< 使徒行傳 1 >

1 德敖斐羅!我在第一部書中,已論及耶穌所行所教的一切,
Littafin da na rubuta da farko, Tiyofilos, ya fadi abubuwan da Yesu ya fara yi ya kuma koyar,
2 直到他藉聖神囑咐了所選的宗徒之後,被接去的那一天為止;
har zuwa ranar da aka karbe shi zuwa sama. Wannan kuwa bayan da ya ba da umarni ga zababbun manzanninsa ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
3 他受難以後,用了許多憑據,向他們顯明自己還活著,四十天之久發現給他們,講論天主國的事。
Bayan ya sha wahala, ya bayyana kan sa da rai a garesu, da alamu da dama masu gamsarwa. Kwana arba'in ya baiyana kansa a garesu yana yi masu magana game da mulkin Allah.
4 耶穌與他們一起進食時,吩咐他們不要離開耶路撒冷,但要等候父的恩許,即你們聽我所說過的:「
Yayin da yana zaune tare da su ya basu umarni cewa kada su bar Urushalima, amma su jira alkawarin Uban, wanda ya ce, ''Kun ji daga gare ni,
5 若翰固然以水施了洗,但不多幾天以後,你們要因聖神受洗。」
cewa Yahaya babu shakka ya yi baftisma da ruwa, amma ku za a yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki nan da kwanaki kadan.''
6 他們聚集的時候,就問耶穌說:「主,是此時要給以色列復興國家嗎﹖」
Sa'adda suna tare suka tambaye shi, ''Ubangiji, a wannan lokaci ne za ka maido da mulki ga Isra'ila?”
7 他回答說:「父以自己的權柄所定的時候和日期,不是你們應當知道的;
Ya ce masu, ''Ba naku bane ku san lokaci ko sa'a wanda Uba ya shirya ta wurin ikonsa.
8 但當聖神降臨於你們身上時,你們將充滿聖神的德能,要在耶路撒冷及全猶太和撒瑪黎雅,並直到地極,為我作證人。」
Amma za ku karbi iko, idan Ruhu Mai Tsarki ya zo bisanku, sa'annan za ku zama shaidu na cikin Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, har ya zuwa karshen duniya.”
9 耶穌說完這些話,就在他們觀望中,被舉上升,有塊雲彩接了他去,離開他們的眼界。
Lokacin da Ubangiji Yesu ya fadi wadannan abubuwa, yayin da suna kallon sama, sai aka dauke shi zuwa sama, kuma girgije ya boye shi daga idanunsu.
10 他們向天注視著他上升的時候,忽有兩個穿白衣的人站在他們前,
Da suka dinga kallon sama yayin da ya tafi, nan da nan, mazaje biyu suka tsaya a gabansu cikin fararen tufafi.
11 向他們說:「加里肋亞人!你們為什麼站著望天呢﹖這位離開你們,被接到天上去的耶穌,你們看見他怎樣升了天,也要怎樣降來。」
Suka ce, ''Ku mazajen Galili me yasa ku ke tsaye a nan kuna kallon sama? Wannan Yesu wanda ya hau zuwa sama zai dawo kamar yadda kuka gan shi yana tafiya zuwa sama.''
12 那時,他們從名叫橄欖的山上,回了耶路撒冷,這山離耶路撒冷不遠,有一安息日的路程。
Da suka dawo Urushalima daga dutsen Zaitun, wanda ke kusa da Urushalima, tafiyar Asabaci daya ne.
13 他們進了城,就上了那座他們所居住的樓房,在那裏有伯多祿、若望、雅各伯、安德肋、斐理伯、多默、巴爾多祿茂、瑪竇、阿耳斐的兒子雅各伯、熱誠者西滿及雅各伯的兄弟猶達。
Da suka iso, sai suka haye zuwa cikin bene inda suke da zama. Sune su Bitrus, Yahaya, Yakubu, Andarawus, Filibus, Toma, Bartalamawus, Matiyu, Yakubu dan Alfa, Siman mai tsattsauran ra'ayi, kuma da Yahuza dan Yakubu.
