< 2 Korintiyawa 2 >

1 Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba.
Actually, I determined this within myself, that I would not come again to you in sorrow.
2 Gama in na sa ku baƙin ciki, wa ya rage yă faranta mini zuciya, in ba ku waɗanda na sa baƙin cikin ba?
For if I make you sorrowful, then who will make me glad, besides the one whom I made sorrowful?
3 Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka.
And I wrote this very thing to you so as not to have sorrow from those who ought to make me rejoice, when I come, having confidence in you all that my joy is also yours.
4 Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.
Now I wrote to you out of great distress and anguish of heart, with many tears, not that you should be made sorrowful, but that you might know the greatness of my love for you.
5 In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne.
So, if anyone has caused grief, he has not so much grieved me as he has all of you, to some extent—not to be too ‘heavy’.
6 Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka.
This punishment that was inflicted by the majority is sufficient to such a one,
7 Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa.
so that now, on the other side, you should forgive and comfort him, so that he not be overwhelmed by excessive sorrow.
8 Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku.
Therefore I urge you to reaffirm your love to him.
9 Abin da ya sa na rubuta muku shi ne don in ga ko za ku jimre da gwajin nan, kuna kuma yin biyayya ta kowace hanya.
Now I also wrote to this end: to put you to the test, to see whether you are obedient in all things.
10 In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi,
If you forgive anyone, I do too; further, if indeed I have forgiven anything to someone, I have done so for your sakes in the presence of Christ,
11 don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.
so that we not be exploited by Satan; for we are not ignorant of his intentions.
12 To, sa’ad da na tafi Toruwas don in yi wa’azin bisharar Kiristi, ko da yake na tarar cewa Ubangiji ya buɗe mini ƙofa,
Also, upon arriving in Troas for the Gospel of Christ, a door having been opened to me by Sovereign,
13 duk da haka, ban sami salama a zuciyata ba domin ban sami ɗan’uwana Titus a can ba. Sai na yi bankwana da su na wuce zuwa Makidoniya.
I had no rest in my spirit, because I did not find Titus my brother; so taking leave of them I went on into Macedonia.
14 Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina.
Now thanks be to the God who always leads us in triumph in the Christ, and through us spreads the fragrance of the knowledge of Him in every place.
15 Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka.
Because we are the aroma of Christ for God, among those who are being saved and among those who are being wasted—
16 Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin?
to these a smell of death into death, while to those a fragrance of life into life—and who is adequate for such things?
17 Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.
However, we are not like the rest who retail the word of God; rather, we speak in Christ, out of sincerity, as of God in His very presence.

< 2 Korintiyawa 2 >