< 马可福音 14 >
1 过两天是逾越节,又是除酵节,祭司长和文士想法子怎么用诡计捉拿耶稣,杀他。
Idin Ketarewa da bukin gurasa mara yisti sauran kwana biyu kenan, sai shugabanin firistoci da malaman attaura suka nemi yadda zasu kama Yesu a asirce domin su kashe shi.
Suna cewa amma “Ba a lokacin idin ba, domin kada su haddasa hargitsi a tsakanin mutane”.
3 耶稣在伯大尼长大麻风的西门家里坐席的时候,有一个女人拿着一玉瓶至贵的真哪哒香膏来,打破玉瓶,把膏浇在耶稣的头上。
Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana shirin liyafa kenan sai ga wata mace dauke da kwalbar turare mai tamanin kwarai, ta shafa masa a kansa.
4 有几个人心中很不喜悦,说:“何用这样枉费香膏呢?
wasu dake tare da Yesu suka husata, suna kwalbarta da cewa
5 这香膏可以卖三十多两银子周济穷人。”他们就向那女人生气。
“Ai wannan turare ne mai tsada, ina laifin a sayar a raba wa talakawa kudin? ina dalilin wannan almubazaranci?
6 耶稣说:“由她吧!为什么难为她呢?她在我身上做的是一件美事。
Sai Yesu yace masu “Ku kyaleta, don me kuke tsauta mata,
7 因为常有穷人和你们同在,要向他们行善随时都可以;只是你们不常有我。
ai Idan kuna da niyyar taimakon talakawa ko matalauta, suna nan tare da ku ko a yaushe amma ni bazan kasance da ku kullum ba.
8 她所做的,是尽她所能的;她是为我安葬的事把香膏预先浇在我身上。
Macen nan tayi aiki nagari domin shirya jikina ga jana'iza.
9 我实在告诉你们,普天之下,无论在什么地方传这福音,也要述说这女人所做的,以为记念。”
hakika, Ina gaya maku, duk inda za'a yi bishara a duniya baza a mance da matan nan da hidimar da ta tayi mini ba.”
10 十二门徒之中,有一个加略人犹大去见祭司长,要把耶稣交给他们。
Da jin haka sai Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin manzannin ya ruga zuwa wurin baban firist domin ya bashe shi a garesu,
11 他们听见就欢喜,又应许给他银子;他就寻思如何得便把耶稣交给他们。
Da mayan firistoci suka ji haka suka yi murna matuka tare da alkawarin kudi ga Yahuza, shi kuwa sai ya fara neman zarafin da zai mika Yesu a gare su.
12 除酵节的第一天,就是宰逾越羊羔的那一天,门徒对耶稣说:“你吃逾越节的筵席要我们往哪里去预备呢?”
A ranar farko ta bukin gurasa marar yisti da kuma hadayar ragon Idin ketarewa, almajiransa suka ce masa “Ina zamu shirya liyafar domin idin ketarewa?
13 耶稣就打发两个门徒,对他们说:“你们进城去,必有人拿着一瓶水迎面而来,你们就跟着他。
Ya aiki biyu daga cikin almajiransa da cewa “Ku shiga cikin birnin, zaku tarar da wani mutum dauke da tullun ruwa.
14 他进哪家去,你们就对那家的主人说:‘夫子说:客房在哪里?我与门徒好在那里吃逾越节的筵席。’
Duk gidan da ya shiga ku bishi, sai ku cewa mai gidan, malam yace “ina bukatar masauki domin hidimar idin ketarewa tare da almajiraina?”'
15 他必指给你们摆设整齐的一间大楼,你们就在那里为我们预备。”
Zai kuwa nuna maku babban bene gyararre. Sai ku yi mana shiri a can.”
16 门徒出去,进了城,所遇见的正如耶稣所说的。他们就预备了逾越节的筵席。
Da shigar almajiran cikin birnin, sai kome ya kasance yadda ya fada, su kuwa suka yi shirye shiryen idin ketarewar.
