box 462, Bellefonte, PA 16823
(814) 470-8028
Nainoia Inc, Publisher
LinkedIn/NAINOIA-INC
Third Party Publisher Resources
Request Custom Formatted Verses
Please contact us below
Submit your proposed corrections
I understand that the Aionian Bible republishes public domain and Creative Commons Bible texts and that volunteers may be needed to present the original text accurately. I also understand that apocryphal text is removed and most variant verse numbering is mapped to the English standard. I have entered my corrections under the verse(s) below. Proposed corrections to the Hausa Contemporary Bible, Ezra Chapter 2 https://www.AionianBible.org/Bibles/Hausa---Contemporary/Ezra/2 1) Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu. 2) Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana). Ga jerin mazan mutanen Isra’ila. 3) Zuriyar Farosh mutum 2,172 4) ta Shefatiya 372 5) ta Ara 775 6) ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,812 7) ta Elam 1,254 8) ta Zattu 945 9) ta Zakkai 760 10) ta Bani 642 11) ta Bebai 623 12) ta Azgad 1,222 13) ta Adonikam 666 14) ta Bigwai 2,056 15) ta Adin 454 16) ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98 17) ta Bezai 323 18) ta Yora 112 19) ta Hashum 223 20) ta Gibbar 95. 21) Mutanen Betlehem 123 22) na Netofa 56 23) na Anatot 128 24) na Azmawet 42 25) na Kiriyat Yeyarim, da Kefira Beyerot 743 26) na Rama da Geba 621 27) na Mikmash 122 28) na Betel da Ai 223 29) na Nebo 52 30) na Magbish 156 31) na ɗayan Elam ɗin 1,254 32) na Harim 320 33) na Lod, da Hadid da Ono 725 34) na Yeriko 345 35) na Sena’a 3,630. 36) Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973 37) ta Immer 1,052 38) ta Fashhur 1,247 39) ta Harim 1,017. 40) Lawiyawa. Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodawiya) mutum 74. 41) Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 128. 42) Masu tsaron haikali. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai mutum 139. 43) Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot, 44) Keros, Siyaha, Fadon, 45) Lebana, Hagaba, Akkub, 46) Hagab, Shamlai, Hanan, 47) Giddel, Gahar, Reyahiya, 48) Rezin, Nekoda, Gazzam, 49) Uzza, Faseya, Besai, 50) Asna, Meyunawa, Nefussiyawa, 51) Bakbuk, Hakufa, Harhur, 52) Bazlut, Mehida, Harsha, 53) Barkos, Sisera, Tema, 54) Neziya da Hatifa. 55) Zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda, 56) Ya’ala, Darkon, Giddel, 57) Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Ami. 58) Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392. 59) Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba. 60) ’Yan zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 652. 61) Daga cikin firistoci kuma, zuriyar Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna). 62) Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne. 63) Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna. 64) Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360, 65) ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200. 66) Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245, 67) raƙuma 435, da jakuna 6,720. 68) Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake. 69) Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100. 70) Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu. Additional comments?
Refresh Captcha
The world's first Holy Bible un-translation!