< 使徒行傳 2 >

1 五旬節日一到,眾人都聚集一處。
Da ranar Fentikos ta zo, dukansu suna tare wuri daya.
2 忽然,從天上來了一陣響聲,好像暴風颳來,充滿了他們所在的全座房屋。
Nan da nan sai ga wata kara daga sama kamar ta babbar iska, kuma ta sauko ta cika duka gidan inda suke zaune.
3 有些散開好像火的舌頭,停留在他們每人頭上,
Sai ga wasu harsuna kamar na wuta sun bayyana a garesu aka rarraba su, kuma suka zauna bisa kowannensu.
4 眾人都充滿了聖神,照聖神賜給他們的話,說起外方話來。
Dukansu suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka fara magana da wadansu harsuna, yadda Ruhu ya ba su iko su yi magana.
5 那時,居住在耶路撒冷的,有從天下各國來的虔誠的猶太人。
A lokacin akwai Yahudawa dake zaune a Urushalima, mutanen Allah, daga kowace kasa karkashin sama.
6 這聲音一響,就聚來了許多人,都倉皇失措,因為人人都聽見他們說自己的方言。
Da suka ji wannan kara jama'a duk suka taru suka rude saboda kowannensu ya ji suna magana da harshensa.
7 他們驚訝奇怪地說:「看,這些說話的不都是加里肋亞人嗎﹖
Suka yi mamaki matuka; suka ce, ''Lallai, wadannan duka ba Galiliyawa ba ne?
8 怎麼我們每人聽見他們說我們出生地的方言呢﹖
Yaya mu ke jinsu duka, kowannensu na magana a cikin harshen da aka haife mu?
9 我們中有帕提雅人、瑪待人、厄藍人和居住在美索不達米亞、猶太及卡帕多細雅、本都並亞細亞、
Fisiyawa da Mediyawa da Elimawa, da Yahudawa da Kafadokiya, cikin Fontus da Asiya,
10 夫黎基雅和旁非里雅、埃及並靠近基勒乃的利比亞一帶的人,以及僑居的羅馬人、
cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma,
11 猶太人和歸依猶太教的人、克里特人和阿剌伯人,怎麼我們都聽見他們用我們的話,講論天主的奇事呢﹖」
Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah.''
12 眾人都驚訝猶豫,彼此說:「這是什麼事﹖」
Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, ''Menene ma'anar wannan?''
13 另有些人卻譏笑說:「他們喝醉了酒!」
Amma wasu suka yi ba'a suka ce, ''Sun bugu ne da sabon ruwan inabi.''
14 伯多祿就同十一位宗徒站起來,高聲向他們說:「猶太人和所有居住在耶路撒冷的人!請你們留意,側耳靜聽我的話!
Amma Bitrus ya tashi tare da sha dayan, ya daga murya ya ce da su, ''Mutanen Yahuda da dukanku dake zaune a Urushalima, bari ku san wannan; ku saurari maganata.
15 這些人並不像你們所設想的喝醉了,因為纔是白天第三時辰;
Domin wadannan mutanen ba buguwa suka yi ba yadda kuke zato, domin yanzu karfe tara ne na safe kawai.
16 反而這是藉岳厄爾先知所預言的:
Amma wannan shine abinda aka fada ta wurin annabi Yowel.
17 『到末日──天主說──我要將我的神傾住在所有有血肉的人身上,你們的兒子和女兒都要說預言,青年人要見異像,老年人要看夢境。
Allah ya ce, 'Haka zai kasance a kwanakin karshe, zan zubo Ruhuna a kan dukan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci, kuma samarinku za su ga wahayoyi, kuma tsofaffinku za su yi mafarkai.
18 甚至在那些日子裏,連在我的僕人和我的婢女身上,我也要傾住我的神;他們要講預言。
Haka kuma a bisa bayi na maza da mata, a kwanakin nan zan zubo da Ruhuna, kuma za su yi anabci.
19 我要在天上顯示奇蹟,在下地顯示徵兆:血、火和煙氣。
Zan nuna al'ajibai a sararin sama da kuma alamu a bisa duniya, jini da wuta, da girgije.
20 在上主的偉大和顯赫的日子來臨以前,太陽要變成昏暗,月亮要變成血紅。
Rana zata juya ta koma duhu kuma wata ya koma jini, kafin Babbar ranan nan ta Ubangiji ta zo.
21 將來,凡呼號上主名字的人,必然獲救。』
Zai kuma zama dukan wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto.
22 諸位以色列人!請聽這些話:納匝肋人耶穌是天主用德能、奇蹟和徵兆──即天主藉他在你們中所行的,一如你們所知道的──給你們證明了的人。
Mutanen Isra'ila, ku saurari wadannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar da shi gareku ta wurin manyan ayyuka da ban mamaki da alamu da Allah ya yi ta wurinsa a tsakiyarku, kamar yadda ku da kanku kuka sani.
23 他照天主已定的計劃和預知,被交付了;你們藉著不法者的手,釘他在十字架上,殺死了他;
Saboda tabbataccen shiri da riga sani na Allah, aka bayar dashi, ku kuma, ta hannun mutane 'yan tawaye, kuka gicciye shi kuma kuka kashe shi.