Da maraice ta yi, sai ya tare da sha biyun.
18 他们坐席正吃的时候,耶稣说:“我实在告诉你们,你们中间有一个与我同吃的人要卖我了。”
Yayin da suke zazzaune a teburin suna cin abincin, sai Yesu ya ce “Hakika ina gaya maku wani da ke ci tare da ni a nan zai bashe ni”.
19 他们就忧愁起来,一个一个地问他说:“是我吗?”
Sai suka damu suka tambaye shi daya bayan daya suna cewa “Hakika bani bane ko?”
20 耶稣对他们说:“是十二个门徒中同我蘸手在盘子里的那个人。
Yesu ya amsa masu da cewa “Daya daga cikin sha biyu ne, wanda ke sa hannu tare da ni yanzu cikin tasar”.
21 人子必要去世,正如经上指着他所写的;但卖人子的人有祸了!那人不生在世上倒好。”
Dan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi amma kaiton wanda zai bashe shi! “zai, fiye masa, dama ba a haife shi ba”.
22 他们吃的时候,耶稣拿起饼来,祝了福,就擘开,递给他们,说:“你们拿着吃,这是我的身体”;
Lokacin da suke cin abincin, Yesu ya dauki gurasa ya sa albarka, ya gutsuttsura ta, sai ya basu yana cewa “Wannan jikinana ne”.
Ya kuma dauki koko, yayi godiya, ya basu, su kuwa suka sha daga kokon.
Ya ce “Wannan jinina ne na alkawari da an zubar ga yawancin mutane”.
25 我实在告诉你们,我不再喝这葡萄汁,直到我在 神的国里喝新的那日子。”
Hakika, bazan kara sha daga wannan ruwan inabi ba sai a ranar da zan sha sabo cikin mulkin Allah.”
Bayan sun raira wakar yabo ga Allah, sai suka tafi wurin dutsen zaitun.
27 耶稣对他们说:“你们都要跌倒了,因为经上记着说: 我要击打牧人, 羊就分散了。
Yesu ya ce masu dukkan ku zaku yi tuntube harma ku fadi saboda ni gama rubuce take cewa “Zan buge makiyayin, tumakin kuwa za su watse;
Amma bayan tashina, zai yi gaba in riga ku zuwa Galili.
Bitrus ya ce masa “ko dukkansu sun fadi, faufau banda ni”.
30 耶稣对他说:“我实在告诉你,就在今天夜里,鸡叫两遍以先,你要三次不认我。”
Yesu yace masa “Hakika ina gaya maka, cikin wannan dare kafin carar zakara ta biyu zaka yi musun sani na sau uku”.
31 彼得却极力地说:“我就是必须和你同死,也总不能不认你。”众门徒都是这样说。
Amma Bitrus ya sake cewa “Koda za'a kasheni tare da kai ba zan yi musun sanin ka ba”. Dukkan su kuwa suka yi wannan Alkawari.
32 他们来到一个地方,名叫客西马尼。耶稣对门徒说:“你们坐在这里,等我祷告。”
Suka isa wani wuri da ake kira Getsamani, sai Yesu ya ce wa almajiransa “Ku dakata anan domin zan je inyi addu'a”.
33 于是带着彼得、雅各、约翰同去,就惊恐起来,极其难过,
Sai ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya. Ya fara jin wahala mutuka tare da damuwa kwarai.
34 对他们说:“我心里甚是忧伤,几乎要死;你们在这里等候,警醒。”
Sai ya ce masu “Raina na shan wahala harma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a fadake”.
35 他就稍往前走,俯伏在地,祷告说:“倘若可行,便叫那时候过去。”
Da Yesu yayi gaba kadan, sai ya fadi kasa yayi addu'a yana cewa idan mai yiwuwa ne “A dauke masa wannan sa'a daga gare shi.