14 這些人同一些婦女及耶穌的母親瑪利亞並他的兄弟,都同心合意地專務祈禱。
Dukansu kuwa suka hada kai gaba daya, yayin da suka ci gaba da naciya cikin addu'a. Tare da su kuma akwai mata, Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.
15 有一天,伯多祿起來站在弟兄們中間說: ──當時在一起的眾人大約共有一百二十名──「
A cikin wadannan kwanaki Bitrus ya tashi tsaye a tsakiyar 'yan'uwa, kimanin mutane dari da ashirin, ya ce,
16 諸位仁人弟兄!聖神藉達味的口,關於領導逮捕耶穌的猶達斯所預言的經文,必須應驗。
'' 'Yan'uwa, akwai bukatar Nassi ya cika, wanda Ruhu Mai Tsarki ya fada a baya ta bakin Dauda game da Yahuza, wanda ya jagoranci wadanda suka kama Yesu
17 他本來是我們中間的一位,分佔了這職務的一分;
Domin yana daya daga cikinmu kuma ya karbi rabonsa na ladan wannan hidima,”
18 但這人竟用不義的代價買了一塊田地,他倒頭墮下,腹部崩裂,一切臟腑都流了出來。
(Wannan mutum fa ya sai wa kansa fili da cinikin da ya yi na muguntarsa, kuma a nan ya fado da ka, cikinsa ya fashe, hanjinsa suka zubo waje.
19 耶路撒冷的居民盡人皆知,為此,他們以本地話稱那塊田地為「哈刻達瑪,」就是「血田」的意思。
Duka mazaunan Urushalima suka ji wannan, saboda haka suka kira wannan fili da harshensu “Akeldama'' wato, “Filin Jini.”)
20 原來在聖詠集上曾記載說:『願他的居所變成荒土,沒有人在那裏居住。』又說:『讓人取去他的職位。』
“Domin an rubuta a littafin Zabura, 'Bari filinsa ya zama kufai, kada a bar kowa ya zauna wurin,'kuma, 'Bari wani ya dauki matsayinsa na shugabanci.'
21 所以必須從這些人中,即主耶穌在我們中間來往的所有時期內,常同我們在一起的人中,
Saboda haka ya zama dole, daya daga cikin wadanda suke tare da mu tun lokacin da Ubangiji Yesu yana shiga da fita, a tsakaninmu,
22 由若翰施洗起,直到耶穌從我們中被接去的日子止,由這些人中,應當有一個同我們一起作他復活的見證人。」
farawa daga baftismar yahaya har zuwa ranar da aka dauke shi daga wurinmu zuwa sama, ya zama daya daga cikin mu wurin shaidar tashinsa.”
23 他們便提出了名叫巴爾撒巴,號稱猶斯托的若瑟,和瑪弟亞兩個人。
Suka gabatar da mutum biyu, Yusufu wanda ake kira Barsabbas, wanda kuma aka yiwa suna Justus, da kuma Matayas.
24 他們就祈禱說:「主,你認識眾人的心,求你指示,這兩個人中,你揀選了那一個,
Su ka yi addu'a suka ce, ''Ubangiji, kai ka san zuciyar dukan mutane, ka bayyana mana wanda ka zaba cikin su biyun nan
25 使他取得這職務的地位,即宗徒的職位,因為猶達斯放棄了這職位,去了他自己的地方。」
Domin ya dauki gurbin da kuma manzancin daga inda Yahuza ya kauce zuwa nashi waje''
26 他們給二人拈鬮,瑪弟亞中了鬮,就列入十一位宗徒之中。
suka jefa kuri'a a kansu; zabe ya fada kan Matayas kuma suka lissafta shi tare da manzanni sha dayan.

< 使徒行傳 1 >