Preface
Read
+
Publisher
Nainoia, Inc.
PO Box 462, Bellefonte, PA 16823
(814) 470-8028
Nainoia Inc, Publisher
LinkedIn/NAINOIA-INC
Third Party Publisher Resources
Request Custom Formatted Verses
Please contact us below
Submit your proposed corrections
I understand that the Aionian Bible republishes public domain and Creative Commons Bible texts and that volunteers may be needed to present the original text accurately. I also understand that apocryphal text is removed and most variant verse numbering is mapped to the English standard. I have entered my corrections under the verse(s) below. Proposed corrections to the Hausa Contemporary Bible, Esther Chapter 7 https://www.AionianBible.org/Bibles/Hausa---Contemporary/Esther/7 1) Saboda haka sarki da Haman suka tafi cin abinci wurin sarauniya Esta. 2) Yayinda suke shan ruwan inabi a rana ta biyun nan, sai sarki ya sāke tambaya, “Sarauniya Esta, me kike so? Za a ba ki. Mene ne roƙonki? Ko da rabin masarautata ne, za a ba ki.” 3) Sai Sarauniya Esta ta amsa ta ce, “In na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, in kuma mai girma ya yarda, a bar ni da raina, wannan shi ne roƙona. Ka kuma sa kada a kashe mutanena, wannan ita ce bukata. 4) Gama an sayar da ni da mutanena don a hallaka, a karkashe mu, a kuma ƙi mu. Da a ce an sayar da mu kamar bayi maza da mata ne, da na yi shiru, domin wannan zai zama abin da bai taka kara ya karye ba, har da za a dami sarki a kai.” 5) Sarki Zerzes ya tambayi Sarauniya Esta ya ce, “Wane ne shi? Ina mutumin da ya yi ƙarfin halin yin wannan karambani?” 6) Esta ta ce, “Maƙiyi da abokin gāban, shi ne wannan mugun Haman.” Sai Haman ya tsorota a gaban sarki da sarauniya. 7) Sarki ya tashi cikin fushi, ya bar ruwan inabinsa, ya fita zuwa cikin lambun fada. Amma da Haman ya gane cewa sarki ya riga ya yanke shawara a kan ƙaddararsa, ya dakata domin yă roƙi sarauniya Esta saboda ransa. 8) Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sarki ya tā da murya da ƙarfi ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya yayinda take tare da ni a cikin gida?” Sarki bai ma rufe baki ba, sai bayin sarki suka rufe fuskar Haman. 9) Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.” Sai sarki ya ce, “Ku rataye shi a kansa!” 10) Saboda haka suka rataye Haman a kan wurin rataye mai laifin da shi Haman ya shirya saboda Mordekai. Sa’an nan sarki ya huce. Additional comments?
Refresh Captcha
The world's first Holy Bible un-translation!