36 他说:“阿爸!父啊!在你凡事都能;求你将这杯撤去。然而,不要从我的意思,只要从你的意思。”
Ya ce “Ya Abba Uba, kome mai yuwane gare ka, ka dauke mini kokon wahalan nan, duk da haka ba nufina ba sai dai naka”.
37 耶稣回来,见他们睡着了,就对彼得说:“西门,你睡觉吗?不能警醒片时吗?
Da komowarsa ya same su suna barci, sai ya ce wa Bitrus, Siman barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a fadake ko da sa'a daya ba?
38 总要警醒祷告,免得入了迷惑。你们心灵固然愿意,肉体却软弱了。”
Ku zauna a fadake, kuyi addu'a kada ku fada cikin jaraba. Lalle ruhu na da niyya amma jiki raunana ne.
Sai ya sake komawa, yayi addu'a, yana maimaita kalmominsa na farko.
40 又来见他们睡着了,因为他们的眼睛甚是困倦;他们也不知道怎么回答。
Har wa yau kuma ya sake dawowa, ya same su suna barci don barci ya cika masu idanu kwarai, sun kuwa kasa ce masa kome.
41 第三次来,对他们说:“现在你们仍然睡觉安歇吧!够了,时候到了。看哪,人子被卖在罪人手里了。
Ya sake komowa karo na uku yace masu “har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka! Lokaci yayi, an bada Dan Mutum ga masu zunubi”.
Ku tashi mutafi kun ga, ga mai bashe ni nan ya kusato.”
43 说话之间,忽然那十二个门徒里的犹大来了,并有许多人带着刀棒,从祭司长和文士并长老那里与他同来。
Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, daya daga cikin sha biyun da taron jama'a rike da takkuba da kulake. Manyan firistoci da malaman attaura da shugabanni suka turo su.
44 卖耶稣的人曾给他们一个暗号,说:“我与谁亲嘴,谁就是他。你们把他拿住,牢牢靠靠地带去。”
Mai bashe shi din nan ya riga ya kulla da su cewa “Wanda zan yi wa sumba shine mutumin, ku kama shi ku tafi da shi a tsare.
45 犹大来了,随即到耶稣跟前,说:“拉比”,便与他亲嘴。
Da isowarsa kuwa, sai ya zo wurin Yesu ya ce “Ya malam!”. Sai ya sumbace shi.
Su kuwa suka kama shi, suka tafi da shi.
47 旁边站着的人,有一个拔出刀来,将大祭司的仆人砍了一刀,削掉了他一个耳朵。
Amma daya daga cikin na tsaye ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya yanke masa kunne.
48 耶稣对他们说:“你们带着刀棒出来拿我,如同拿强盗吗?
Sai Yesu ya ce “kun fito kamar masu kama yan fashi da takkuba da kulake, domin ku kama ni?
49 我天天教训人,同你们在殿里,你们并没有拿我。但这事成就,为要应验经上的话。”
Lokacin da nake koyarwa a Haikali, kowace rana da ku, baku kama ni ba. Amma anyi haka ne domin a cika abinda Nassi ya fada.”
Daga nan duk wadanda suke tare da Yesu suka yashe shi, suka tsere.
51 有一个少年人,赤身披着一块麻布,跟随耶稣,众人就捉拿他。
Wani saurayi, daga shi sai mayafi ya bi shi, suka kai masa cafka.
Shi kuwa ya bar masu mayafin ya gudu tsirara.
53 他们把耶稣带到大祭司那里,又有众祭司长和长老并文士都来和大祭司一同聚集。
Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. a can suka tara dattawa duk da manyan firistoci da shugabanni da marubuta, suka taru a wurinsa.
54 彼得远远地跟着耶稣,一直进入大祭司的院里,和差役一同坐在火光里烤火。
Bitrus kuwa ya bi shi daga nesa har cikin gidan babban firist. Ya zauna tare da dogaran Haikalin, yana jin dumin wuta.
