< Hebræerne 9 >

1 Vel havde også den første Pagt Forskrifter for Gudstjenesten og en jordisk Helligdom.
To ko da alkawarin farko ma ya na da wurin sujada da kuma ka'idojin sujada a nan duniya.
2 Thi der var indrettet et Telt, det forreste, hvori Lysestagen var og Bordet og Skuebrødene, det, som jo kaldes det Hellige.
Domin a cikin alfarwar akwai daki da aka shirya, daki na waje wanda ake kira wuri mai tsarki. A wannan wuri akwai kebabbun fitilu, akwai teburi da kuma gurasa.
3 Men bag det andet Forhæng var et Telt, det, som kaldes det Allerhelligste,
Kuma bayan labule na biyun akwai wani daki, wanda ake kira wuri mafi tsarki.
4 som havde et gyldent Røgelsealter og Pagtens Ark, overalt beklædt med Guld, i hvilken der var en Guldkrukke med Mannaen, og Arons Stav, som havde blomstret, og Pagtens Tavler,
Yana da bagadin zinariya domin turare. Yana kuma da akwatin alkawarin, wanda aka lailaye shi gaba daya da zinariya. A cikinsa a kwai kaskon zinariya dake dauke da manna, da sandar Haruna wadda tayi toho, da kuma allunan duwatsu na alkawarin.
5 men oven over den var Herlighedens Keruber, som overskyggede Nådestolen, hvorom der nu ikke skal tales enkeltvis.
A sama da akwatin alkawarin akwai siffofin kerubobi masu daukaka da suke wa marfin jinkai inuwa, wadanda yanzu ba zamu iya yin bayani akansu ba daki daki.
6 Idet nu dette er således indrettet, gå Præsterne til Stadighed ind i det forreste Telt, når de forrette Tjenesten;
Bayan an shirya wadannan abubuwa, firistocin alfarwar sukan shiga daki na wajen alfarwar akai akai suna aikin hidimominsu.
7 men i det andet går alene Ypperstepræsten ind een Gang om Året, ikke uden Blod, hvilket han ofrer for sig selv og Folkets Forseelser,
Amma babban firist din ne kadai yake shiga daki na biyun, sau daya tak a shekara, kuma tilas sai tare da jinin hadaya domin kansa, da kuma domin laifuffukan mutane da a kayi ba dagangan ba.
8 hvorved den Helligånd giver til Kende, at Vejen til Helligdommen endnu ikke er bleven åbenbar, så længe det førreste Telt endnu står,
Ruhu Mai Tsarki yana nuna cewar ba'a riga an bayyana hanyar zuwa wuri mafi Tsarki ba muddin alfarwar nan ta farko na a tsaye.
9 hvilket jo er et Sindbillede indtil den nærværende Tid, og stemmende hermed frembæres der både Gaver og Ofre, som ikke i Henseende til Samvittigheden kunne fuldkomme den, der forretter sin Gudsdyrkelse,
Wannan ya zama bayani ne game da lokacin yanzu. Da kyaututtuka da hadayu dukka da ake mikawa basu iya sun kammala lamirin mai yin sujadar ba.
10 men som kun, ved Siden af Mad og Drikke og forskellige Tvættelser, ere kødelige Forskrifter, pålagte indtil den rette Ordnings Tid.
Abinci ne da abin sha kawai wadanda aka hada da bukukuwan wanke wanke dabam dabam. Wadannan duka tsare tsare ne da aka shirya a dinga yi a zahiri har sai an shirya sabuwar ka'ida.
11 Men da Kristus kom som Ypperstepræst for de kommende Goder, gik han igennem det større og fuldkomnere Telt, som ikke er gjort med Hænder, det er: som ikke er af denne Skabning,
Almasihu yazo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da suka zo, ta wurin alfarwa babba, kammalalla kuma mafi tsarki wadda ba hannuwan mutane suka gina ba, wadda ba ta wannan duniyar aka halicce ta ba. Amma almasihu ya zo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da ke zuwa.
12 og gik ikke heller med Blod af Bukke eller Kalve, men med sit eget Blod een Gang for alle ind i Helligdommen og vandt en evig Forløsning. (aiōnios g166)
Ba ta jinin awaki da 'yan, maruka bane, amma Almasihu da jininsa ya shiga wuri mafi tsarki sau daya tak domin kowa dukka ya karbo mana fansa ta har abada. (aiōnios g166)
13 Thi dersom Blodet af Bukke og Tyre og Aske af en Kvie ved at stænkes på de besmittede helliger til Kødets Renhed:
To idan jinin awaki da na bajimai da yayyafa tokar karsana bisa wadanda suka bata tsarkinsu yana tsarkake su ya wanke jikkunansu.
