< Revelation 19 >

1 After this I heard what sounded like the noise of an enormous crowd in heaven, shouting, “Hallelujah! Salvation, glory, and power describe our God,
Bayan wadannan abubuwa na ji wata karar da ta yi kamar muryar mutane masu yawa a sama suna cewa, “Halleluya. Ceto, daukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu.
2 because his judgments are true and right, for he has condemned the infamous prostitute who corrupted the earth with her immorality, and has brought her to justice for her murders of his servants.”
Hukunce - hukuncensa gaskiya ne da adalci, domin ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta kazamtar da duniya da fasikancinta. Ya dauki fansar jinin bayinsa, wadda ita da kanta ta zubar.”
3 Again they shouted, “Hallelujah! The smoke from her destruction ascends for ever and ever.” (aiōn g165)
Suka yi magana a karo na biyu: “Halleluya! Hayaki na tasowa daga wurinta har abada abadin.” (aiōn g165)
4 The twenty-four elders and the four living creatures fell down and worshipped God who sits on the throne. “Amen! Hallelujah!” they shouted.
Dattawan nan ashirin da hudu da rayayyun halittun nan hudu, suka fadi suka yi wa Allah sujada shi da yake zaune a kan kursiyin. Suna cewa, “Amin. Halleluya!”
5 A voice spoke from the throne that said, “Praise our God, everyone who serves him and respects him, from the smallest to the greatest.”
Sai wata murya ta fito daga kursiyin tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku bayinsa, ku da kuke tsoronsa, da duk marasa iko da masu iko.”
6 Then I heard what sounded like the noise of an enormous crowd, like rushing water and loud thunder, shouting, “Hallelujah! For the Lord our God, the All-powerful One, he reigns!
Sai na ji murya kamar na kasaitaccen taron mutane, kamar rurin kogi na ruwaye masu yawa, kuma kamar tsawar aradu, cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji yana mulki, Allah mai iko duka.
7 Let's celebrate and be glad and give him the glory, because the wedding day of the Lamb has arrived, and his bride has prepared herself.”
Bari mu yi murna, mu yi farinciki matuka mu kuma ba shi daukaka domin bikin auren Dan Ragon ya zo, amaryarsa kuma ta shirya kanta.
8 She was given fine linen to wear, white and clean. (Fine linen represents the good works of believers.)
An yardar mata ta sa kaya masu haske da tsabta na lilin mai laushi” (domin lilin mai laushi shine ayyukan adalci na tsarkaka).
9 The angel told me, “Write this down: How happy are those who are invited to the Lamb's wedding feast.” Then he said to me, “These are God's true words.”
Mala'ika ya ce mani, “Rubuta wannan: Masu albarka ne wadanda aka gayyace su zuwa bikin auren Dan Ragon.” Ya kuma ce mani, “Wadannan kalmomin Allah na gaskiya ne.”
10 I fell down at his feet to worship him. He told me, “Don't do that! I am one of God's servants just as you are, and those who accept Jesus' testimony. Worship God, for Jesus' testimony is the prophetic spirit.”
Na fadi a gaban kafafunsa domin in yi masa sujada, amma ya ce mani, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne tare da kai da 'yan'uwanka wadanda ke rike da shaida game da Yesu. Yi wa Allah sujada, domin shaida game da Yesu shine ruhun annabci.”
11 I saw heaven was opened. A white horse was standing there. Its rider was called Trustworthy and True. He is right when he judges, and he is right when he makes war.
Sai na ga sama a bude, na kuma duba sai ga wani farin doki. Mahayinsa ana kiransa amintacce da gaskiya. Yana shari'a da adalci yana yaki.
12 His eyes were like flaming fire. On his head were many crowns. He had a name written on him which no one but he himself knows.
Idanunsa kamar harshen wuta suke, a kansa akwai kambuna da yawa. Yana da suna a rubuce a jikinsa wanda ba wani da ya sani sai dai shi da kansa.
13 He wore a robe covered in blood, and his name is The Word of God.
Yana sanye da riga da aka tsoma a cikin jini, kuma ana kiran sunansa Kalmar Allah.
14 Heaven's armies were following him, riding on white horses and clothed in fine linen, white and clean.
Rundunonin sama suna biye da shi a kan fararen dawakai, suna sanye da lilin mai laushi, fari mai tsabta.
15 From his mouth came a sharp sword to strike the nations. He will rule them with an iron rod, and he himself treads the winepress of the All-powerful God's judgment.
Daga cikin bakinsa takobi mai kaifi na fitowa, da ita yake sarar al'ummai, zai kuma mulke su da sandar karfe. Yana tattake wurin matsar ruwan inabi da matsananciyar fushin Allah Mai iko duka.
16 Written on his robe and on his thigh was the name, King of kings and Lord of lords.
Yana da suna a rubuce a rigarsa da cinyarsa: “Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.”
17 I saw an angel standing in the sun, shouting in a loud voice to all the birds that fly in the sky, “Come and gather together for God's great feast.
Na ga mala'ika tsaye a rana. Yayi kira da murya mai karfi ga dukan tsuntsaye da ke firiya a sama.
18 Here you can eat the flesh of the dead: kings, leaders, and powerful men, as well as that of horses and their riders, the flesh of all people, free and slave, great and small.”
“Ku zo, ku tattaru saboda babban bukin Allah. Ku zo ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaki, da naman manyan mutane, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman dukan mutane, yantattu da bayi, marasa iko da masu iko.”
19 I saw the beast and the kings of the earth gathered together to wage war on the one sitting on the horse and his army.
Na ga dabban da sarakunan duniya da rundunoninsu. Suna tattaruwa domin su yi yaki da wanda ke bisa doki da rundunarsa.
20 The beast was captured, along with the false prophet who performed miracles in his presence (by which he deceived those who had received the mark of the beast and those who worshiped the beast's image). Both of them were thrown alive into the lake of fire that burns with sulfur. (Limnē Pyr g3041 g4442)
Aka kama dabban tare da makaryatan annabawa da suka yi ayyukan al'ajibai a gabansa. Da wadannan alamu ya yaudari wadanda suka karbi alamar dabbar da wadanda suka yi wa siffarta sujada. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin farar wuta mai ci. (Limnē Pyr g3041 g4442)
21 The rest were killed with the sword of the one sitting on the horse—the sword that came out of his mouth. All the birds gorged themselves on their flesh.
Sauran aka karkashe su da takobin da ke fitowa daga bakin mahayin dokin. Dukan tsuntsaye suka ci gawarwakinsu.

< Revelation 19 >