< 詩篇 84 >

1 詠【朝拜上主歌】 科辣黑子孫的詩歌,交於樂官。調寄「加特」。 萬軍的上主,您的居所是多麼可愛!
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Na’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki!
2 我的心靈對上主的宮庭渴慕及緬懷。我的心靈及肉身向生活的天主踴躍歡欣。
Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai.
3 萬軍的上主,我的君王,我的天主,麻雀您的祭壇找到了住所,燕子也找到了安置 幼雛的窩巢。
Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.
4 上主,居住在您的殿宇,時常讚美您的,真是有福!
Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. (Sela)
5 那以您作為自己的助佑,居心朝聖的人,真是有福!
Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.
6 他們把他們經過的乾谷變為水泉,並以初雨給乾谷披上祝福的衣衫。
Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.
7 他們的體力越行越壯,來到熙雍覲見至高天主。
Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.
8 萬軍的上主,求您允我的懇請,雅各伯的天主,求您側耳傾聽!
Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. (Sela)
9 天主,我們的護盾,求您目睹,請對您的受傅者予以回顧。
Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka.
10 的確在您的聖殿逗留一日,遠勝過在別處逗千日。我寧願站在我天主殿宇的門限,我不願逗留在惡人帳幕的裏面,
Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye.
11 因為上主天主是護盾。上主常廣施恩愛和光榮;祂對行為正直純潔的人,從來不會拒絕賜祐賜福。
Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
12 萬軍的上主,依賴您的人,那人才是真有福的。
Ya Ubangiji Maɗaukaki, mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.

< 詩篇 84 >