14 hvor meget mere skal da Kristi Blod, hans, som ved en evig Ånd frembar sig selv lydeløs for Gud, rense eders Samvittighed fra døde Gerninger til at tjene den levende Gud? (aiōnios g166)
To balle kuma jinin Almasihu, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya mika kansa hadaya marar aibi ga Allah, wanda yake wanke lamirinmu daga matattun ayyuka domin muyi bautar Allah mai rai? (aiōnios g166)
15 Og derfor er han Mellemmand for en ny Pagt, for at de kaldede, da der har fundet Død Sted til Genløsning fra Overtrædelserne under den første Pagt, må få den evige Arvs Forjættelse. (aiōnios g166)
Domin wannan dalili, Almasihu shine magamin sabon alkawari. Wannan kuwa ya kasance ne domin anyi mutuwar da ta 'yantar da wadanda ke karkashin tsohon alkawari daga sakamakon zunubansu, saboda wadanda Allah ya kira su karbi alkawarin gadonsu madawwami. (aiōnios g166)
16 Thi hvor der er en Arvepagt, der er det nødvendigt, at hans Død, som har oprettet Pagten, skal godtgøres.
Gama duk inda wani ya rubuta wasiyya ya bari, dole ne a tabbatar da mutuwar wanda yayi wasiyyar nan.
17 Thi en Arvepagt er urokkelig efter døde, da den ingen Sinde træder i Kraft, medens den, som har oprettet den, lever.
Gama sai inda akayi mutuwa ake amfani da wasiyya, amma ba ta da amfani idan wanda ya rubuta ta yana nan da rai.
18 Derfor er heller ikke den første bleven indviet uden Blod
Ko alkawari na farko bai tabbata ba sai tare da jini.
19 Thi da hvert Bud efter Loven var forkyndt af Moses for hele Folket, tog han Kalve- og Bukkeblod med Vand og skarlagenrød Uld og Isop og bestænkede både Bogen selv og hele Folket, idet han sagde:
Gama bayan Musa ya bada dukkan dokoki da ke cikin shari'ar ga dukkan mutanen, sai ya dauki jinin 'yan marukan da awakin, tare da ruwa, da jan yadi, da reshen itacen doddoya mai soso, ya yayyafa bisa mutanen da kuma littafin dokokin.
20 "Dette er den Pagts Blod, hvilken Gud har pålagt eder."
Daga nan yace, “Wannan ne jinin alkawarin da Allah ya bayar da dokoki gareku.”
21 Og Tabernaklet og alle Tjenestens Redskaber bestænkede han ligeledes med Blodet.
Ta haka kuma, ya yayyafa jinin bisa alfarwar da dukkan kayayyakin da ke cikinta wanda ake hidimar firistanci da su.
22 Og næsten alt bliver efter Loven renset med Blod, og uden Blods Udgydelse sker der ikke Forladelse.
Kuma bisa ga shari'a, kusan komai da jini ake tsarkake shi. Idan babu zubar da jini to babu gafarar zunubi.
23 Altså var det en Nødvendighed, at Afbildningerne af de himmelske Ting skulde renses herved, men selve de himmelske Ting ved bedre Ofre end disse.
Saboda haka ya zama tilas wadannan kayayyaki na kwaikwayon abubuwan dake cikin sama a tsarkake su da hadayar dabbobi. Duk da haka abubuwa na sama dole a tsarkake su da hadaya mafi kyau.
24 Thi Kristus gik ikke ind i en Helligdom, som var gjort med Hænder og kun var et Billede af den sande, men ind i selve Himmelen for nu at træde frem for Guds Ansigt til Bedste for os;
Domin Almasihu bai shiga cikin wuri mafi tsarki da aka yi da hannuwa ba, wanda kwaikwayo ne kawai na abin da ke na gaske. Maimakon hakan, ya shiga cikin samaniya da kanta, sa'an nan yaje gaban Allah domin mu.
25 ikke heller for at han skulde ofre sig selv mange Gange, ligesom Ypperstepræsten hvert År går ind i Helligdommen med fremmed Blod;
Bai je wurin don ya mika kansa sau da yawa, kamar yadda firist din alfarwa yake yi ba, wanda yake shiga wuri mafi tsarki kowacce shekara da jinin wata dabba.
26 ellers havde han måttet lide mange Gange fra Verdens Grundlæggelse; men nu er han een Gang for alle ved Tidernes Fuldendelse åbenbaret for at bortskaffe Synden ved sit Offer. (aiōn g165)
Idan haka ne, to dole ke nan ya sha wahala akai akai tun farkon duniya. Amma yanzu sau daya ne tak aka bayyana shi a karshen zamanai domin ya kauda zunubi ta wurin mika hadayar kansa. (aiōn g165)
27 Og ligesom det er Menneskene beskikket at dø een Gang og derefter Dom,
Kamar yadda aka kaddara wa kowa ya mutu sau daya tak, kuma bayan haka sai shari'a.
28 således skal også Kristus, efter at være bleven een Gang ofret for at bære manges Synder, anden Gang, uden Synd, vise sig for dem, som foruente ham til Frelse.
Haka kuma Almasihu, wanda aka mika shi sau daya tak domin ya dauke zunuban mutane da yawa, zai kuma bayyana karo na biyu, ba domin yin aikin kawar da zunubi ba, amma domin ceton wadanda suke jiran zuwansa da hakuri.

< Hebræerne 9 >