< Esta 7 >

1 Saboda haka sarki da Haman suka tafi cin abinci wurin sarauniya Esta.
The king and Haman went to Queen Esther's dinner.
2 Yayinda suke shan ruwan inabi a rana ta biyun nan, sai sarki ya sāke tambaya, “Sarauniya Esta, me kike so? Za a ba ki. Mene ne roƙonki? Ko da rabin masarautata ne, za a ba ki.”
At this second dinner, as they were drinking wine, the king asked Esther again, “What are you really asking for, Queen Esther? It will be given to you. What do you want? You shall have it, as much as half my empire!”
3 Sai Sarauniya Esta ta amsa ta ce, “In na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, in kuma mai girma ya yarda, a bar ni da raina, wannan shi ne roƙona. Ka kuma sa kada a kashe mutanena, wannan ita ce bukata.
Queen Esther answered, “If the king looks on me favorably, and if it please Your Majesty to grant me my life, that is my request; and the lives of my people, that is what I ask.
4 Gama an sayar da ni da mutanena don a hallaka, a karkashe mu, a kuma ƙi mu. Da a ce an sayar da mu kamar bayi maza da mata ne, da na yi shiru, domin wannan zai zama abin da bai taka kara ya karye ba, har da za a dami sarki a kai.”
For my people and I have been sold to be destroyed, killed, and annihilated. If we had only been sold as slaves, I would have kept quiet, because our suffering would not have justified disturbing the king.”
5 Sarki Zerzes ya tambayi Sarauniya Esta ya ce, “Wane ne shi? Ina mutumin da ya yi ƙarfin halin yin wannan karambani?”
The king asked Queen Esther, demanding to know, “Who is this? Where is the man who has dared to do this?”
6 Esta ta ce, “Maƙiyi da abokin gāban, shi ne wannan mugun Haman.” Sai Haman ya tsorota a gaban sarki da sarauniya.
“The man, the opponent, the enemy, is this evil Haman!” Esther replied. Haman shook with terror in front of the king and the queen.
7 Sarki ya tashi cikin fushi, ya bar ruwan inabinsa, ya fita zuwa cikin lambun fada. Amma da Haman ya gane cewa sarki ya riga ya yanke shawara a kan ƙaddararsa, ya dakata domin yă roƙi sarauniya Esta saboda ransa.
The king was furious. He got up, leaving his wine, and went out into the palace garden. Haman stayed behind to beg for his life from Queen Esther, for he realized the king planned an evil end for him.
8 Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sarki ya tā da murya da ƙarfi ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya yayinda take tare da ni a cikin gida?” Sarki bai ma rufe baki ba, sai bayin sarki suka rufe fuskar Haman.
When the king came back in from the palace garden to the dining room, Haman had thrown himself on the couch where Queen Esther was. The king shouted out, “Is he even going to rape the queen here in the palace, right in front of me?” As soon as the king said this, the servants covered Haman's face.
9 Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.” Sai sarki ya ce, “Ku rataye shi a kansa!”
Then Harbonah, one of the eunuchs attending the king, said: “Haman set up a pole beside his house for Mordecai, the one whose report saved the king's life. The pole is fifty cubits high.” “Impale him on it!” the king ordered.
10 Saboda haka suka rataye Haman a kan wurin rataye mai laifin da shi Haman ya shirya saboda Mordekai. Sa’an nan sarki ya huce.
So they impaled Haman on the pole that he had set up for Mordecai. Then the anger of the king died down.

< Esta 7 >