< Ezekiyel 13 >

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
ויהי דבר יהוה אלי לאמר
2 “Ɗan mutum, yi annabci a kan annabawan Isra’ila waɗanda suke annabci yanzu. Ka faɗa wa waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji!
בן אדם הנבא אל נביאי ישראל הנבאים ואמרת לנביאי מלבם שמעו דבר יהוה
3 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake faɗa, Kaiton wawaye annabawan da suke bin ruhunsu kuma ba su ga kome ba!
כה אמר אדני יהוה הוי על הנביאים הנבלים אשר הלכים אחר רוחם ולבלתי ראו
4 Annabawanki, ya Isra’ila, suna kama da diloli a kufai.
כשעלים בחרבות--נביאיך ישראל היו
5 Ba ku haura don ku rushe katanga don ku gyara gidan Isra’ila saboda ya tsaya daram a yaƙi a ranar Ubangiji ba.
לא עליתם בפרצות ותגדרו גדר על בית ישראל לעמד במלחמה ביום יהוה
6 Wahayoyinsu ƙarya ne suna yin dubansu na ƙarya ne. Sukan ce, Ubangiji ya furta, alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba; duk da haka sukan sa zuciya ga cikawar maganarsu.
חזו שוא וקסם כזב--האמרים נאם יהוה ויהוה לא שלחם ויחלו לקים דבר
7 Ba ku ga wahayin ƙarya kuka kuma faɗa yin duban ƙarya sa’ad da kuka ce, “Ubangiji ya furta,” ko da yake bai yi magana ba?
הלוא מחזה שוא חזיתם ומקסם כזב אמרתם ואמרים נאם יהוה ואני לא דברתי
8 “‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa saboda maganganunku na ƙarya da wahayinku na ƙarya, ina gāba da ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
לכן כה אמר אדני יהוה יען דברכם שוא וחזיתם כזב--לכן הנני אליכם נאם אדני יהוה
9 Hannuna zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya suna kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin gidan Isra’ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
והיתה ידי אל הנביאים החזים שוא והקסמים כזב בסוד עמי לא יהיו ובכתב בית ישראל לא יכתבו ואל אדמת ישראל לא יבאו וידעתם כי אני אדני יהוה
10 “‘Domin sun ɓad da mutanena, suna cewa, “Salama,” sa’ad da ba salama, kuma saboda, sa’ad da ana gina katanga marar ƙarfi, sukan shafe ta da farar ƙasa,
יען וביען הטעו את עמי לאמר שלום--ואין שלום והוא בנה חיץ והנם טחים אתו תפל
11 saboda haka ka faɗa wa waɗanda suka shafe da farar ƙasa cewa za tă fāɗi. Ruwan sama zai sauko da rigyawa, zan kuma aika da ƙanƙara, kuma babbar iska za tă ɓarke.
אמר אל טחי תפל ויפל היה גשם שוטף ואתנה אבני אלגביש תפלנה ורוח סערות תבקע
12 Sa’ad da katangar ta fāɗi, mutane ba za su tambaye ku ba cewa, “Ina shafen farar ƙasar da kuka yi mata?”
והנה נפל הקיר הלוא יאמר אליכם איה הטיח אשר טחתם
13 “‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a cikin hasalata zan saki babbar iska, kuma cikin fushina zan tura ƙanƙara kuma rigyawan ruwan sama zai sauko da fushin hallaka.
לכן כה אמר אדני יהוה ובקעתי רוח סערות בחמתי וגשם שטף באפי יהיה ואבני אלגביש בחמה לכלה
14 Zan rushe katangar da kuka shafe da farar ƙasa zan baje ta har ƙasa saboda tushenta zai tsaya tsirara. Sa’ad da ta fāɗi, za a hallaka ku a cikinta; kuma za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
והרסתי את הקיר אשר טחתם תפל והגעתיהו אל הארץ--ונגלה יסדו ונפלה וכליתם בתוכה וידעתם כי אני יהוה
15 Ta haka zan aukar wa katangar da hasalata da kuma a kan waɗanda suka yi shafenta da farar ƙasa. Zan ce muku, “Katangar ta fāɗi haka kuma mutanen da suka shafe ta da farar ƙasa,
וכליתי את חמתי בקיר ובטחים אתו תפל ואמר לכם אין הקיר ואין הטחים אתו
16 waɗannan annabawan Isra’ila waɗanda suka yi annabci wa Urushalima suka kuma ga mata wahayin salama sa’ad da ba salama, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”’
נביאי ישראל הנבאים אל ירושלם והחזים לה חזון שלם ואין שלם נאם אדני יהוה
17 “To, ɗan mutum, ka kafa idonka a kan’yan matan mutanenka waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu. Yi annabci a kansu
ואתה בן אדם שים פניך אל בנות עמך המתנבאות מלבהן והנבא עליהן
18 ka kuma ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton matan da suke ɗinka kambuna a hannuwansu suna kuma yin gyale masu tsawo dabam-dabam wa kawunansu don su farauci mutane. Za ku farauci rayukan mutanena ku bar naku?
ואמרת כה אמר אדני יהוה הוי למתפרות כסתות על כל אצילי ידי ועשות המספחות על ראש כל קומה--לצודד נפשות הנפשות תצודדנה לעמי ונפשות לכנה תחיינה
19 Kun jawo mini kunya a cikin mutanena don a tafa muku sha’ir da ɗan dunƙulen burodi. Ta wurin yin ƙarya wa mutanena, waɗanda suke jin ƙarairayi, kuka kashe waɗanda bai kamata su mutu ba kuka bar waɗanda ya kamata su mutu.
ותחללנה אתי אל עמי בשעלי שערים ובפתותי לחם להמית נפשות אשר לא תמותנה ולחיות נפשות אשר לא תחיינה בכזבכם--לעמי שמעי כזב
20 “‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kambunanku waɗanda kuke farautar mutane da su kamar tsuntsaye don haka zan kuma tsintsinke su daga hannuwanku; zan’yantar da mutanen da kuka farauto kamar tsuntsaye.
לכן כה אמר אדני יהוה הנני אל כסתותיכנה אשר אתנה מצדדות שם את הנפשות לפרחות וקרעתי אתם מעל זרועתיכם ושלחתי את הנפשות אשר אתם מצדדות את נפשים לפרחת
21 Zan kyakketa gyalenku in ceci mutanena daga hannuwanku, ba za su kuma ƙara zama ganima a hannunku ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji
וקרעתי את מספחתיכם והצלתי את עמי מידכן ולא יהיו עוד בידכן למצודה וידעתן כי אני יהוה
22 Domin kun karya zuciyar masu adalci da ƙarairayinku, sa’ad da na fitar da su babu damuwa, kuma domin kun ƙarfafa mugaye kada su juye daga mugayen hanyoyinsu su ceci rayukansu,
יען הכאות לב צדיק שקר ואני לא הכאבתיו ולחזק ידי רשע לבלתי שוב מדרכו הרע להחיתו
23 saboda haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi duba. Zan ceci mutanena daga hannuwanku. A sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’”
לכן שוא לא תחזינה וקסם לא תקסמנה עוד והצלתי את עמי מידכן וידעתן כי אני יהוה

< Ezekiyel 13 >