< 約翰福音 20 >
1 週的第一天,清晨,天還黑的時候,瑪利亞瑪達肋納來到墳墓那裏,看見石頭已從墓門挪開了。
To da sassafe ranar farko ta mako, da sauran duhu, Maryamu Magadaliya ta zo kabarin, ta tarar an kawar da dutsen daga kabarin.
2 於是她跑去見西滿伯多祿和耶穌所愛的那另一個門徒,對他們說:「有人從墳墓中把主搬走了,我們不知道他們把他放在那裡了。」
Sai ta ruga da gudu zuwa wurin Saminu Bitrus tare da almajirin nan da Yesu ke kauna, tace masu, “Sun dauke Ubangiji daga kabarin, bamu kuwa san inda aka sa shi ba.”
Sai Bitrus tare da almajirin nan suka fita, kuma suka tafi kabarin,
4 兩人一起跑,但那另一個門徒比伯多祿跑得快,先來到了墳墓那裏。
dukansu suka ruga da gudu tare, amma daya almajirin ya riga Bitrus isowa kabarin,
Sai ya sunkuya ya leka ciki, ya ga likkafanin lillin a wurin, amma fa bai shiga ciki ba.
6 隨著他的西滿伯多祿也來到了,進了墳墓,看見了放著的殮布,
Sai Saminu Bitrus ya iso daga bayansa sai ya shiga kabarin, ya tarar da likkafanin lillin a ajiye.
7 也看見耶穌頭上的那塊汗巾,不同殮布放在一起;而另在一處捲著。
sai fallen kuma da yake kansa. Ba'a ajiye tare da likkafanin ba amma aka linkeshi aka ajiye shi daban.
8 那時,先來到墳墓的那個門徒,也進去了,一看見就相信了。
Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga ya gani, sai ya ba da gaskiya.
9 這是因為他們還不明白,耶穌必須從死者中復活的那段聖經。
Har ya zuwa wannan lokacin basu san nassin daya ce zai tashi daga matattu ba.
Sai almajiran suka sake komawa gida kuma.
11 瑪利亞卻站在墳墓外邊痛哭;她痛哭的時候,就俯身向墳墓裏面窺看,
Amma Maryamu tana tsaye a bakin kabarin tana kuka. Yayin da take kuka, sai ta sunkuya ta leka cikin kabarin.
12 見有兩位穿白衣的天使,坐在安放過耶穌遺體的地方:一位在頭部,一位在腳部。
Sai ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya zaune, daya ta wurin kai daya kuma ta wurin kafafu inda aka kwantar da Yesu.
13 那兩位天使對她說: 「女人! 你哭什麼?」她答說: 「有人把我主搬走了,我不知道他們把他放在那裏了。」
Sukace mata, “Uwargida don me kike kuka? Sai tace masu, “Domin sun dauke Ubangijina, ban kuwa san inda suka ajiye shi ba.
14 說了這話,就向後轉身,見耶耶穌站在那裡,卻不知道他就是耶穌。
Bayan ta fadi haka, ta juya sai ta ga Yesu tsaye a wurin. Amma bata san cewa Yesu bane,
15 耶穌向她說:「女人,妳哭什麼?你找誰?」她以為是園丁,就說:「先生,若是你把他搬走了,請告訴我,你把他放在那裏,我去取回他來。」
Yesu yace mata, “Uwargida, me yasa kike kuka? Wa kuma kike nema? Domin tana zaton shine mai kula da lambun, sai tace masa, “Maigida in kaine ka dauke shi, gaya mani inda ka sa shi, ni kuwa in dauke shi.”
16 耶穌給她說:「瑪利亞! 」她便轉身用希伯來話對他說:「辣步尼!」就是說「師傅。」
Yesu yace mata, “Maryamu”. Sai ta juya, tace masa da Armaniyanci “Rabboni!” wato mallam.
17 耶穌向她說:「你別拉住我不放,因為我還沒有升到父那裏;你到我的弟兄那裏去,告訴他們::我升到我的父和你們的父那裏去,升到我的天主和你們的天主那裏去。」
Yesu yace mata, kada ki taba ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna, amma kije wurin 'yan'uwana kice masu, zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku”.
18 瑪利亞瑪達肋納就去告訴門徒說:「我見了主。」並報告了耶穌對她所說的那些話。
Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran, “Na ga Ubangiji” Ta kuma ce ya fada mata wadannan abubuwa.
19 正是那一週的第一天晚上,門徒所在的地方,因為怕猶太人,門戶都關著,耶穌來了,站在中間對他們說:「願你們平安!」
Da yamma a wannan rana, a rana ta farko ta mako, almajiran suna kulle a daki saboda tsoron Yahudawa, Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu, yace “Salama Agareku”.
20 說了這話,便把手和肋膀指給他們看。門徒見了主,便喜歡起來。
Bayan ya fadi haka, sai ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa. Da almajiran suka ga Ubangiji, sai suka yi farin ciki.
21 耶穌又對他們說:「願你們平安! 就如父派遣了我,我也同樣派遣你們。」
Yesu ya sake ce masu, “salama agareku. “Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku”.
22 說了這話,就向他們噓了一口氣說:「你們領受聖神罷!
Da Yesu ya fadi haka, sai ya hura masu lumfashinsa, yace masu, “Ku karbi Ruhu Mai Tsarki.
23 你們赦免誰的罪,就給誰赦免;你們存留誰的,就給誰存留。」
Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; kowa kuka rike zunubansa, an rikesu.”
24 十二人中的一個,號稱狄狄摩的多默,當耶穌來時,卻沒有和他們在一起。
Toma, daya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana.
25 別的門徒向他說:「我們看見了主。」但他對他們說:「我除非看見他手上的釘孔,用我的指頭,探入釘孔;用我的手,探入他的旁,我決不信。」
Sauran almajiran sukace masa “Mun ga Ubangiji”. Sai yace masu, “In ban ga gurbin kusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsana a gurbin kusoshin ba, in kuma sa hannuna cikin kuibinsa ba, ba zan bada gaskiya ba.
26 八天以後,耶穌的門徒又在屋裏,多默也和他們在一起。門戶關著,耶穌來了,站在中間說:「願你們平安! 」
Bayan kwana takwas har wa yau almajiran na cikin gida, Toma ma na tare dasu, kofofin suna kulle, sai ga Yesu a tsakaninsu yace, “Salama agareku”.
27 然後對多默說:「把你的指頭伸到這裏來,看看我的手罷! 並伸過你的手來,探入我的肋旁,不要作無信的人,但要作個有信德的人。」
Sa'an nan yace wa Toma, “Iso nan da yatsanka, dubi hannuwana. Miko hannunka kuma kasa a kuibina, kada ka zama marar bada gaskiya, sai dai, mai bada gaskiya”.
Toma ya amsa yace “Ya Ubangijina da Allahna!”
29 耶穌對他說:「因為你看見了我,才相信嗎?那些沒有看見而相信的,才是有福的!」
Yesu yace masa, “Wato saboda ka gan ni, ka bada gaskiya? Albarka ta tabbata ga wadanda basu gani ba, amma kuwa sun bada gaskiya.
30 耶穌在門徒前還行了許多其他的神跡,沒有記在這部書上。
Yesu yayi wadansu alamu da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, wadanda ba'a rubuta a littafin nan ba.
31 這些所記錄的,是為叫你們相信耶穌是默西亞,天主子;並使你們信的人,賴他的名獲得生命。
Amma an rubuta wadannan ne, domin ku bada gaskiya Yesu shine Almasihu, Dan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai cikin sunansa.