55 祭司长和全公会寻找见证控告耶稣,要治死他,却寻不着。
Sai, manyan firistoci da duk 'yan majalisa Yahudawa suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi. Amma basu samu ba.
56 因为有好些人作假见证告他,只是他们的见证各不相合。
Da yawa kuma suka yi masa shaidar Zur (Karya), amma bakin su bai zama daya ba.
Sai wadansu kuma suka taso suka yi masa shaidar zur (karya) suka ce.
58 “我们听见他说:‘我要拆毁这人手所造的殿,三日内就另造一座不是人手所造的。’”
“Mun ji ya ce, wai zai rushe haikalin nan da mutane suka gina, ya sake gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba”.
Duk da haka, sai shaidar tasu bata zo daya ba.
60 大祭司起来站在中间,问耶稣说:“你什么都不回答吗?这些人作见证告你的是什么呢?”
Sai babban firist ya mike a tsakanin su, ya tambayi Yesu yace “Ba ka da wata amsa game da shaidar da mutanen nan suke yi a kanka?
61 耶稣却不言语,一句也不回答。大祭司又问他说:“你是那当称颂者的儿子基督不是?”
Amma yayi shiru abinsa, bai ce kome ba. Sai babban firist din ya sake tambayarsa “To, ashe kai ne Allmasihu Dan Madaukaki?
62 耶稣说:“我是。你们必看见人子坐在那权能者的右边,驾着天上的云降临。”
Yesu ya ce “Nine. Za ku kuwa ga Dan Mutum zaune dama ga mai iko, yana kuma zuwa cikin gajimare”.
63 大祭司就撕开衣服,说:“我们何必再用见证人呢?
Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa yace “Wacce shaida kuma zamu nema?
64 你们已经听见他这僭妄的话了。你们的意见如何?”他们都定他该死的罪。
Kun dai ji sabon da yayi! Me kuka gani? Duk suka yanke masa hukunci akan ya cancanci kisa.
65 就有人吐唾沫在他脸上,又蒙着他的脸,用拳头打他,对他说:“你说预言吧!”差役接过他来,用手掌打他。
Wadansu ma suka fara tottofa masa yau, suka daure masa idanu, suka bubbuge shi suna cewa “Yi annabci” Dogaran kuma suka yi ta marinsa.
Bitrus kuwa na kasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo.
67 见彼得烤火,就看着他,说:“你素来也是同拿撒勒人耶稣一伙的。”
Da ta ga Bitrus na jin dumi, ta yi masa kallon gaske ta ce “Kaima ai tare kake da banazaren nan Yesu”.
68 彼得却不承认,说:“我不知道,也不明白你说的是什么。”于是出来,到了前院,鸡就叫了。
Amma ya musa ya ce “Ni ban ma san abinda kike fada ba balle in fahimta”. Sai ya fito zaure. Sai zakara yayi cara.
69 那使女看见他,又对旁边站着的人说:“这也是他们一党的。”
Sai baranyar ta ganshi, ta sake ce wa wadanda ke tsaitsaye a wurin, “Wannan ma daya daga cikinsu ne”.
70 彼得又不承认。过了不多的时候,旁边站着的人又对彼得说:“你真是他们一党的!因为你是加利利人。”
Amma ya sake musawa, jim kadan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus “Lalle kai ma dayansu ne don ba Galile ne kai”.
71 彼得就发咒起誓地说:“我不认得你们说的这个人。”
Sai ya fara la'anta kansa yana ta rantsuwa yana ce wa “Ban ma san mutumin nan da kuke fada ba”.
72 立时鸡叫了第二遍。彼得想起耶稣对他所说的话:“鸡叫两遍以先,你要三次不认我。”思想起来,就哭了。
Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu, Bitrus kuwa ya tuna da maganar Yesu a gare shi cewa “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sani na sau uku”. Da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.