< Titus 3 >
1 Påmind dem om at underordne sig Øvrigheder og Myndigheder, at adlyde, at være redebonne til al god Gerning.
Ka tuna masu su zama masu sadaukar da kai ga masu mulki da masu iko, suyi masu biyayya, su zama a shirye domin kowane kyakkyawan aiki.
2 ikke at forhåne nogen, ikke være stridslystne, men milde, og udvise al Sagtmodighed imod alle Mennesker.
Ka tuna masu kada su zagi kowa, su gujiwa gardama, su bar mutane su bi hanyarsu, su kuma nuna tawali'u ga dukan mutane.
3 Thi også vi vare fordum uforstandige, ulydige, vildfarende, Slaver af Begæringer og, mange Hånde Lyster, vi levede i Ondskab og Avind, vare forhadte og hadede hverandre.
Domin a da, mu da kan mu marasa tunani ne kuma masu rashin biyayya. Mun kauce hanya muka zama bayi ga sha'awoyin duniya da annashuwa. Mun yi zama a cikin mugunta da kishi. Mu lalatattu ne kuma muna kiyyaya da junanmu.
4 Men da Guds, vor Frelsers Godhed og Menneskekærlighed åbenbaredes,
Amma da jinkan Allah mai ceton mu da kaunarsa ga 'yan Adam ta bayyana,
5 frelste han os, ikke for de Retfærdigheds Gerningers Skyld, som vi havde gjort, men efter sin Barmhjertighed, ved Igenfødelsens Bad og Fornyelsen i den Helligånd,
ba saboda wani aikin adalci da muka yi ba, amma sabili da jinkan sa ne ya cece mu. Ya cece mu ta wurin wankewar sabuwar haihuwa da sabuntuwar Ruhu Mai Tsarki.
6 som han rigeligt udøste over os ved Jesus Kristus, vor Frelser,
Allah ya zubo mana Ruhu Mai Tsarki a wadace ta wurin Yesu Almasihu mai cetonmu.
7 for at vi, retfærdiggjorte ved hans Nåde, skulde i Håb vorde Arvinger til evigt Liv. (aiōnios )
Ya yi wannan saboda, bayan mun samu 'yantarwa ta wurin alherinsa, za mu zama magada a cikin begen rai na har abada. (aiōnios )
8 Den Tale er troværdig, og derom vil jeg, at du skal forsikre dem, for at de, som ere komne til Tro på Gud, skulle lægge Vind på at øve gode Gerninger. Dette er Menneskene godt og nyttigt.
Wannan amintaccen sako ne. Ina son kayi magana gabagadi game da wadannan abubuwa, yadda dukan wadanda suka bada gaskiya ga Allah za suyi kudirin yin kyawawan ayyuka da Allah ya mika masu. Waddannan abubuwa masu kyau ne da kuma riba ga dukan mutane.
9 Men hold dig fra tåbelige Stridigheder og Slægtregistre og Kiv og Kampe om Loven; thi de ere unyttige og frugtesløse.
Amma ka guji gardandami na wofi, da lissafin asali, da husuma da jayayya game da dokoki. Wadannan abubuwa basu da amfani kuma marasa riba.
10 Et kættersk Menneske skal du afvise efter een og to Ganges Påmindelse,
Ka ki duk wani dake kawo tsattsaguwa a tsakaninku, bayan ka tsauta masa sau daya ko biyu,
11 da du ved, at en sådan er forvendt og synder, domfældt af sig selv.
ka kuma sani cewa wannan mutumin ya kauce daga hanyar gaskiya, yana zunubi kuma ya kayar da kansa.
12 Når jeg sender Artemas til dig eller Tykikus, da gør dig Flid for at komme til mig i Nikopolis; thi der har jeg besluttet at overvintre.
Sa'adda na aiki Artimas da Tikikus zuwa wurin ka, kayi hanzari ka same ni a Nikobolis, a can na yi shirin kasancewa a lokacin hunturu.
13 Zenas den lovkyndige og Apollos skal du omhyggeligt hjælpe på Vej, for at intet skal fattes dem.
Kayi hanzari ka aiko Zinas wanda shi gwani ne a harkar shari'a, da Afolos ta yadda ba zasu rasa komai ba.
14 Men lad også vore lære at øve gode Gerninger, hvor der er Trang dertil, for at de ikke skulle være uden Frugt.
Ya kamata Jama'armu su koyi yadda zasu yi ayyuka masu kyau da zasu biya bukatu na gaggawa yadda ba za suyi zaman banza ba.
15 Alle, som ere hos mig, hilse dig. Hils dem, som elske os i Troen. Nåden være med eder alle!
Dukan wadanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gai da masu kaunar mu a cikin bangaskiya. Alheri ya kasance tare da dukan ku.