24 天主卻解除了他死亡的苦痛,使他復活了,因為他不能受死亡的控制,
Wanda Allah ya tayar, bayan ya cire zafin mutuwa daga gareshi, saboda ba zai yiwu ba ta rike shi.
25 因為達味指著他說:『我常將上主置於我眼前;我決不動搖,因他在我右邊。
Gama, game da shi, 'Ina ganin Ubangiji a gabana ko yaushe, domin yana gefen hannun damana saboda kada in firgita.
26 因此,我心歡樂,我的舌愉快,連我的肉身也要安息於希望中,
Saboda haka zuciyata na farin ciki harshena yana yin murna. Kuma, jikina zai zauna gabagadi.
27 因為你決不會將我的靈魂遺棄在陰府,也不會讓你的聖者見到腐朽。 (Hadēs g86)
Gama ba za ka watsar da raina a lahira ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka ya ga ruba ba. (Hadēs g86)
28 你要將生命的道路指示給我,要在你面前用喜樂充滿我。』
Ka bayyana mani hanyar rai; da fuskarka zaka cika ni da farin ciki.
29 諸位仁人弟兄!容我坦白對你們講論聖祖達味的事罷!他死了,也埋葬了,他的墳墓直到今天還在我們這裏。
'Yan'uwa, zan yi magana da ku gabagadi game da baba Dauda: ya mutu kuma aka bizne shi, kuma kabarinsa na nan tare da mu har yau.
30 他既是先知,也知道天主曾以誓詞對他起了誓,要從他的子嗣中立一位來坐他的御座。
Domin haka, don shi annabi ne kuma ya san Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa daga cikin zuriyarsa zai sanya wani bisa kursiyinsa.
31 他既預見了,就論及默西亞的復活說:『他沒有被遺棄在陰府,他的肉身也沒有見到腐朽。』 (Hadēs g86)
Ya hango wannan al'amari kuma ya yi magana game da tashin Almasihu, 'Ba ayi watsi da shi ba a lahira, kuma jikinsa bai ga rubewa ba.' (Hadēs g86)
32 這位耶穌,天主使他復活了,我們都是他的見證人。
Wannan Yesun - Allah ya tashe shi, wanda dukanmu shaidu ne.
33 他被舉揚到天主的右邊,由父領受了所恩許的聖神;你們現今所見所聞的,就是他所傾注的聖神。
Saboda haka yadda aka tashe shi zuwa hannun dama na Allah kuma ya karbi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, shine ya zubo mana wannan da kuke gani kuma kuke ji.
34 達味本來沒有升到天上,但是他卻說:『上主對吾主說:你坐在我右邊,
Dauda bai hau zuwa sama ba, amma ya ce, ''Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna hannun dama na,
35 等我使你的仇敵,變作你腳的踏板。』
har sai na maida makiyanka abin takawar sawunka.'''
36 所以,以色列全家應確切知道:天主已把你們所釘死的這位耶穌,立為主,立為默西亞了。」
Saboda haka, bari gidan Isra'ila su sani tabbas wannan Yesun wanda kuka gicciye, Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu.
37 他們一聽見這些話,就心中刺痛,遂向伯多祿和其他宗徒說:「諸位仁人弟兄!我們該作什麼﹖」
Da suka ji haka sai suka soku a zukatansu, suka cewa Bitrus da sauran manzanni, '''Yan'uwa me za mu yi?''
38 伯多祿便對他們說:「你們悔改罷!你們要以耶穌基督的名字受洗,好赦免你們的罪過,並領受聖神的恩惠。
Sai Bitrus ya ce masu, ''Ku tuba ayi wa kowannenku baftisma, cikin sunan Yesu Almasihu domin gafarar zunubanku, kuma za ku karbi baiwar Ruhu Mai Tsarki.
39 因為這恩許就是為了你們和你們的子女,以及一切遠方的人,因為都是我們的上主天主所召叫的。」
Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira.''
40 他還講了很多別的作證的話,並勸他們說:「你們應救自己脫離這邪惡的世代。」
Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, ''Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara.''
41 於是,凡接受他的話的人,都受了洗;在那一天約增添了三千人。
Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku.
42 他們專心聽取宗徒的訓誨,時常團聚,擘餅,祈禱。
Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i.
43 因為宗徒顯了許多奇蹟異事,每人都懷著敬畏之情。
Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin.
44 凡信了的人,常齊集一處,一切所有皆歸公用。
Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne,
45 他們把產業和財物變賣,按照每人的需要分配。
kuma suka saida kadarorinsu da mallakarsu kuma suka rarrabawa kowa, bisa ga irin bukatar da kowannensu yake da ita.
46 每天都成群結隊地前往聖殿,也挨戶擘餅,懷著歡樂和誠實的心一起進食。
A kowace rana suka cigaba tare da nufi daya a cikin haikali, suna kakkarya gurasa a gidaje, kuma suna raba abinci tsakaninsu cikin farin ciki da tawali'u a zuciya;
47 他們常讚頌天主,也獲得了全民眾的愛戴;上主天天使那些得救的人加入會眾。
Suna yabon Allah kuma suna da tagomashi a gaban dukan mutane. Ubangiji kuma kullum yana kara masu wadanda suke samun ceto.

< 使徒行傳 2 >