< 马可福音 13 >

1 耶稣从殿里出来的时候,有一个门徒对他说:“夫子,请看,这是何等的石头!何等的殿宇!”
da Yesu ke fita daga Haikalin, sai daya daga cikin almajirnsa ya ce masa “malam, dubi kyawawan duwatsunnan da kyawawan gine-ginnenan!”
2 耶稣对他说:“你看见这大殿宇吗?将来在这里没有一块石头留在石头上,不被拆毁了。”
Ya ce masa, ka ga wadannan kyawawan gine- ginen? babu wani dutsen da za a bar shi akan dan'uwansa, da ba za a rushe shi ba.”
3 耶稣在橄榄山上对圣殿而坐。彼得、雅各、约翰,和安得烈暗暗地问他说:
Yana zaune a kan dutsen zaitun wanda yake kusa da Haikali, sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawus suka tambaye shi a asirce, suka ce.
4 “请告诉我们,什么时候有这些事呢?这一切事将成的时候有什么预兆呢?”
Gaya mana yaushe za a yi wadannan abubuwa? mecece zata zama alamar faruwar wadanna abubuwa da zasu faru?''
5 耶稣说:“你们要谨慎,免得有人迷惑你们。
Yesu ya ce masu, “ku kula, kada kowa ya rudeku.
6 将来有好些人冒我的名来,说:‘我是基督’,并且要迷惑许多人。
Da yawa za su zo da sunana, suna cewa nine shi, har su bad da mutane da yawa.
7 你们听见打仗和打仗的风声,不要惊慌。这些事是必须有的,只是末期还没有到。
In kuka ji labarin yake- yake, da jita-jitarsu kada ku damu, wannan zai faru, amma karshen duniya bai gabato ba.
8 民要攻打民,国要攻打国;多处必有地震、饥荒。这都是灾难的起头。
Al'umma za ta tasarwa al'umma, mulki ya tasarwa mulki. Za a yi girgizar kasa awurare dabam-dabam, da kuma yunwa, amma fa dukkan wadanna abubuwan mafarin azaba ne.
9 但你们要谨慎;因为人要把你们交给公会,并且你们在会堂里要受鞭打,又为我的缘故站在诸侯与君王面前,对他们作见证。
Amma, ku zauna a fadake. Don za su kai ku gaban majalisa. za a yi maku duka a cikin majami'u. Su kuma kai ku gaban masu mulki da sarakuna, saboda sunana, domin ku ba da shaida a gare su.
10 然而,福音必须先传给万民。
Amma lallai sai an fara yi wa dukkan al, ummai bishara.
11 人把你们拉去交官的时候,不要预先思虑说什么;到那时候,赐给你们什么话,你们就说什么;因为说话的不是你们,乃是圣灵。
Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka mika ku, kada ku damu a wannan lokacin, za a baku abin da zaku fada, Amma duk abin da aka yi muku a wannn lokacin, shi za ku fada, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu mai tsarki ne.
12 弟兄要把弟兄,父亲要把儿子,送到死地;儿女要起来与父母为敌,害死他们;
Dan'uwa zai bada dan'uwarsa akashe shi, uba kuwa dansa. Yara kuma zasu tayar wa iyayensu har su sa akashe su.
13 并且你们要为我的名被众人恨恶。惟有忍耐到底的,必然得救。”
Za a ki ku saboda sunana, amma duk wanda ya jumre har karshe zai cetu.
14 “你们看见那行毁坏可憎的,站在不当站的地方(读这经的人须要会意)。那时,在犹太的,应当逃到山上;
Sa'adda kuka ga an kafa mummunan aikin sabo mai ban kyama a wurin da bai kamata ba (bari mai karatu ya fahimta), to, bari wadanda suke kasar Yahudiya, su gudu zuwa dutse.
15 在房上的,不要下来,也不要进去拿家里的东西;
Wanda yake tudu kuma kada ya sauko ya shiga gida garin daukar wani abu.
16 在田里的,也不要回去取衣裳。
Wanda yake gona kuma kada ya koma garin daukar mayafinsa.
17 当那些日子,怀孕的和奶孩子的有祸了!
Amma, kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokacin.
18 你们应当祈求,叫这些事不在冬天临到。
Ku yi addu, a kada abin ya faru da damina.
19 因为在那些日子必有灾难,自从 神创造万物直到如今,并没有这样的灾难,后来也必没有。
A lokacin za ayi wata matsanaciyar wahala, wadda bata taba faruwa ba, tun farkon halittar da Allah ya yi har zuwa yau, ba kuwa za a taba yi ba har abada.
20 若不是主减少那日子,凡有血气的,总没有一个得救的;只是为主的选民,他将那日子减少了。
In da ba ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba Dan adam din zai tsira. Amma saboda zabbabunan da ya zaba, ya rage kwanakin.
21 那时若有人对你们说:‘看哪,基督在这里’,或说:‘基督在那里’,你们不要信!
To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata.
22 因为假基督、假先知将要起来,显神迹奇事,倘若能行,就把选民迷惑了。
Gama almasihan karya, da annabawan karya zasu bayyana kuma, zasu yi abubuwan al'ajibai masu ban mamaki.
23 你们要谨慎。看哪,凡事我都预先告诉你们了。”
Amma ku zauna a fadake, Na dai fada maku wadannan abubuwan kafin lokacin.
24 “在那些日子,那灾难以后, 日头要变黑了, 月亮也不放光,
Amma, bayan matsanaciyar wahalannan, rana zata duhunta, wata kuma ba zai bada haske ba.
25 众星要从天上坠落, 天势都要震动。
Taurari za su fado daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.
26 那时,他们要看见人子有大能力、大荣耀,驾云降临。
Sa' annan zasu ga Dan mutum na zuwa a cikin gajimare, da iko mai girma da daukaka.
27 他要差遣天使,把他的选民,从四方,从地极直到天边,都招聚了来。”
Zai aiko da mala'ikunsa su tattaro zabbabunsa daga kusuwoyi hudu na duniya(watau Gabas da Yamma, kudu da Arewa) har zuwa karshen sama.
28 “你们可以从无花果树学个比方:当树枝发嫩长叶的时候,你们就知道夏天近了。
“Ku yi koyi da itacen baure. Da zarar rassansa sun fara taushi yana kuma fitar da toho, kun san damina ta yi kusa ke nan.
29 这样,你们几时看见这些事成就,也该知道人子近了,正在门口了。
Sa'adda kuka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku dai sani ya kusato, a bakin kofa ma ya ke.
30 我实在告诉你们,这世代还没有过去,这些事都要成就。
Hakika ina gaya maku, zamanin nan ba zai shude ba sai dukan abubuwan nan sun faru.
31 天地要废去,我的话却不能废去。”
Sararin sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba.
32 “但那日子,那时辰,没有人知道,连天上的使者也不知道,子也不知道,惟有父知道。
Amma wannan rana ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai dai Uban kadai.
33 你们要谨慎,警醒祈祷,因为你们不晓得那日期几时来到。
Ku kula, ku zauna a fadake, kuna addu'a don baku san ranar da lokacin zai yi ba.
34 这事正如一个人离开本家,寄居外邦,把权柄交给仆人,分派各人当做的工,又吩咐看门的警醒。
Kamar yadda mutum mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta bayinsa kan gidansa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai gadi ya zauna a fadake.
35 所以,你们要警醒;因为你们不知道家主什么时候来,或晚上,或半夜,或鸡叫,或早晨;
To, ku zauna a fadake don ba ku san lokacin da maigidan zai zo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne.
36 恐怕他忽然来到,看见你们睡着了。
Kada ya zo ba zato, ya samu kuna barci.
37 我对你们所说的话,也是对众人说:要警醒!”
Abinda na gaya maku, ina gaya wa kowa, shine ku zauna a fadake!”

< 马可福音 13 >